← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

gani-gani. Daman can ma jinina da ita bai hadu ba, a dalilinku ne ma mu ke gaisawa." Halima ta girgiza kai ta ce "kai Rukayya ko a bayan idon mutum ne ka fadi gaskiya mana. Babu wanda zai yiwa Sharifa shaidar baqin hali wallahi, ga kyauta ba ta da mugunta. Kawai dai yanzu ta zama abar a gudu dan ba ta da kammannin mutane sak." Samha dai ba ta magana har suka isa gida suka fito suka shiga falonta aka zauna, aka yi jugum kamar gidan makoki. Samha ta zabura ta jawo wayarta ta kira Fanna ta saka ta a hand's free.Fanna na dauka ko gaisawa ba su ba. A gigice Samha ta ce "Fanna! dan girman Allah me kika sani akan matsalar da ke damun Sharifah. Ba ta fada miki wasu daga cikin matsalolinta ba?" Fanna ta yi dariya ta ce "ai kun yarda Sharifah fatalwa ce ta mutu ta dawo ko? Toh a je a hakan. Ban sani ba ko dan ni ma mun samu matsala iri daya da ita ne shiyasa ba na jin tsoronta. Dan nima na yi ciwo na mutu fa, mata da maza sun cika gida an fasa kukan mutuwata. Har an yi min wankan gawa, an saka min likkafani, maza sun kinkimi gawa za su fita da ni waje, zaa yi min salla a kai ni kabarina sai na farfado." Samha da kawayenta su ka daka tsalle har da Rukayya da take sallah suka fafara da gudu, suka yi waje. Anan Samha ta bar wayar a yashe, su na jiyo dariyar Fanna, ta na ta dariya babu kakkautawa, irin ta muguntar nan. Wannan karon yaren KANURI ta juye harshe take yi. Ta na ambaton sunanta da na Sharifah da na Shariqah. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Me yake shirin faruwa kenan? Fanna ma fatalwa ce ashe shiyasa bata tsoron Sharifah, an ce ta zo ta raka mu gidan ta ki zuwa." Nana ce take magana har da hawaye. Su na ta kai kawo a farfajiyar gidan an rasa wacce ta iya shiga cikin falon. Su mayafansu ma suke so su dauko su tafi gidajensu. Kowacce na tunanin in da za ta kaura ta kwana ko mutanen da zata biya ta dauko a cikin danginsu su taya su kwana. Samha ta fi su dimaucewa ba ta so ta dawo gidan jiya na firgici da susucewa, kuma da alama dai sai ta dawo saboda duk yadda ta kai ga yiwa Sharifah kyakykywan zato abin ya ci tura. Da kyar suka samu suka yi jarumta suka shiga falon, ga waya nan a yashe a kasa. Da Samha ta duba 9 missed calls Fanna da 3missed calls din wata lamba wacce ta yi ma ta kama da ta Sharifah wacce ta taba kiranta da ita, ta gani. Samha ta sha aradu ba za ta amsa kiransu ba, ta ma kashe wayar gaba daya. Su Rukayya da aka yi sallah raka biyu baa idar ba aka runtuma da gudu ta ce za ta rama sallar a gida. Wasu ma sun manta take way din da suka yiwa miji anan saboda gigita, kowacce ta suri jaka da mayafi jiki na karkarwa ta fita. Daman dukkansu da motocinsu suka zo dan haka kowacce ta shiga ta ja ta tafi tana addu'a. Aka bar Samha ita kadai a gida tana muzurai, da sauki ma tunda Aliyu yana gari zai dawo komai dare, amma ta tabbatar zai neme ta a waya kafin ya iso, ga shi kuma ta kashe wayar. Ta hau kan abin sallah ta na lazumi amma fa dukka motsin da ta ji sai ta zabura ta waiwaya. Aliyu bai dawo gida da wuri ba sai bayan qarfe goma na dare ta wuce. Lokacin Samha ta gama zabura-zaburenta har ya zame ma ta jiki. Wani irin tsoro mai tsanani ne ke damunta. Amma ta kasa bawa Aliyu amsa a dukkannin tambayoyin da yake jero ma ta. Musamman akan dalilin da ya sa ta kashe wayarta. Amsar da ta bashi ba ta gamsar da shi ba na cewa babu caji. Sai ya kalli fitilar lantarki a kunne, ya jiyo ya dube ta. Ta lalubo wayar ta kunna sakonnin Fanna ne ya shigo har guda uku. Sako na farko ta ce "kin kira kina so ki ji labari kuma kin kashe waya." Sako na biyu ta ce " ki kunna waya mana." Sako na uku ta ce "in kina so in baki labarin matattu da fatalwa ki kira ni ki ji." Ta na karantawa sai ta zabura. Aliyu ya tsaya ya na kallonta. Can ya tambaya ya ce "kun sami zuwa gidan Sharifah kuwa? Me ya faru? Ko wata fatalwar kika gani ne na ga kin susuce?" Samha ta zazzare ido ta ce "fatalwa kuma? Ai an wuce wannan babin. Ba mu sami damar zuwa ba. Amma za mu saka wata ranar." Da ya ci gaba da yi ma ta kallon tuhuma sai ta yi gaggawar barin falon don kada ya gane ta.
Chapter 6 · 0% Book details