← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 23

Sashe 17

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sharifah ta daga da fulasan daga qasa, Allah Ya sa basu bude abin ciki ya zube ba. Ta bude kofa da sauri ta leqa, babu su babu kamanninsu. Sharifah ta juyo ta kalli Samha cike da mamaki ta ce "kin san idanuwana ba sa gani sosai, kamar Nana Ahmad da Maryam na gani." Samha dan dariya har sai da ta kwanta, ta san abinda suka gani suka gudu. Samha ta fada a ranta "Su ne mana, amma nima na yi mamakin yadda ta gansu. Ban san wanda ya fada musu ba ma ina asibiti. Sharifah ba ta damu ba amma tabbas ta gane abinda ya sa suke gudu. Ta bude fulasan biyu sakwara ce a daya, dayan kuma miyar agushi ce ta sha kaji da kifi. Samha ta ce a zuba ma ta za ta ci sai Sharifah ta zubo musu tare. Samha har yanzu dariya ce take cin ta, amma sai ta dinga kunshe baki tana yi a ciki-ciki. Su na cikin cin abincin, wannan karon a kan kafet suka zauna suna ci. Kamar daga sama Sharifah ta ce "su Nana Ahmad da Maryam Alqali kenan. Manyan gari Hmmmmm. Na gane su fa tun ba yau ba." Samha ta na ta kawar da maganar dan bata so a yi amma Sharifah ta ci gaba da yi. Ta ce " basu san Sharifah ba ne ganinta kawai suke yi nesa-nesa amma nan gaba za su santa." Samha shiga gyara magana sai murmushi kawai Sharifah take yi. Sharifah ta ce "labarinmu mun tsaya a daidai in da na ce na amsa kira kotu ta biyu da ya kaini aka ce ana qarata ne akan in dawo masa da yara saboda ina da aure dan haka raino ya saraya a kaina. Ba ni da lauya ni kadai nake zirga-zurga daga wannan kotun zuwa waccan. Dukka dangina wasu 'yan mata ne guda biyu da muke uba daya su ne suke tare da ni, sauran kowa ya yi shiru har ta da Bello ya koma gefe ya zuba min ido, shi ya fi so in bar masa yaransa kawai ni kuma na ce ba zan taba bari ba. Cikar dangina da batsewarsu babu wanda ya kira Adamu ya ce masa bai kyauta ba akan wulaqancin da yake yi min ba, sai ma wasu sababbin informations da zai yaqe ni yake ta samu daga gare su. Ikon Allah kawai na tsaya ina kallo, na yi ta tunanin laifin da na taba aikatawa dangina na cancanci wannan hukuncin. Amma sai aka ce min wadaka da kudi yake yi musu, amma ban taba dauka cewa kudi zai sayi zumunci ba. Kuma ban taba sanin Adamu mai kudi ba ne dan na ga gidansa bai wadata ba ni ce ma nake yin aikinsa da bai sauke ba. Saboda a bi bayansa dan ya wulaqanta ni kudi yake ta rabo da kayan abinci da kayan dadi, har da ragunan sallah. Aka yi min wata irin Shari'a wacce ban gane ba zuwa biyu kacal mu ka yi, aka ji ta bakina sai kawai aka yanke hukunci aka ce an ba ni mako guda kacal in kwashi yara in mayar da su tsakar gidan ubansu. Lallai kuwa tunda na kima hijabi har qasa, gashi na kode na jejjeme ai dole su yi zaton bagidajiya ce. A take na bude baki a gaban kotu na ce ban yarda da wannan hukuncin ba, kuma ina neman kwafin Shariah zan daukaka kara." Wannan kalma tawa ce ta tabbatar musu da na san abinda nake yi ashe. Samha ta tafa hannu ta ce da kyau 'yar gidana na jinjina miki." Sharifah ta yi dariya ta ce "na rantse da ubangijin Musa da Haruna a lokacin na fara jin wani qarfi da rashin tsoro. Tabbas na ga mata a kotu su na ta wahala, ga rashin ilimi, ga rashin karfi, ga rashin wayewa kuma su na da gaskiya an danne musu haqqunansu amma basu da lauya basu da cikar kamalar da zasu iya tsawa su yi bayani. Abin tausayi, ya kamata idan akwai lauyoyi musamman lauyoyi mata da zasu dinga leqawa irin wadannan kotuna su na bibiya su taimakawa irin wadannan matan. Ina fitowa bakin kotu na hadu da mazigin nan da na fada miki a baya mai suna Idris, ya na murna sun yi galaba akaina. Na ce masa "ka gama murna amma ka sani babu kotun da ta isa ta raba ni da yaran nan. Ka je ka fadawa Adamu ni da shi sharia yanzu muka fara." Na fada da karfi cikin daga murya sai da kowa na cikin kotun ya waiwayo. Muryata radau har cikin kotu kowa yana ji. Bana tsoron kowa a lokacin banqi duniyar ta kife ba." Samha ta gyara zama ta ce "toh yaya aka yi kuma?" Sharifah ta ce "na shiga ofishin wani abokina lauya da yake babbar kotu wato high court a fusace na rufe shi da fada na ce ka na garin nan amma samun lauya daya da zai tsaya min ya gagara. Kai me kake yi da ba za ka tsaya min ba?" Ya ce "ni lauyan gwamnati ne ba zan iya tsaya miki ba amma ki kwantar da hankalin zan hada ki da wani lauya mai mutunci, malami ne, mai tsoron Allah shine na tabbatar idan ya ce zai yi zai yi, ba zai taba yarda su siye shi ba." Na yarda da maganarsa tunda ya ce tabbas shi mai tsoron Allah na san na gama dacewa. Ya kira shi a waya su ka yi magana sanan ya bani lambar wayarsa da addireshin ofishinsa wannan lauya shine Inuwa Ahmad. 