← Book details Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 23

Sashe 22

Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta ce "daman ana mutuwa a dawo? Ai rai daya ne idan ya tafi ya tafi kenan, in kin ga an mutu an dawo daman suma ne ba mutuwa ba. Toh ni ban suma ba amma an cire rai da ni. Wannan hausar Fanna ce ta yi miki sai ki yi ma ta uzuri tunda ba bahaushiya ba ce da ta ce na mutu na dawo. Amma ita a nata matsalar ta yi ciwo sai ta yi doguwar suma har an hada ta zaa kaita sai ta farfado. Wannan baya nufin ta mutu ta dawo ko ta yi fatalwa." Samha ta gyara zama ta na daukar ilimin da ba ta sani ba a baya. Ta ce "Shariqah doguwar suma ta yi kenan baa sani ba aka binne ta tunda tana dawowa duniya kuma ki yi hira fuska da fuska a bayyane." Sharifah ta yi shiru kamar mai tunani sau ta dauko wayarta tana daddannawa, ashe Bello ta kira a waya. Tambayarsa ta yi yana ina? Ya ce yana gida yana jin yunwa. Ta ce ya bari zata taho masa da abinci Samha fa jiran amsa take amma Sharifah ta qi maganar har ta fara hada kaya za ta tafi. Samha ta jawo hannunta ta zaunar ta ce " wallahi ba za ki tafi ba, sai kin bani labarin yadda kike yin "HIRA DA MATATTU ". Sharifah ta kwashe da dariya ta ce " hirata da Shariqah ta qarshe ita ce da ta kira ni a waya na hangota a zaune karkashin kasa, ni kuma ina zaune a cikin dakina anan ina duniya. Na ce Shariqah so mu ke mu ganki." Ta yi dariya ta ce "idan ku ka ganni ai guduwa za ku yi. Yanzu na zama ba irinku ba." Daga ranar ban sake ganinta ba sai lokacin da na fara ba ki wannan labarin, na ganta ta zo kofar gidana, na kamata na kai ta wani gida mai kyawun gaske da gado a wani daki mai haske. Na ce ta kwanta zan koma in kawo ma ta yaranta, sai ta ce a a kada in kawo ma ta su za ta dawo da kaita ta kwashe su amma ba yanzu ba." Sharifah ta miqe yayin da ta yafa mayafinta ta dauki jakar ta rataya. Samha ta tabbatar zata cutu in har Sharifah ta bace bata gama bata wannan amsar ba, abin zai yi ta damunta. Sai ta sake cafke mayafi Sharifah ta riqe gam ta ce "wallahi baki isa ba sai kin fada mun yadda matacce yake kira a waya daga cikin kabari har a yi hira da shi a waya." Aliyu ne ya shigo ya iske su ana kokawa, Samha ta damqe ta ita kuma ta na kokarin kufcewa Ya cika da mamaki amma sai ya ga su dukka dariya suke yi. Ya yi dariya ya ce "Lafiya kuwa? Lallai kun ci kun koshi har dambe ku ke?" Sharifah ta ce " matar nan taka yau ta karar min da dukka karfina wajen bata labarina, na gaji da magana, nace ma ta zan tafi shine wai zata hana ni." Samha ta ce " dan Allah Yah sheik ka saka sakata ba zata tafi ba sai ta bani amsa. Kai ne fa ka ce ta zo ta karasa bani labari, shine ta saka ni a rami ta qi fitar da ni, kuma idan ban ji amsar nan ba wallahi daina bacci zanyi sabo da tunani." Aliyu ya ji maganar hana bacci, sai ya danna mukulli ya datse da sauri. Ya ce " Sharifah ni ne fa na riqe ki, dan Allah ki koma ki zauna ki karasa bata labarin nan, ki ceto rayuwar 'yayanki tagwaye " Su dukka suka kwashe da dariya. Manyan ledoji cike da kayan marmari da lemuna na kwalaye hade da tsire da kaji masu yawan gaske ya ajiye a gabansu. Ya ce gashi nan ya kawo musu su yi ta ci. Yana so ya koma ofis amma ya ji dadin ganin Samha ta warware da taimakon Sharifah ya na roqomta da ta zauna har Samira ta dawo." Sharifah ta yarda ta koma ta zauna bayan Aliyu ya fita sai suka hau fada. Sharifah ta harari Samha ta ce " kin sami waje ne shine kike yi mana abinda kika ga dama dan kinga ana lallabaki." Samha ta yi ma ta gwalo ta ce "oho dai mijina ya baki amanata kuma kin karba." Samha ta bude nama jifgi