← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 23

Sashe 13

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce masa bismillah. Sai na sami sammaci daga Hukumar Sulhu ta musulumci yana karata akan na je har gidansa na kwashe yara na boye. Tarihi ya maimaita kansa ashe babu dadi. Daman su ma su na nemansa ya qi zuwa, yanzu da ya ji wuya ya kawo kansa. Da ranar ta zo sai na je ana masa kira na tafi da yan uwana ya tafi da nasa. Aka fara magana irin ta sulhu, aka tabbatar masa sai an bi dangin uwa goma sha daya sannan aka ambaci mahaigiyarsa ba ma shi ba. Aka ce ya dawo da dayar ya bawa wata yar uwata ita ce babba nima in kawo yaran wajenta. Amma tun a ranar na fara gane wasu daga cikin dangina da na sami barka su na bayansa. A ranar wasu suka bayyana na gane basa tare da ni. Aka dinga kai kawo a Hukumar sulhu ta musulumci yayin da yake samun rakiyar wani wanda ba ma dan uwansa ba ne, shine aka wakilta ya tsaya masa dan kada in yi rinjaye akansa. Sunan dan zugar Idris ya dinga juya magana, sai an zo matsaya sai ya dawo baya har su ma hukumar suka gane shi, su ka tabbatar baya son ayi sulhu, dan basa shiri. Da aka tutsiye shi sai su ka gane bai san komai a addini ba ma amma yana ikirarin shima malami ne. Ashe da Adamu ya kwashe yaran gidansa aka kai su aka boye, su ka sami abin duniya, a sati ukun da yaran su ka yi a gidansa sai da aka azabtar da su da yunwa da kyara. Aka yards zaa bani yaran dukka amma dokokin da aka saka min su ne: zan tashi daga gidan da nake zaune in dawo gidan iyayenmu wanda shine gidan da na gada ni da Shariqah da Bello sannan duk karshen sati zai dinga kwasar yaran zuwa gidan sa jumaa zuwa lahadi da yamma. Ban yarda ba saboda babu tarbiyya ga yaran da suke da gida biyu. Anan dai aka daddanne ni aka in yi hakuri in yarda akan hakan dan an fi wata guda ana zarya. Na rasa dalilin da ya sa zaa tashe ni daga gidan da nake a kai ni wani gida alhali ba shi yake biya min hayar ba. Bello ya fi son hakan da wasu daga cikin dangi suka ce in yi hakuri, zaman hayar ma bai dace da ni ba daman saboda Allah ya rufa min asiri ai saukina ne. Na san halina ba zan iya zama a gidanmu ba kasancewar gini ne irin na da, komai ya kwararrabe. Na fitar da kudi mai yawa na fara gyaran saman gidan kusan komai sai da na fitar da shi na zuba na zamani. Mu ka tafi a haka, da na gama gyara na kaura can. Ya na aikowa duk karshen sati ana kai su. Amma sai ya shiga zuga su akan kada su yi min biyayya wato idan na gaji da halinsu sai dawo da su. Uba ne da hannunsa yake batawa yaransa tarbiyya innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Ya ce in sun shigo gidan kada su gaida kowa su sha kunu su wuce daki. Sannan ni bani da kirki ban tsinanawa uwarsu komai ba bana kaunarta. Ki duba ki ga wannan al'amari yana so ya wanke kansa alhali yaran sun san komai." Samha ta dafe haba ta ce " ikon Allah wannan wanne irin mutum ne kenan?" Sharifah ta ce "sai lokacin nima na gane haqiqanin halinsa na gaskiya. Dukka a dalilin haushin na qi yiwa Dinar auren dole. Ashe ma rigima baa fara ta ba sai a gaba. Ya na ta jin haushina akan nasarar da na yi akansa an bani yaran kuma babu yadda ya iya. Sai ya shiga ba su wulaqantaccen abincin da ya tabbatar ba zai ishe su ba kuma ba masu kyau ba. Dukkan abinda aka yanke masa ya ki bin doka. Ko kallonsa ban yi ba kuma ban koma na kai kararsa ba. Allah Ya dinga bude min ta wasu hanyoyi daban-daban ina ciyar da su. Bayan duk an yi haka ina zaune sai kawai na ga an kawo min sammaci daga wata kotu, anan birnin Kano mai nisan gaske daga unguwarmu wanda a ka'ida gidana da gidansa su na kusa da juna ya kamata ya kai kotun da tafi kusa da mu amma aka tafi wata unguwa da take karshen garin Kano. Sai na yi tafiyar fiye da awa guda kafin in kai. Ya na karata akan rabon gado, na rasa dalilin wannan karar, ga gado nan a hannunsa suke yana karbar kudin hayarsu. Gida daya ne mu ka yi hadaka da ita ni da Bello kuma a ciki muke zaune. Na nemi shawarar masana dan su bani shawara dan ba san kotu ba, ban taba zuwa kotu ba ko da rakiya ma. Da farko aka ce in dauki lauya nima, dan shari'ar yanzu in ba ka da lauya daman ka bar maganar samun nasara ma kawai. Sai daidaiku ne suke nasara. Na sami lauya na biya shi ya je