← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 23

Sashe 23

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"kawata ina tare da ke a dukka halinda kike ciki, ki dauke ni a matsayin 'yar uwarki jininki ina tare da ke duk halin wuya ko dadi. Ga kudi nan naira dubu dari biyu na turo miki ki yiwa yara soyayya ki kula da su. Sannan na yi miki alqawarin duk ribar da na samu a makarantata ta koyar da abinci zan dinga raba ta gida uku, Kashi daya zan dinga baki dan ki kara kula da yara. Na sami number ki da account number ki a wayarki a lokacin da kika shiga bandaki, dan na san idan na tambaye ki ba za ki bani ba. Ina yi miki addu'a Allah Ya taya ki riqe.
Na gode Amiyarki Samha.Mahmud.

Hawaye mai zafi gami da tausayin kanta da kanta ne ya far ma ta. Ta rantse da Allah a wannan zamanin da wuya ka sami mai sonka saboda Allah haka. Gashi dai kawata har ta fi 'yan uwanta,ta tausaya ma ta, ta yi ma ta kyautar bazata.
Sharifah ta ba ta amsa da kalamai masu dadi ta nuna godiya da jin dadi. Haka ta tsaya tana kallon alert din dubu dari biyu a dunkule, abinda babu wanda ya taba yi ma ta haka a danginta bayan su na da masu kudin da zasu iya kyautar miliyan biyu ma ba tare da sun san sun yi ba yin ne ba zasu yi ba.
Haka Sharifah ta ke jin saukar alert daga Samha lokaci-lokaci ba tare da ta saka rai ba, na kudi masu yawa kuma. Tabbas alkhairi baya faduwa a kasa, ta tuna sanda kudin motar zuwa makaranta da kudin handout yake gagarar Samha da Aliyu. Sharifah ce mai siya ma ta ko ta bata kudin mota ko ta dauko a motarta ta kai ta makaranta kuma ta biyo ta sauke ta idan sun tashi.
Dan halak baya manta alkhairi ashe Samha ba ta manta ba itama. Allahu akbar!

*** *** ***
Wancan labarin ya rage tsakanin Samha da su Nana Ahmad ne, an hadu an haura an sauko an daidaita. Samha ta sha aradu duk mai daukar Sharifah fatalwa zasu bata idan Sharifah fatakwa ce itama su dauke ta fatalwa, duk daya suke sai dai su guje su, su biyu.
Sharifah ba ta ce komai ba bata ma san an yi ba, sai dai ta ga Samha ta kawo su dukka gidanta, bayan sun gaisa ta ci gaba da sauraronsu, su ka gama bayani da bayar da hakuri. Ta ce ya wuce kuma ta gode.

*** *** ***

Kwanci tashi Allah Ya sauki Samha lafiya ta haife 'yan biyu su dukka mata, kyawawa kamar ubansu. An sha murna, abin mamaki aka saka mu su suna Sharifah da Shariqah.
Da farko da aka fadawa Sharifah ba ta yarda ba, ta zaci wasa ne.Tabbas sun cika ma ta burinta da ta roqe ta a asibiti ta ce a sakawa baby sunan Shariqah, da suka zama tagwaye sai aka saka mu su har da sunanta.
Sai yanzu ta sake yarda tabbas Samha aminiyar kwarai ce, haka da yardar Aliyu da ta mama. Dan Samha ta basu labarin Sharifah tas kuma ta ce dan Allah su dauke ta danginsu. Dan tana bukatar ja a jiki da soyayya da kulawa.
Akwati guda Sharifah ta yiwa yaran cike da kaya har da 'yan kunnayen gwal, da alama kwangila nan mai karfi ta fara sauka.
An hadu a sunan Samha da su Nana sai ga Sharifah da Fanna sun iso.
Fanna ta cafke Nana gam ta riqe dan ta ga alamar tana dan jin tsoronta har yanzu. ta ce " ni ma fatalwa ce na zo mu tafi mu yi HIRA DA MATATTU a kabarina."
Zo ka ga ihu a wajen Nanah, kowa ya kwashe da dariya har da kyakyatawa.

Alhamdulullah!
Karshe!!
Madalla da alqalamin Jut.

Mu hadu a sabon littafina mai suna LOKACIN DA NAKE RAYE.
[3/6, 5:19 PM] Jamila Umar Tanko: Haqqin mallaka:Jamila Umar tanko
Copyright: Jamila umar tanko

Wannan littafi mai suna HIRa DA MATATTU na 2 na kudi ne.

300 ne kacal Zaa biya
0112240731
Gt bank
Jamila umar tanko

Idan an biya a turo shaidar biya ta wannan lambar:
08061225337

Na gode
Chapter 23 · 0% Book details