Sashe 12
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Samha ta ce "Sharifah na san ki a baya ki na da zafi bakya daukar raini. Yaya aka yi har mutumin nan ya sami dama yake taka ki yadda ya ke so?" Sharifah ta yi murmushi ta jingina a jikin kujera ta rufe ido kamar mai tunani har zuwa wasu 'yan lokuta sannan ta dago ta dubi Samha ta yi dariya. Ta ce " ba ke kadai ba ma ko 'yar da na haifa Hamidah ta yi min irin wannan tambayar. Samha wato na ga rayuwa, na tabbatar babu wanda ya Isa sai Allah, babu wani mai iko sai Allah. Dan Adam ba komai ba ne. Na qara yin imani, na koyi hakuri, na koyi tawakkali, ina so in gyara mu'amulata da Ubangijina, da kuma sauran jama'a. Me ya yi saura kuma a duniyata? Babu Mama, babu Baba, babu Yayana Bellocity, babu Shariqah. Na dogara ga Allah gaba daya na miqa maSa wuya, ina ganin kamar rayuwar matattu ta fi irin rayuwar da nake yi yanzu dadi. Na karkata gaba daya na fuskanci kabarina, kullum ina jiran isowar layi ya zo kaina. Samha me kika sani akan mutuwa? Me ki ka sani akan rayuwa? Me kika sani akan halayyar dan Adam? Ana ganin idanuwan iyayenki ba zaki taba gane masoyinki ba sai ranar da aka ce yau babu ran mahaifa za ki ga rashin kara da rashin kunya. Ko a sanin da kika yi min ada Samha, ba na neman fada ko kadan. Ina takatsantsan dan kada in shiga harkar wani in bata masa amma kuma bana so a shiga harkata a takura min. Idan na takura ne sai in fashe toh idan na fashe ba ta yin kyau. Ai Adamu bai kai rabin neman rigimar mijina ba amma da ya kaini karshe bai ji da dadi ba. Na kan bawa mutum dama mai yawa kafin in gaji. Ai yanzu na ke ba ki labarina da mijin Shariqah za ki ji yadda ta kaya. Sai ya tabbatar min ya kwashe yaran ba zai kawo min kuma dan rashin kunya ya kira ni yana yi min maganar gado. Bayan tun lokacin da aka yi sadakar arba'in ake ta bin kansa ya zo a zauna ya qi. Ashe shi niyyarsa babu rabon gado daman shine zai gada daga shi sai yaransa, idan ya auri Dinar sai ya dauki yaransa, ya karbe gado, sai ya yi gaba shikenan ya gama da shafinmu. Sai ya je ya ci gaba da mulkinka. Kuma daman dukka kara da bin dokar da nake yi akan kada ya kwashe yaran ne, yanzu kuma me yayi saura tunda ya kwashe? Na rikice ta inda na shiga ba ta nan nake fita ba, wani yanayi na shiga wanda ni da kaina ba yin kaina ba ne, har sai da Hamida da Dinar suka kwace wayar. Ina ganin bai taba jin maganganun da ya ji a ranar ba. Daga nan ya tabbatar ko ya sha giyar wake ba zai iya takowa ya zo gidana ba. Sai ya nemo Bello a waya. Sai ga kiran Bello ya na tambayata abinda ya faru sabanin abinda Adamu ya fada masa masa har ya shirya min wani sharri da karya karya kala kala. Daga nan fa fada ya fara a tsakanina da Adamu. Ya boye yara ba sa gidansa ba sa gidan iyayensa ya kai su ajiya. Ki duba fa ki gani wai yaran da suka rasa uwa yake yiwa wannan wulakancin alhali ga inda aka san darajar ake kaunarsa ya dauke su. Mu ka yi samame mu ka je gidansa babu yaran, wata 'yar uwata ta nemo lambar mahaifinsa saboda dattijo ne mun yi tunanin bai san rashin arzikin da dansa yake aikatawa ba. Amma sai kalamansa su ka nuna shine ma yake zuga shi akan ya kwato yaran. Tsohonsa ya yi rantsuwa su babu wanda ya isa ya riqe mu su yaransu, su ne masu alhakin rikewa. Ashe ma dai shine ya dora shi akan wannan karatun na ya sace yaran. Amsar da na bayar ita ce daga kaina kuwa za ku sauke wannan salon." Samha ta gyara zama ta ce "ikon Allah wannan wacce irin rayuwa ce? Daman ana yin haka?" Sharifah ta langwabar da kai ta ce " Wallahi Samha tunda daga ranar da aka kwashe yaran nan Shariqah ba ta sake kwanciya a labarinta ba, kuma ba ta barni na kwanta haqarqarina ba." Samha ta zazzare ido ta tambaya a gigice "Kamar yaya?" Sharifah ta sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani, ta ce " duk in da na jefa kafata Shariqah sai ta jefa ta ta qafar. Bi na a baya kawai take take yi. Sai in juyo in tambaye ta Shariqah menene? Sai ta yi shiru ba ta magana. Babu safe, babu rana, babu dare, Sharqah na biye da ni. Sai daga baya na gane bin nan da take yi min ya na da alaqa da yaranta da aka kwashe ne fa, take so in karbo ma ta. Satin yaran nan uku cur baa san inda suke