kotu aka fara shari'a muka saurari dalilin karar. Wai ya na kara akan rzbon gado ya zayyano komai, har da wanda guda biyu ne kadai muke hadaka da ita . Sai kuma na ji an kinkimo wani gidana an saka a cikin lissafin. Gidan nan nawa da ne taba siyar ma ta sannan ta sake siyar min, cikon kudi kadai zan yi ma ta . Babu wanda bai san labarin ba har shi kansa ya san komai amma anan ya ce na ta ne. Mu ka mayar da martani akan ba haka abin yake ba. Abu kamar wasa sharia ta miqe ana ta zuwa kotu ba kakkautawa. Shi yana da kudin da yake ta biyan lauyansa ni ce yake so ya saka a wahala amma da yake Allah ba azzalumin bawanSa ba ne na dogara ga Allah. Hakan bai ishe shi ba sai su ka fara saye dukka lauyoyin da na dauka . Akwai lauyan da bai fada min ba zai yi ba sai ana gobe zaa je kotu sannan ya kira ni a waya ya ce ya janye. Yaransa su na ganin office din su ka ce sun taba zuwa da babansu. Wato ya siye su, lauyansa ke karbar lambarsu a kotu ya bi su ya siye su. Ana cikin wannan hali sai na sake jin kira daga wata kotu ta daban an kawo min sammaci, ita ma mai nisa ce sosai daga gidana. Ita kuma yana kara ta akan karbar yaransa." Samha ta dafe kirji ta ce " innalilahi wa inna ilaihi rajuun. Sharifah irin rayuwar da kika shiga kenan? Amma hada zuria da irin su Adamu ya zama masifa wallahi." [3/5, 8:12 PM] Jamila Umar Tanko: 6 Sharifah ta tabe baki ta ce "mutumin da ya wulakanta matarsa tana raye kina ganin zai ji kunyar wulakanta ta ne bayan ta rasu? Ai duk abinda yayi min ba ni ya yiwa ba Shariqah ya yiwa....." Ba ta rufe bakinta ba wayarta ta dauki ruri sai ta dauko ta amsa, Fanna ce akan layi. Nan da nan sai Samha ta firgice dan a halin yanzu ta fi jin tsoron Fanna ma akan Sharifah. Sharifah ta ce "Fanna ga fim dinki ina kallo fa 'walking dead', a MBC 2 na tabbatar shi kike kallo kema ko dan na jiyo saurin?" Fanna ta ce "Ah ai ba zai wuce ni ba, ina son shi sosai." Samha ta ji kirjinta yana bugawa ta ce a ranta "me ya hada mata da son kallon fim din Matattu? In ba rami me ya kawo rami ?" Sharifah ta ci gaba da cewa "Fanna ya kike? Yaya yara? Meye kike so ki fada min rannan? Hamidah ta ce kina ta kira kin ce in kira zamu yi magana." Fanna ta fara magana, Samha ta na jiyo ta tana ta ambaton sunan Samha da Nana, sai ta tabbatar akan maganar rannan ce. Sharifah ta dago da sauri ta dubi Samha. Toh fah akwai magana kenan sai Samha ta ji hankalinta ya tashi da alama ta shiga tarkon fatalwoyi, shikenan Sharifah ta san har yanzu ban gama yarda da ita ba duk da labarin da ta ba ni. Wai ni wanne tsausayi ne ma ya kai ni yin qawance da Sharifah da Famna ne ma?" Samha ce ta fada a ranta. Sharifah ta qurawa Samha ido tana kallo yayin da take sauraron Fanna tana ta magana. "innalillahi wa inna ilaihi rajuun. Wanne tuggu kanuriyar nan take hada min ne?" Samha take karantowa a zuciyarta. Sharifah ta katse Fanna ta ce "ina tare da Samha ma yanzu haka, in kin amince zan saka ki a hand's free sai mu yi hirar tare." Fanna ta ce "ah ai na fi son haka ma daman, ina neman Samha dan ina ta kiranta a waya ma ba ta amsawa." Sharifah ta taso daga kujerar da take zaune ta zo kusa da Samha ta zauna yayin da ta bude muryar Fanna wacce take ta magana. Fanna ta ci gaba da cewa " Samha Ya kuke? Ina sauran kawayena su Nana?" Samha cikin tsoro da takura ta ce" lafiya kalau mu ke Alhamdulullah." Fanna ta ce "rannan mu na labari da ku sai kuma ku ka ajiye min waya babu sallama. Na dauka ku na neman ilimi ne akan rayuwar matattu." " Hmmm! Hmmm!!" Kawai Samha ke fadi ba tare da ta iya bada amsa ba. Fanna ta ci gaba da cewa "wai ni kam shin menene abin tsoro ne a fatalwa? Fatalwa mutum ne fa kamar ku, ya mutu ne kawai sai kuma ya tashi ya zo wajen kawayensa ko 'yan uwansa dan ayi zumunci. Har na ba ku misali da ni kaina na ce kamar ni din nan da na mutu kuma na tashi. Ko ba haka ba ne Sharifah? Kuma ke ma ai kin yi ciwo kika mutu kuma kika dawo ko?" Abinda ya daurewa Samha kai ya kara bata tsoro shine amsar da Sharifah ta bata. Sharifah ta gyada kai ta ce " Haka ne Fanna." Sai Samha ta zabura ta matsa daga kusa da Sharifah, ta ga ma dai gara ta tashi kacokan daga kusa da ita. Ta fara tunanin nemo mafaka dan dai wannan abu ya wuce tunaninta. Fanna ta
Chapter 13 · 0% Book details