Sashe 2
Hira Da Matattu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*** *** ***
Sharifah ta ci gaba da cewa "Ko Shariqah tayi yunkurin fita daga gidan idan abin yayi ma ta yawa, mijin yana tsoratar da ita da cewa idan ta fita ma ina za ta je? Tunda bata da sauran gata iyayenta gaba daya sun rasu, danginta babu hadin kai, babu mai kula da ita. Kuma idan zata fita bata isa ta tafi da yaransa ba har da na goye, duk kotun da zasu je sai ya kwace su.
Wannan rashin fahimtar ita take saka mata da yawa ci gaba da zama a ukuba a gidan mijin da yake gallaza musu har su rasa rayuwarsu.
Ta kai ta kawo gidanta da suturarta da ta yaranta babu tsari gaba daya ba irin rayuwar da ta taso ba ce, ta fada wata rayuwar da ba ajinta ba ne, ba ta saba gani ba.
Shariqah kyakykywar mace ta koma abar tausayi, baqiqirin ta rame babu maganar gayu ma.
Aure bautar Allah babu wanda ya damu da ita a dangi, wasu lokutan ne ma idan na ganta na kan hau fada ina cewa akwai abinda take boyewa zan sami mijin in yi masa magana. Sai ta hana dan ya dora su akan kishiyarki na jin haushi dan na yi miki abu kaza dan haka ko marinsu yayi kokari suke su fito su na yaqe su na dariya kada kishiya ta gane an yi fada.
Ya same su ya dinga cin karansa babu babbaka babu wanda yake yi masa magana. Bayan rashin wadatasu da kudi ga tsananin kulle, su ba zasu fita ba kuma baya so a zo.
Takai ta kawo yana korar baqinsu, Idan bakuwa zata kwana sai dai a boye takalmana ta. Kishiyar na lallabawa ta fada masa akwai bakuwa a gidan Shariqah. Sai da tsakar dare misalin karfe goma sha biyu sai yayi sumame ya shiga ya ritsa su...."
*** *** ***
Sharifah ta yi shiru ta kasa ci gaba da magana saboda tsantsar radadin da take ji a cikin zuciyarta tamkar fami labarin yake yi ma ta, akan katon gyambon da yake fafare a cikin zuciyarta."
Samha ta dafa kafadarta ta girgiza ta, ta ce "ki zubo da hawayen zai sa ki ji sanyi. Saboda Idanuwanki sun yi jajawur, zuciyarki ta na bugawa da sauri."
Sharifah ta girgiza kai ta ce "haba Samha tun yaushe na wuce babin yin kuka akan bil'adama. Na yi rantsuwa da Ubangijin da Ya busa min numfashi ba zan sake yin kuka ba, sai dai in kai su kara wajen Allah wanda Shine gatana kuma gatan Shariqah, in roqe Shi ya nuna min hanyar da zan bulle wajen daukar mataki da fansa.
Na shiga bala'an da ya fi karfin kuka, mutane sun ba ni mamaki kuma sun ci amanata wanda a baya ban taba sanin haka mutum yake ba sai yanzu."
Samha ta fara tausayawa Sharifah tun bata gama jin labarinta ba. Ta tabbata Sharifah ta shiga bala'in da a dole ma kamanninta suka canja, ta rame ta yi baqiqirin tayi kuraje.
Sharifah ta ci gaba da cewa "mijin Shariqah ya binciko bakuwar Shariqah, ya hada su su dukka ya ci musu mutunci. Shariqah na kuka bakuwar tana kuka ya ce ya yi rantsuwa ba zata kwana a gidansa ba. A cikin daren ya kore ta daga gidan, kuma 'yar uwarmu ce daga wani gari me nisa ta zo Kano yin sari. Ba ta san yadda zata bi ta je unguwar wasu 'yan uwan na mu ba. Yarinya budurwa ya kora a cikin dare dan qarfe goma sha biyu ta gota.
Akwai karamar kanwar mu wacce muke uba daya mai suna Dinar, watarana ta zo hutu daga makaranta kwana itama aka ce sai dai a boye ta, har ta gama yin kwanakin da zata yi ba zai san tana ciki ba dan idan ya sani zai iya korar ta itama.
Ba ta san shi ba sai dai ta dinga leqensa ta windo, tunda bata nan aka yi aurensu kuma bata zuwa gidan.
