Sashe 5
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** *** *** Bayan wasu kwanaki ne qawayen Samha su ka hadu su dukka suka zo gidan Samha. Anan aka tayar da magana aka dinga hayani, maryam da Nana dai an basu laifi an ce ba su kyauta ba akan tsoronta da suke ji bayan sun tabbatar ba fatalwa ba ce yanzu. Samha ta na daga kicin ta na tsomo baki. Ta yi musu girke-girke kala-kala daman ita cikakkiyar chef ce har ma tana da makarantar da take koyar da girki. Ta na son girki kuma ta iya girki, tabbas ta sha karbar kambun yabo idan aka yi gasa ita ke cinyewa. Sunanta ya yadu ya bazu a fadin birnin Kano da ma arewa baki daya. Ashe da walakin goro a miya shiyasa dangin Aliyu su ka kasa yin nasara wajen tursasa shi akan ya rabu da ita ya auro wata. Ya qi fur ya ce shi sai Samha ita kadai. Allah sarki ya ce haihuwa ta Allah ce, tunda likita ya tabbatar mu su shi da ita dukka lafiyarsu kalau lokaci kawai suke jira. Ga shi kuwa lokaci ya zo, bai yi garaje ba, ya yarda da cewa baa yiwa Allah shishshigi, baa yi maSa tilas. Allahu akbar! Mai yadda Ya so a lokacin da Ya so. Su Nanah su ka ci su ka yi haniqan har da ma su daukarwa miji da yara a 'yar roba, saboda dadin abincin ba zasu taba iya dafa irinsu ba. Samha ta saba ganin hakan dan haka baya bata mamaki, dan duk wanda ya ci abincinta sai ya yi santi kuma sai ya so ya kaiwa masoyansa su ma su dandana. Amma fa ba dukka abincin ta kawo musu ba, ta ware na Sharifah daban ta adana a kicin. Abincin me yawa kuwa kasancewar ta ga su na da yawa, ga yara, ga Bello. Samha ba ta karbi lambar wayar Sharifah ba duk da ma alamu sun nuna ba ta riqe waya, sai wata karamar waya ce a hannu Hamidah. Amma dai za su yi shahada su je sun san ko ba ta gida yara na gida tunda akwai makaranta islamiyya da boko, ba za ta fita da su ba. A mota daya su ka dunguma suka tafi wato motar Nana ita ce babba. Su ka isa gidan Sharifah suka iske Bello ya fito zai shiga motar nan da su Nana su ka ga Sharifah a ciki a wajen barista, ashe motar Bello ce. Ya kalle su ya kawar da kansa gefe, kafin ma su sami waje su gyara tsayuwar motar, ya shige motarsa ya tafi, da alama har yanzu haushinsu yake ji musamman ma Samha. Su ka fito suka iske get din a rufe, sai su ka cika da fargabar ko babu kowa a gidan. Wadanda har yanzu zuciyoyinsu basu gama yarda da cewa ba gidan fatalwa ba ne, suka ji fargabar kwankwasawa yayin da wasunsu irin su Samha gaba gadi suka hau bugawa. Sai can da jimawa suka jiyo motsin tafiya, aka zo aka bude. Hamidah ce ta bayyana wannan karon idanuwanta sun yi jajawur, alamar ta sha kuka. Su Nanah su ka daka tsalle suka yi gefe, Samha ta harare su alamar su daina yin abinda suke yi haka. Samha ta rungume Hamidah ta na lallashi ta tambaye ta ko lafiya take kuka? Amsar ita ce "babu komai." Samha ta ci gaba da lallashinta akan ta fada ma ta abinda yake faruwa. Amma Hamidah ta dage ta ce ita babu komai. Samha ba ta yi mamakin kukan da Hamidah ke yi ba, saboda ta ji labarin shakuwarta da Shariqa dole har yanzu ta yi kukan rabuwarsu. Samha ta tambaya "Mamarku na cikin gida?" Hamidah ta gyada kai ta ce "Eh ta na sama." Samha ta kama hannun Hamidah su ka yi gaba tana ci gaba da ba ta hakuri da yi ma ta nasiha akan ta yi hakuri, kowanne mai rai mamaci ne. Mu dukka anan wataran za mu mutu mu tarar da su acan." Su Nana su na ta jan kafa su na tafe su na sanda yayin da zuciyoyinsu ke karkarwa. Har yanzu gidan tsoro yake basu duk da dai an gyara, ba irin yadda su ka gan shi rannan ba, ada dai ga duhun bishiya, ga na datti da kura amma yanzu fes da shi. Su ka hau sama cikin wani katafaren falo mai girman gaske kuma ya tsaru kamar a turai. Sai mamaki ya rufe su, ai basu taba zaton har da gyararren waje a gidan nan ba, sun zaci kwango ne kawai. Kowacce ta sami kujera ta zauna yayin da suka bawa Hamidah fulasan abincin da suka kawo mu su, ta karba gami da godiya sannan ta dora akan dining table, ta koma gefe ta tsaya. Sun tambaye ta ya fi a kirga shin ina Mamarta take dan ba su ganta a falo ba, sai Hamidah ta yi shiru ba ta ba su amsa ba. Ba su ankara ba muryar Sharifah su ka jiyo a daya daga cikin dakunan. Ta na magana cikin fushi da daga murya ta na cewa "ke 'yar uwata Shariqah