ne guda ta ce Sharifah ta sa hannu su ci. Sharifah ta ce ta koshi amma a daukarwa Bello, ya na gida yana jin yunwa. Gida bi biyu Samha ta raba komai ta ba ta rabi. Samha ta kalli Sharifah ta ce " lalali ki na da zumunci da son 'yan uwa, Bello fa ba yaro ba ne amma kina ta shagwaba shi. Kuma kin ce ko shi bai taba taimakonki da taliya kwaya daya ba a lokacin da baban yara ya qi ciyar da su, amma ke har yanzu kina wahala da shi." Sharifa ta ce "haka ne amma babu komai. Haka zuciyata take bana iya hanawa. Bello ya na da kudi amma nawa yake ci kin ga ai hannun da yake sama ya fi wanda yake karba a wajen Allah.". Samha ta ce "bayan mun dauke ki fatalwa mu na gudunki sai gashi kin koma zama fes 'yar gayu, kin gyara gidanki da jikinki da yaran nan, da suturu masu kyau. Sharifah ta yi dariya ta ce "kaina na yiwa fada na cire damuwa da depression, na fara dawo da rayuwata kamar ta da dan na fuskanci kai za ka fara son kanka kafin wani ya so ka. Na dukufa da gyaran fatata da shan supplements da gyaran jiki da kunshi da turaren wuta. Na fitar da tsofaffin kayanmu na kyauta na siyo mana masu kyau. Na Samo almajirai suka yi sati su na kwashe bola da sharar tsakar gida. Ni da Bello mu ka hada kudi, dan aurensa ya kusa zai zauna a kasa. Shari'a ta kare kuma hankalina ya kwanta mutane masu guduna da masu surutu na lalace ta kare min sai daina murna, Sharifah ta tafi ta dawo." Samhabta ce " ina kika sami kudi?" Sharifah ta yi dariya ta ce "kin manta Ina da Allah?." Samha ta ce " Shine Ya ce mu tashi mu nema Zai taimake mu." Sharifah ta ce "rannan na ce miki zan yi meeting da matar gwamna, na fara samun kananan kwangiloli, ina samun 'yan kudi, wasu manyan ma sai nan gaba dan na samu an hada ni da oga kwata-kwata her excellencymun tattauna ta yi alqawura. Alhamdulullah mu na saka ran samun babban rabo. Har na bawa Bello kudin motata zai kawo min daga America, tunda harkarsa ce. Wannan motar da nake hawa ta sa ce." Samha ta ce " ina gaida ke, ga mace mai kamar maza. Allah Ya kara rufa miki asiri kawata, da mu baki daya." Sharifah ta ce " Amin." Samha ta ce " ba ki bani labarin yadda ake ganin matacce a yi hira da shi ba fa.Ranar da muka je gidanki ma kina magana da Shariqah a zahiri. Zuwa ta yi kenan?" Sharifah ta yi dariya ta ce "an kwashe yara an ki dawowa da su, na je har gidansa na iske basa nan ya boye su. Sai na dawo gida raina a bace na kwanta na yi bacci, shine na ga Shariqah a mafarki cike da damuwa. Motsin shigiwarku ne na farka shine ku ka ji ina yi ma ta wannan maganar, a mafarki na ganta na ba ta amsa a zahiri." Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce " kenan duka labarin da kika bani kika ce tana ta binki da wanda kika ce ta gyara kwanciya da maganar waya da ku ka yi, da kuma ganinki da ita na farko a bakin rijiya da magruba dukka a mafarki ne kenan?" Sharifah ta gyada kai ta ce " tabbas a mafarki nake ganin Shariqah kuma muke magana, har nake gane danuwarta " Samha ta d'ala ma ta duka a cinya ta ce " shine ki ke ta wahalar da ni da kwakwalwata? Na dauka a fili ma kike ganinta." Sharifah ta yi dariya ta ce " na yi miki haka ne dan na ga kin yarda akwai fatalwa a duniya ni kuma na san baa mutuwa a dawo " Samira ce ta shigo yayin da Sharifah ta miqe ta dauki babbar ledar, ta yi musu sallama ta tafi. Ba dan Samha ta na so ta tafi ta bar ta ba. Dan hirar ba ta ishe ta ba. Sharifah na isa gida ta ana kiran magrib, ta bawa Bello abinda ta kawo masa ta shiga ta yi sallah.Ta na idarwa, wayarta ta gani tana ta haske da alama sako ya shigo. Sako Samha ta rubuta ma ta kamar haka:
Chapter 22 · 0% Book details