Sashe 16
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** *** *** Bayan wssu kwanaki Aliyu ya dawo daga tafiya ya sami Samha a kwance ba ta jin dadin jikinta, Samira ta zo ta na taya ta zama. Amma a waya babu wanda ya fada ma sa cewar ba ta da lafiya wato dan kada hankalinsa ya tashi. Ya dinga fada musamman akan ba ta je asibiti an duba ta ba. Ko abinci bai zauna ya ci ba ya ce ta tashi su tafi asibiti. Sai da ya sami asibitin gyaneacology mai kyau da tsada sannan ya kai ta, aka bude file. Likita ta duba ta, ta duba abunda yake cikin cikin aka tabbatar lafiya kalau, amma an tabbatar mu su da cewa ba ta cin abinci kuma tana da damuwa da yawa da rashin bacci. Nan da nan Aliyu ya nemi da a ba ta "bed rest" Samha ba ta kaunar kalmar nan ta "Bed rest" dan daga 'bed rest' ta shiga bala'in da bata shirya ba. Ziyarar da Sharifah ta kai musu asibiti. Ta na addu'a wannan karon kada Allah Ya kawo ma ta Sharifah dubiya. Kwanakin Samha biyu a asibiti wannan karon kuwa ta mori bed rest dan ta huta sosai, ta yi bacci ta ci me kyau tana shan mai kyau. Bayan Mama babu wanda ya san tana asibiti balle 'yan dubiya su dame su. Samira ce ke zuwa gida ta taho musu abinci kala-kala ta kawo, Aliyu kuwa duk da ya zama busy amma kullum kafin ya fita aiki sai ya shigo, haka da daddare idan ya taso sai ya biyo ya duba ta kuma ya biya asibiti maqudan kudade. Ana dai cin kudi bana wasa ba amma dai ana ganin kulawa. Abin mamaki da rana misali qarfe goma sha biyu, Aliyu ya dade da tafiya, samira ta tafi gidan Samha dan ta dafa abinci, yayin da Mama kuma sun tafi yobe ita da Ana's gaisuwar mutuwa. Daman su ne kadai suka san tana asibiti,su kadai ne suke zuwa duba ta. Sai ta ji an yi sallama an murda qofa an shigo.Ta dauka ma'aikatan jinya ne wato (Nurses) amma ko su ne ai yanzun nan su ka fita. Me su ka manta, su ka dawo kuma? Wannan tunani na ta ba daidai ba ne wata mata ce ta shigo sanye da atamfa ruwan hoda da gyale shima ruwan hoda (pink color), ta na daga kai su ka hada ido da Sharifah. Yadda ka san bom ya fashe haka karar bugun zuciyar Samha ta kasance. "Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ta fada a bayane. Yayin da Sharifa ta taya ta suka karasa tare. Dan neman magana sai ta qi zama a kan kujerun da suke dakin ta zata zauna a gefen gadon kusa da Samha. Samha ta koma ta kwanta yayin da take numfashi sama-sama.Sharifah ta dauka duk a cikin ciwo ne, sai ta zabura ta riqe ta tana yi ma ta sannu. Ta dora da cewa "haba Samha kada ki dinga jefa kanki a cikin damuwa mana, alhali kina dauke da ciki na 'yan biyu ba ma guda daya ba." Samha ta sake gigicewa, ko ita kanta sai a daren jiya aka fada ma ta cewa tagwaye ne a cikinta. Ta ina Sharifah ta sani? Ita fa ba ciwo ba ne matsalarta, daman Sharifah ce matsalar. Ga matsalar da kanta ta zo har da karin wata babbar matsalar ma, ta kawo ma ta. Samha ta sirnano da hawaye ta na magana cikin sanyin murya ta ce "Sharifah! Ya kamata ki fada min gaskiya, maimakon ki bar ni ina ta wahala. Shin menene labarin karen da ya cije ki har ya zama shine ajalinki kika mutu kika dawo? Yaya ake kike sanin boyayyen al'amari? In har ke mutum ce ba za ki iya sanin ina nan ba. Waye ya sanar miki yara biyu ne a cikin cikina? Sharifah idan na mutu wallahi ke ce sila ba zan boye miki ba, ki na bani tsoro na kasa yarda da ke. Duk sanda na cirewa raina zargi akan ki sai ki aikata wani abu da kwakwalwata zata kasa dauka. Shin kin shiga wata kungiyar matsafa ne da kike iya bacewa ki ke ganin abinda baa fada miki ba?" Sharifah ta kwashe da dariya har kamar za ta shide. Samha ta sake sankarewa a kwace, ta yi saranda ta fitar da rai daga ci gaba da rayuwa. Sharifah ta jawo hannun Samha ta riqe, yayin da jikin Samha ya hau karkarwa. Sharifah ta ce "in har kowa bai yarda da ni ba, na san ke ce kadai a duniya za ki yarda da ni. Ba zan fada miki yadda na san kina nan ba amma lokaci zai fada miki, ba zan fada miki waye ya sanar da ni kina da cikin tagwaye ba amma mu na zaune za ki sani." Samha ta ce " na godewa Allah da Ya jarrabe ni da ciwo. Allah Ya bani mafita. Sharifah ta ce " za ki sauka lafiya ki haife kalau ma in sha Allah." Takaicin da ya sake addabar Samha shine har yanzu Sharifah