Sashe 15
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
*** *** ***
Samha ta dawo falonta ta zauna yayin da idanuwanta su ka dira akan wannan fim din me firgitarwa abin ba kyan gani, matattune hagar naman masu rai.
Ta tashi da sauri ta kashe talabijin din ma gaba daya sannanta sami dan saukin hayaniyar, ta hada kai guiwoyinta biyu ta takure, ta na addu'a ta rasa abinda yake damunta. Ta na son zumuncinta da Sharifah ya dore amma ba za ta iya ci gaba da zaman zulumi irin wannan ba. Gaskiya tana ta sake bayyana duk da tana kawarwa gefe, amma abu ya ci tura. Sharifah ba mutane ba ne wasu halittu ne na daban.
Maganar Fanna ce ta dinga dawowa cikin kanta da ta ta ce "shin ba ki bata labarin baqin karen da ya cije ki har ya zama ajalinki ba ne?"
Sharifa kuma ta amsa da "eh haka ne ban bata labari ba." Meye hakan ke nufi?"
Samha ta fara tunanin kawai ta yi irin yadda su Nana da Maryam su ka yankewa kansu shine sun hakura da kawance da Sharifah, ko da ita kadai kawarsu da ta rage a duniya. Samha ta ga hakan zai fiye ma ta alkhairi da kwanciyar hankali. Gara su yafewa juna dan duk iya yadda ta so Sharifah ta gyaru ta dawo daidai abu ya gagara, daga wannan sai a koma wancan.
Samha ta sirnano da hawaye ta fada a bayyane "tunda uwata ta haife ni ban taba ganin masifa irin wannan ba."