'Yar uwata ce ma take ta kuka a lokacin, ni kuma na ce wallahi ba zan yi kuka ba, na daina bata lokacina in yi kuka akan mutumin da bai san darajar matar da ya aura da 'yayan cikinsa ba. Wallahi in raina zai salwanta a cikin yaqin nan, na yarda akan ina raye ina kallon yaran Shariqah su na wulaqanta. Dan shi ba irin uban nan da na san zai kula da yaransa ba ne, haka gidansa ba irin gidan da zaa kai yaro ba ne ya rayu, matar da bata kula da na ta yaran ba ma tayaya zata kula da yaran wata. Wacce ta tsana ma basu zauna lafiya ba. Ya na yi ne dan ya wulaqanta ni sai dai Allah bai wulaqanta ni babu mahalukin da zai iya wulaqanta ni. Ki hasko min maganar jifa irin na asiri, bana duba ba na zuwa a duba min amma Allah Ya na nuna min komai a mafarki, ka na taba ni zan ganka. Ko a suffarka ko a suffar wata dabba mai cutarwa amma a ko wanne hali ko da dakyar ne dai ina kubuta, baa samuna na. Ina da nacin addu'a da kuma tsarkakekkiyar zuciya. Ban cuci kowa ba Allah ba Zai bari a cutar da ni ba . Masu bani shawara su na bani shawara akan in bazama neman magani a wajen malamai, in tashi tsaye da addu'a akan in yi rinjaye akansa a Shari'a, bayan haka kuma kowa ya dube ni ya san ana jifana da asiri asiri a jikina Ba na kuraje amma a lokacin wasu kuraje suka feso min, ciwo kala-kala da kasala da bacin rai. Samha kin san ni nima na sanki, bin malamai da bokaye ba aikinmu ba ne. Ko da an takura ni na yarda na je to sau daya zan je kuma ba zan koma ba, sai in ga kamar na zubar da gaba daya imanina ne sai na yi sabuwar kalmar shahada. Abu daya na riqe shine in tashi cikin dare in roqi Ubangijin da Ya busa min numfashi, Ya raya ni, wanda raina ke hannuns Sa kuma idan na mutu gare Shi zan koma. Shi yake da wuta kuma yake da aljanna. Tunda kuwa na yi imani da haka na watsar da neman taimakon kowa, na daina bacci cikin dare, na dingi tashin dare ina rokonSa, Shine sarkin sardauna. Nayi imani da Shi, abu na farko sai na daina fargaba, na daina tsoron kowa. Duk wanda ya dogara ga Allah Shi kadai baya tsoron faduwa sai dai nasara a komai. Haka baya neman taimako daga wajen kowa sai Allah dan haka ya wuce wulaqanci. Baya gudun ko wani zai iya cutar da shi. Zai ji kamar duk duniya ya na daidai da kowa ko da kuwa bashi da ko Sisi ko wani mai karfi. Zai ji a ransa zai iya tunkarar kowanne irin bala'i da ake binsa da shi. Zai ji zuciyar ta washe babu haushin kowa. Baya tsoron talauci ko ya ce wani zai juya masa baya ya hana shi wani abu. Baya tantama ko kokonto akan abinda ya saka a gaba. Kawata na ga aya, na ga mu'ujuza da isa irin ta Ubangiji. Da na matso kusa da mahalaccina Allah da Shi nake magana cikin dare ke kya ce ina ganinSa a gabana tabbas Shi Yana kallona idaniyata bata ganinsa amma ruhins da zuciyata su na tare da shi 100%. Bayan na yi sallar nafilfili ina yi masa kirari da kyawawan sunayensu tsarkaka guda casa'in da tara, sai in yi tawasali da kyawawan aiyukan da na aikata daga ni sai shi, bayan na tuba kuma na yiwa masoyi salati SAW sai in yi magana da Ubangiji ke kya ce ina ganinSa, tabbas shi Ya na ganina amma zuciyata tana hasko shi. Buwayi gagara misali. Na ce "Ya ubangijin kai ka halicce ni, bani da kowa bani da komai sai kai kuma da kai kadai na dogara, kai ne ka ce mu roqe Ka, za ka amsa mana. Allah ka tsaya min da kanKa kada Ka bar ni da iyawata daidai da kiftawar ido dan ba zan iya ba." Samha ta ce : Allahu akbar! kawata na ji har tsikar jikina tana tashi. Tabbas ba kowa ya gane wannan sirrin ba. Dogara ga Allah Shi kadai babbar nasara ce." Sharifah ta ci gaba da cewa "Allah Ya nuna mu su Shine Allah kuma baYa mantawa da bawanSa a lokacin da bawa Ya tuna da mahalaccinSa, na rantse da Allah Samha mai Shari'ar farkon nan kacokan aka dauke shi daga alkalanci ba zai sake alqalanci ba ma a duniya. Shi kuma dayar kotun da ya ce zai kwace yara shine kika ganni a
Chapter 17 · 0% Book details