ba kuma ya qi fada. Haka itama ba ta taba yin fashin barina ba, koda yaushe ina ganinta. Ta biyo ni daga cikin gida mu ka fito kofar gida na shiga mota na zauna sai ta tsaya a bakin get, na ce ma ta ta zo mu tafi mana, sai ta tsaya ta qi ta shigo cikin motar. Ta san na gane abinda take so ta nusar da ni, wajen yaranta take so in je dan haka ba ta biyo ni ba." Kan Samha fa ya daure gaba daya, har hayaqi yake yi na rashin fahimta. Ta sosa goshi cikin in-line ta ce " Sharifah da tsaya pls me kike cewa ne akan Shariqah?" Sharifah ta yi murmushi ta ce "abinda kika ji ina fada shine dai abinda nake nufi. Ke dai ki biyo ni kawai ki ji karshen labari. Masana su ka bani shawara akan in kai shi qara wajen hukumar sulhu ta musulumci, su ne masu yin sulhu dan Allah da kuma fadar qur'ani. Da tambaya har na sami inda ofishinsu yake, na je na shigar da korafi. Nan da nan suka neme shi a waya, dakyar ya zo bayan ya gama kamun kafa da wani da ya sani a wajen. Amma maganar gaskiya kuma maganar cikin qur'ani baa canjawa. Aka ce ya dawo min da yara ni na fi cancanta na riqe su. Babbar matsalar da ta afku ita ce, a daren zaa fara kulle gari wato lock down, a lokacin Corona ne kuma a ranar zaa tashi da Azumi. Aka yi ta fama da shi akan ya dawo min da yaran dukka biyar din, saboda ana kan teburin sulhu ne ba kotu ba ce amma ya dage shi bai yarda ya kawo da su dukka ba sai dai ya dawo da kananan guda biyu. Kasancewar dare yayi zaa rufe gari aka tafi akan hakan amma bayan sati biyu zaa bude gari aka ce mu dawo. Yara biyu su na wajena, guda uku su na wajensa sai, ya fito da su daga inda ya boye su ya dawo da su gidansa. Anan ma na sake ganin Shariqah, ta ce min in zo in gani. Ina biye da ita har mu ka isa wani gida mai qofofi guda biyu. Ta bude qofar farko sai na ga haske sosai ga ranta guda biyu wadanda suke wajena kenan, su na ta bacci a cikin ni'ima. Sai ta bude qofa ta biyu sai na ga duhu na hango ragowar yaranta guda ukun da basa wajena, a cikin duhu da damuwa. Daga nan sai ta bace. Kin ga kenan ta na nuna min ga halin da wadancan suke ciki, kuma ta na so lallai-lallai su ma a dauko su kenan." Samha ta fada a bayyane " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah wai me kike cewa ne?" Sharifah ta qura ma ta wasu jajayen idanuwanta da suka cika da kwalla ta ce "wai me kika ji ina fada ne? Abinda nake fada shine kike ji." Samha ta shafa jikinta don ta tabbatar ko tana raye. Eh tana raye tabbas dan ruhinta da gangar jikinta su na tare kawai dai ta na HIRA DA MATATTU ne. In har Sharifah mutum ce toh ba za ta dinga ganin matattu a fili haka ba, sai dai idan ita ma ta mutu din ne. Samha ta sadddakar asan ita kadai matattun nan su ka zaba suke bi suke so a dole sai ta ji labarinsu. Dan haka ya zama wajibi ta sallama ta zauna ta saurare su. Daga nan kuma ta san karshen zancen zasu tafi da ita ne kawai. Ta fara yiwa kanta addu'ar cikawa da imani, da fatan Allah Ya bawa iyalanta hakurin rashinka kawai. Amma ta fara gani kuma ta na jin abin da rayayyu ba sa ji, kuma ba sa gani. Sai kwalla ta cika ma ta ido ta fara ban kwana da rayuwa kuma. Sharifah ba ta damu ko bata ma kula da gumi da dimaucewar da Samha ta shiga ba, sai ta ci gaba da cewa "bayan sati biyu na koma hukumar sulhu aka ce bai zo ba kuma ya qi amsa kiran da ake ta yi masa a waya. Haka dai har sallah ta qarato, ana gobe sallah sai na kwashi yara biyun da suke wajena na aika masa da su. Don su yi sallah tare da 'yan uwansu, na kuma nuna masa cewar ni bani da niyyar raba shi da yaransa kuma shima bai isa ya raba ni da sauran ba. Ya cika da mamakina amma idan ya san wata ai bai san wata ba. Na shammace shi na dawo daukar guda biyun bayan sallah sai na hada guda hudu na tafi da su dan dayar ma tana ciki ne shiyasa ban hada da ita ba. Nima na kai su wani gida ajiya." Samha ta yi murmushin karfin hali ta ce "haba ni fa na san halinki kawata ba kya yafiya." Sharifah ta yi murmushi itama ta ce " bana son rigima amma ya siyo ta da kudinsa wallahi. Ya shigo gidana a gigice yana tsawa yana ihu ya na cewa in fito masa da yaransa. Ko kallo bai ishe ni ba, da shi da wata 'yar uwata suka buga.Ya ce wallahi ba zai yarda ba zai kai karata.