ta kasa ganewa cewa itace ummul aba isin ciwonta. Idan ta fita daga rayuwata zata warke. Aka jima babu wanda yake magana, Samha dai ta saka hannu ta dafe goshi kamar mai ciwon kai yayin da hawaye ya yi ma ta qawanya daga ido zuwa bayan kunne. Sharifah ta tashi cimak ta linke gyalenta ta ajiye tare da jakarta a gefen kujera. Gami da cewa "an ce in zo in wuni tare da ke, in yi miki hira, in dauke miki kewa." Sai hankalin Samha ya tashi ta kalli Sharifah da gefen ido dan bata da kuzarin waiwayowa. Ta fada cikin sanyin jiki "waye ya ce ki zo ki zauna da ni? Ko dai kin zo ki tare ni ne, nima zan zama ku?" Sharifah ta ce "Mu su wa kenan? Ciwonki ai nawa ne Samha, dan haka ina nan har dare." Samha ta ce " na gode amma da kin tafi gida dan ki kula da yaran nan kanana." Sharifah ta yi dariya ta ce "Ah babu kowa a gidan sun tafi ziyara daga su har Hamidah sai gobe zasu dawo." Samha ta sake fashewa da kuka ba tare da Sharifah ta tabe dan ta juya baya tana ta salati tana fatan ta cika da imani. Wayarta ta dauko ta turawa Aliyu sako ta ce ya yafe ma ta da wuya ya dawo ya same ta da rai. Bai karanta ba sai da aka dade sannan ya kira a gigice. Tambayoyi yake ta jero ma ta ama ta kasa amsawa kasancewar Sharifah ta tsura ma ta idanuwa b ata ko qifatawa. Wa ta magana ya fada sai da Samha ta girgiza. Ya ce "saboda zaman kadaici ne ya sa na je gidan su Sharifah na fada ma ta baki da lafiya, ta zo ta taya ki zama ku wuni tunda Mama ba ta nan yau. Samira kuma in ta tafi sai an ganta dan kada a barki ke kadai babu dadi. Sannan kuma akwai wata tambaya da kika yi min akan Sharifah toh bani da amsar na san a cikin magagin bacci kika yi ta. Na tabbatar ba zai wuce labarin da Sharifah take ba ki ne, ba ku gama ba shine abin ya tsaya miki rai. Kika ce min baqin kare ne ya ciji Sharifah sai ta kwanta ciwo. Ni ba na so ki dinga saka abu a rai shiyasa nake so ta zo ta karasa baki labarin baqin karen." Haushin Aliyu ya rufe ta yayin da suka tsurawa juna ido ita da Sharifah. Duk da ma dai ta san Sharifah bata jin abinda yake cewa Samha ta kasa cewa komai. Wato Aliyu ne da hannunsa ya dauko ma ta ajalinta ya kawo ma ta. Ai shikenan zai ga karshen labarin baqin kare kuwa idan zuciyarta ta karasa fashewa, zai zo ya dauki gawa. Samha ta kashe waya ba tare da ta iya bashi amsa ba. Ya sake kira sai ta qi amsawa, da ya kira a karo na uku sai Sharifah ta dauka ta amsa Ta na dauka ta ce " Aliyu ina tare da ita kada ka damu, yau zamu sha labari da kawata. Ka ci gaba da aikinka ga ni ina kular maka da ita." Ya yi godiya ya yi ma ta sallama cikin jin dadi. "Tashi ki zauna in baki yogot ki sha, na ga ga kaji ma ga fruits. Da yake a gigice na taho ban tsaya na saya miki komai ba amma kada ki damu gobe zan kawo miki kwadon zogale, kin ji qawata." Samha ta qi tashi ta zauna, sai da Sharifah ta dame ta da magiya sannan ta tashi ta zauna. Sai ta ji tsoron da take tsananin ji na Sharifah ya ragu, tunda yanzu ta san wanda ya bawa Sharifah labarin tana asibiti da kuma tagwayen da suke cikinta. Tare suke shan kayan marmarin akan gado suke zaune, su na fuskantar juna Samha ta ga gara ma ta tsaya ta saurari labarin Sharifah akan ta mutu saboda zulumi. Samha ta kalli Sharifah da gefen ido cikin rashin fara'a ta ce " ki bani labarinki da na Fanna, Musamman yadda baqin kare ya cije ki." Sharifah ta yi murmushi ta ce "tabbas na yiwa mijinki alqawari yau zan zame miki radiyo mai jini za ki sha labari kuwa kala-kala, da na nan da na can ." " Can ina? Samha ta tambaya cikin rashin tsoro. Dan abin ya zame ma ta dole ma ta tsaya ta ji. Sharifah ta ce "duniyar rayayyu da duniyar matattu." Samha ta gyada kai ta ce " na shirya sauraro. " Ta na rufe bakinta Nana Anmad da Maryam Alqali ne suka murda kofa suka shigo hannayensu dauke da fulasan abinci. Da faraa suka shigo sai kawai aka yi ido hudu da Sharifah da Samha da su. Su Nana suka yi turus sula ja da baya su na zare idanuwa su kalli Sharifah su juya su kalli Samha. Nana ta zabura ta ce " A a ba wannan dakin muke nema ba." Sharifah ta ce "Nana nan ne mana ku shigo." Ta taso da sauri za ta tare su. Wani uban tsalle da wuntsulawa gami da zubar da fulasan hannu su su ka yi sannan su ka fafara da gudu. Sai