ki koma ki kwanta. Na rantse da Ubangijin da Ya busa min numfashi kuma Ya raya ni nake yawo a doron kasa, kuma Shine Ubangijin da Ya dauke miki numfashi kina kwance a karkashin kasa, ba zan bari 'ya'yanki su wulaqanta ba. Ki koma ki kwanta, ki koma ki kwanta na ce , ki je ki huta abinki. Wannan yaqin na rayayyu ne ba na Matattu ba ne." Daga Samha har kawayenta su ka daka tsalle suka miqe tsaye, yayin da su ka bazama neman kofar da za ta sada su zuwa waje. Aka hau damben bude qofar da ta qi buduwa sai da kyar. Su ka falfala da gudu kai ka ce gudun famfalaqi suke yi, ba su tsaya a ko ina ba sai da suka gansu a farfajiyar kofar gida a bakin motarsu. Huci su ke musamman Nanah 'yar lukata. Ta na ta huci ta zaro mukullin motar daga cikin jakarta ta ce sai dai wata ta karba ta tuqa. Ta ci gaba da cewa "Samha ai na fada miki Sharifah ba cikakkiyar mutum ba ce, kika nece kika ce kin tabbatar mutum ce, ai gashi nan zaa kashe mu." Samha ta na ta nishi ta dafe kirji ta ce " Sharifah daman ta fada min, bayan ta yi rantsuwa da Ubangijin da ya halicce ta Ya halicci Shariqah ta ce tana magana da Shariqah fuska da fuska kamar yadda take magana da ni. Ta sake yin rantsuwa cewa Mamaci ya na sanin abinda yake faruwa a duniya kafin mu bil'adama mu sani. Ta ce idan malaman garin nan ko na duniya kaf zasu taru akanta su karyata ta ita fa ta fada ba za ta janye ba, cewa mamaci ya san abinda yake faruwa a duniya saboda ita ganau ce akan Sharqah ba labari aka ba ta ba." Maryam ta zabura ta dafe kirji ta ce "wato dai yanzu Shariqah na cikin dakin da Sharifah take magana, tare suke hira kenan? Ban taba ji ana HIRA DA MATATTU ba sai a yau. Mun shiga uku, innalilahi wa inna ilaihi rajuun.Wannan wacce irin Sharifah ce mu ka kwasowa kanmu?" Hamidah ce ta bayyana a bayansu har yanzu idanuwanta na cike da hawaye sun yi jajajur abin tsoro. Sai su ka razana su dukka, har wasu sun ruga da gudu baya mota sun sami mafaka. Hamidah ta sharce hawaye cikin sanyin murya ta ce "Mamana ta ce ku hawo sama, ta fito falo yanzu, ta na jiranku." Aka hau kalllon-kallo a junansu. Nanah ta yi karfin hali daga nesa ta ce "wacce Mamar ta ki daga ciki Sharifah ko Shariqah?" Maryam ta nisa ta ce "tab! ai ni kam sai dai a kai gawata cikin gidan nan kuma." Samha ta yi sauri ta katse su dan ba ta so su sake ganewa har yanzu a fatalwa aka dauke su. Ta ce " 'ya ta Hamidah ki fadawa Mamarki wani emergency kira aka yi mana zuwa asibiti. Ki ce ma ta za mu dawo a cikin satin nan in sha Allah. Ga abinci nan na dafa mu ku. Ku ci ke da kanananki. Su na ina ne ban gansu ba?" Hamida ta sharce hawaye ta ce " ba sa nan an sace su." Samha ta zabura ta dafe kirji ta ce "an sace su kamar yaya?" Muryar Bello su ka ji a bayansu ya dakawa Hamidah tsawa ya ce "ke Hamidah! shiga gida kuma ki saka sakata kada in kara ganin kafarki a waje." Jikinta na rawa ta shiga gida. Su ka juya su na kallonsa, ya na zaune a cikin motarsa yayin da ya wurgo musu wata uwar harara. Nan da nan kowacce ta hau laluben kofar shiga mota. Samha ce ke tuqawa dan Nana ta sha aradu ba za ta iya tuqi ba. Aka yi shiru babu wacce ta ke magana sai zulumi da tunani. Abin ya fi bawa Samha mamaki dan ada ta yarda Sharifah mutum ce dari bisa dari amma ta yaya take iya yin HIRA DA MATATTU? Su daman su Nana basu gama yarda Sharifah mutum ba ce dan haka ba su yi mamaki da yawa da ta fito a wata sabuwar sigar ba. Innalilahi wa inna ilaihi rajuun kowacce ke kira. Samha tuqi take kamar za su tashi sama saboda zuciyarta tafasa take ta yi kawai, wannan labari ba za ta iya fadawa Mama ko Aliyu ba dan za ta iya saka babban kokonto a ransu bayan sun cire zargi a baya. Nanah ta yi ajiyar zuciya ta ce "Samha yanzu duk nacinki dai za ki rabu da Sharifah ko kuwa har yanzu za ki sake bata wata damar kuma? Ni dai na gama, na sallama ta, na hakura da kawancen nan, kawaye har sun yi min yawa dan na rasa ta ba komai, ni dai na yafe." Maryam ta zabura ta ce "ai ko ita kadai ce kawata a duniya na yafe ma ta wallahi, itama ta yafe min mu yi sallama." Rukayya ta yi ajiyar zuciya ta ce " daman ni da Sharifah ba shiri mu ke yi ba tun a jami'a, dan ta ga tana da kokari a jami'a ina cewa ta koya min karatu sai ta dinga yi min wani