← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mu anan? Wallahi daga CBN, kudin nan da ake rabawa na tallafin corona." Samha ta ce " kin bani satar amsa in sha Allah zan tattara lamurana waje daya in miqawa Ubangijina Allah. Wato ma mutum ya daina neman shawara ko fadawa wani matsalarka, dukka bata lokaci ne da tonar asiri.Gara kawai ka kalli gabas ka fadawa Allah." Sharifah ta ce "sosai Samha. Ga rashin lafiya dan a lokacin idan kin ganni ba za ki gane ni ba, kawai kuraje suka dinga feso min, idanuwana ciwo, wani lokaci har bana gani sosai. Idan ina tafiya sai in fara haki, har ana so a dora min ciwon zuciya. Sanda kika ganni ma me ai na ji sauki akan da. Addu'a kawai na tsaya ina ta yi, abinda na cewa Rabbil samawati shine Ya Allah zuciyata ba zata kamu da ciwo ba saboda a cike take da tsoronka da son matsayinka Annabi Muhammad S.A.W. dan haka zuciyata babu ciwo. Ya Allah kada ka kaddara zuciyar da ta cika da son Annabi ta kamu da ciwo. Ina zuwa gwaji zuciya babu ciwo Samha, alhali ada komai na alamun ciwon zuciya ya tabbata. Kai duk wanda ya ce babu Allah bai yarda da Allah ba, tabbas ya na cikin asara babba." Samha ta yi kabbara ta ce " gaskiya kin kama babbar madafa. Ina tare da ke 'yar uwa." [3/6, 5:15 PM] Jamila Umar Tanko: 7 Lokacin sallar azhar ta yi dan haka su ka katse labari, Sharifah ta shiga bandaki don dauro alwallah. Samira ce ta shigo a gigice har sai da Samha ta ji tsoro. Samira na ganin Samha sai ta yi ajiyar zuciya ta dafe kirji, har da wata kwallar farin ciki ce ta sirnano. Samha ta tambaya a gigice "lafiya? ina su Mama?" Samira ta ce " ba maganar Mama ba ne, ita yanzu ma mun yi waya sun isa lafiya. Kawayenki ne su Aunty Nana suka zo gidanki nemanki, na fada mu su ki na asibiti. Daidai lokacin na gama sakwara sai na basu su taho miki da ita dan an kira ni a BUK ance mu kai wani wani assignment da aka bamu. To ina can makaranta tare da kawayena mu na yi sai su ka hana ni sakat su na ta kira na a waya wai in kira Yaya Aliyu da 'yan uwa a je asibiti, sun baro ki kina cikin wani hali kina neman taimako. f Fatalwa ta saka ki a gaba bakya iya magana bakya iya daukar waya, kuma ba lallai ba ne ma likitocin su ganta ke kadai kike ganinta." Samha ta jawo Samira da sauri ta toshe ma ta baki ta yi magana cikin rada ta ce "yi a hankali Sharifah ce fa, tana cikin bandaki kada ta ji ki ba zata ji dadi ba. Allah Ya shirye su, su kuma. Babu wata fatalwa qawata ce kuma aminiyata." Samira ta yi tsaki ta na magana a hankali ta ce "daman Aunty Sharifah ce? su har yanzu ba zasu bar maganar fatalwar nan ba ne? Bayan an fayyace komai zance ya wuce. Wallahi sun hana ni karatu sai waya suke, Anti Nana har da kuka take yi min a waya." Samha ta ce "in ba ki gama Assignment dinki ba ki je ki gama kawai ki manta da su." Samira ta gyada kai ta ce "ba mu gama ba na Taso wallahi. Allah Ya sa ma da motarki na je da na sha wahalar neman abin hawa. Bari in koma da sauri." Ta fice da saurin, yayin da Samha ta jawo wayarta, missed calls dinsu ta gani ya fi ashirin da sakonni da na su da na Samira. Sakon Nana ne ta rubuta wai Samha ta fada musu gaskiya idan itama ta zama fatalwar ne su rabu da ita, dan sun ga alamu har akwai munafunci tunda in an yi shawarar rabuwa da Sharifah sai ta sake jajubo musu ita. Dariya ta kama ta ba mamaki ba, har sai da ta toshe baki, ta sha dariya ta gode Allah. Sannan ta ajiye wayar daidai lokacin Sharifah ta fito daga bandaki. Itama ta shiga don yin alwallah. Bayan sun idar da sallah ne Sharifah ta tambaya wacece ta shigo? Dan ta ji tana magana da wata? Samha ta yi murmushi ta ce "Samira ce ta zo ta dauki wani abu ta koma Makaranta." Ita fa Samha har yanzu a labarin Sharifah ba ta ji an sauka a in da take so a sauka ba. Alaqar Sharifah da baqin kare da ciwo da mutuwa, sannan kuma da labarin Fanna yadda ta mu. Samha dai sai tsokano labari take Sharifah tana zuqewa. Sharifah da Hamidah ne suka yi waya, Hamidah tana bata labarin cewa Mahaifinta ya kira ta a waya yana bata hakuri akan rashin kula ta da baya yi, ya san yayi kuskure zai gyara. Sannan kuma yana so ta tubure ta cewa mamarta ta dawo gidansa. Sharifah ta tabe baki ta yi murmushin karfin hali ta ce "Hmmm! Rabu da shi, idan ma mafarki yake yi to ya farka." Bayan sun kashe waya Samha ta gyara zama ta ce "watakila ya canja halinsa, ki yi hakuri mana ku koma." Wannan karon wata katuwar harara Samha ta amsa daga wajen Sharifah. Ta ce "kin san kuwa bayan rabuwata da shi aure sa nawa? Ya kai aure takwas yi, wata ma watanni uku kacal ta yi ta fita, wasu matan ma basu kai watanni ukun ba. Dan bashi da hali ko kadan. Ya zagi iyayenki,ya zage ki, ga cin mutunci, babu abinci, babu Biyan kudin haya, babu kula da yaranki, ke hatta kudin wutar lantarki in baki biya ba sai dai a yanke ba zai biya ba. Ga Hamidah nan zan iya rubuto abinda ya taba kashe ma ta tun daga ragon suna zuwa yanzu, ba ta ci dubu darinsa ba. Haba Samha ni kuma wacce irin asararriya ce da zan zauna da mai karancin addini? Wasu abubuwan ma ba zasu fadu ba saboda alfarmar aure da haihuwa. Danginsa su na kirana a ways su na roqo wai in dawo dan Auwal ba zai iya zama da kowa ba sai ni. Saboda ni kadai ce na iya yin zaman shekaru masu yawa da shi. Sun kuwa san wahalar da na sha da shi?" Samha ta bude baki ta dafa haba ta ce " wai! wai!! wai!! har abin na sa ya kai haka daman. Gaskiya wannan ba mijin zama ba ne. A haka kyakykywa da shi kamar wani gentle man." Sharifah ta ce "kyawun dan miciji ne, shiyasa nake so 'yan mata su gane su rabu da kyawun sura, su zabi hali, duk namijin da bashi da hali mai kyau kuma addini bai ratsa shi ba toh kada su sake su aure shi, koda yana zubar da naira dan za suyi nadama duniya da lahira.' Samha ta ce " gaskiya ne Allah Ya zaba miki wanda ya fi alkhairi kawata. Yanzu yaya kuke ciki da Adamu da maganar yara? Sanda mu ka zo na ga Hamidah tana kuka rannan, ta ce min an sace yaran ne. Ke kuma mu ka jiyo kina magana da Shariqah a daki. Me ya faru ne?." Sharifah ta kwashe da dariya ta ce "shine ku ka fice da gudu ko? Ai na san kun ji shine har yanzu su Nana suke ta guduna? Ba su da hankali." Samha ta ce " toh meye ya faru?" Sharifah ta ce "da aka fara zaman sulhu sai aka ce in bashi yaran ya gani saboda sun shekara bai gansu ba. Kin ga ai ba zan hana ba tunda an ce sulhu, ga lauyana ga lauyansa ga barista Aisatu ba zan kawo komai a raina ba ai ko? Kuma an yi Hutun makaranta a lokacin. Na rantse da Allah mutumin nan dan bashi da ta ido sai ya riqe yaran ya hana su, har sati biyar, ke har ya saka su ma a wata makarantar. Kamar mu na garin mahaukata inda babu doka. Ya manta a tsakiyar lauyoyi aka yi magana kuma an rubuta komai. Ya tafi ya sami lauyansa wai ya zo su je wajen Bar. Aisatu a canja magana, saboda shi ya dauka kowa ne a Nigeria ya yake karbar cin hanci. Ai kuwa ta yi masa fata-fata kuma ta tabbatar masa ya karya doka. Daman kuma lauyansa ya fada masa gaskiya babu in da zai je a goyi da bayansa, akan abin nan da ya yi. Su Shariqah ne suka shiga damuwa dan ta na zo min akai-akai, ranta a bace dan bata cika yin magana ba ma idan ta zo amma ina gane yanayinsa. Hamidah ce ma take ta kuka, shine a lokacin ku ka ji ina fadawa Shariqah gaskiya, cewa ta je ta kwanta wannan yakin na masu rai ne." Tsoro ya kama Samha gami da daurewar kai ta ce "Sharifah na kasa gane abinda kike fada idan kika ce Shariqah ta zo." Sharifah ta yi murmushi ta ce "ai na fada muku a baya, ni na gani da idanuwana mamaci yana sanin abinda yake faruwa a duniya." Samha ta ja wata doguwar ajiyar zuciya ta ce " kuma ya mutu mutuwar gaske, amma ake ganinsa?" Sharifah ta ce "ki dai mu je zuwa za ki ji komai. Ina zamana na ga an dawo da yaran, ban ce komai ba amma na fadawa lauyana duk abinda ya faru. Sai ya riqe Hamid dan yaron nan da nake yawo da shi wanda ya fi kowa sona a cikinsu, nima na fi shakuwa da shi. Sai ya riqe shi dan ya san abin zai taba min zuciya. Ya yi karya wai yaron bashi da lafiya, ashe har a makaranta ya saka shi." Samha ta ce "Adamu fa ya sami matsala, ya rasa yadda zai yi da ke ne yake wannan kame-kamen." Sharifah ta yi dariya ta ce "ya raina mata ne, bai dauki mace a komai ba sai ga shi ya takalo fada da mace ta hana shi bacci. Akwai mata ai kuma akwai mu na mata. Bayan nan aka dinga zamansulhu amma an kasa cimma matsaya. Bar.Aisatu har tausayi ta bani, tana ta kokarin yin sulhu amma abu ya ci tura. Ta na da abubuwa da yawa a gabanta, kullum a na layi a ofishinta, ga gidajen radiyo da dama su na
Chapter 19 · 0% Book details