Yaran Shariqah basu san danginta ba saboda baa kai su ziyara, toh uwar ma bata je ba balle yaranta. Dan haka basu san kowa ba sai wadanda suke iya daurewa da wulakancinsa su je gidanta.
Asibiti ne kadai ya yarda ta je shima sai ya hada da tsine-tsine idan ta kuskure ta biya wani gidan. Wato ya san ta tara barka da gaishe-gaishen mutuwa bila adadin dan bakar mugunta shine baya so ta je ta sauke nauyi.
Tunda ya fatattaki kawayenta da 'yan uwa ai zai fi samun damar da zai ci karansa babu babba akanta wannan ce manufarsa.
Ta koma baiwarsa ba matarsa ba, ko generator zaa kunna sai idan yana gidan idan zai fita sai ya kashe, sai ya dawo zai kunna. Idan yayi tafiya kuwa idan zai yi wata guda ke matar gida ba ki isa ki kunna ba, ko da kina da kudin siyan man fetur.
Daman ita uwar gidan 'yar wahala ce bata fito daga gidan dadi ba, ita Shariqah ce duk bata saba da wannan qangin ba. Akwai ranar da ta zuba mai a inji ta kunna. Ta kashe lafiya kalau amma dan annamimanci sai uwar gidan ta aiko danta ya yanke igiyar saboda idan ya dawo ya gan shi a lalace sai ace Shariqah ce ta kunna. Haka kuwa aka yi, ya zo ya tambaya aka gada masa Shariqah ce ta kunna, ya ci ma ta mutunci tas.
Sunan kishiyar Talatuwa ita da 'yayanta suka dinga hada mata tughu kala-kala, a gaban Hamidah ake yin wasu abubuwan sai Shariqah ta ce kada Hamidah ta fada min .
Abin ya kai har qawayenta da suka yi makaranta tare suka ga halin da take ciki ya kazanta. Hatta kujerunta na falo sun lalace idan baqo ya zauna akai sai ya zurmuka ciki sai an zakulo shi. Su ka hada meeting cewa anya kuwa na san halin da Shariqah take ciki kuwa? Amma aka yi shiru aka zuba masa ido? Su ka yi niyyar su zo su same ni. Daga baya me suka gani dai suka fasa zuwa dan su na ganin zaa ce sun shiga abinda da ba ruwansu tunda tana da dangi babu wanda ya taba yi masa magana, su yaya zaa yi su tsoma bakinsu?
Wataran ledar pure water da za ta siya su sha ta gagare ta, bata da shi komai bai wadace taba.
Idan ma asiri ya yi ya rufe mana baki toh asirinsa ya ci dan babu wanda ya iya yi masa magana.
Ta yi hakurin jiran kudin hayar gidanta na gado dan ta gyara kujerunta amma da kudin suka zo sai ya karbe. Ya ce shi zai samo mai gyaran. Ta san halinsa ba zai taba bari maza su shigo su kwashi kujerun ba, har gara ta lallabashi shi din ya gyara sai ta bashi kudin.
Mutumin nan ya karbe dukka kuma ya qi kawo masu gyaran. Mafarin da ta kamu da ciwon zuciya kenan."
[2/28, 5:50 PM] Jamila Umar Tanko: 2
Ban san ma ta je asibiti an ce tana da ciwon zuciya ba, sai daga baya take fada min a waya. Dan a lokacin ba na zama a Kano, ina zama a Rivers ni da mijina.
A lokacin Hamidah ta dawo wajena tunda babu inda za ta zauna kasancewar Mamarmu ta rasu.
Na ji hankalina ya tashi matuqa na shiga damuwa ba 'yar kadan ba gami da tunanin me ya jawo ma ta kamuwa da ciwon zuciya da kananan shekarunta? Amma ban yi mamaki ba domin kowa ya dube ta ya san bata jin dadin gidan mijin..Sai a lokacin ne Hamidah ta ke fada min wasu daga cikin matsalolin da Shariqah take ciki. Da irin cin kashin da mijin da kishiya da 'yayan miji ke yi ma ta. Su yi ma ta rashin kunya kuma su daki 'ya'yanta."
Sharifah ta juya ta dubi Hamidah wacce ke sharbar kuka ta ce " ki tashi ki shiga daki tunda ke zuciyarki ba ta iya jurewa idan ana labarin Shariqah."
Hamidah ta ja kannenta suka shiga daki, masu wayon dai jikinsu ya yi sanyi sun ji an ambaci mahaifiyarsu, yayin da kananan suke wasansu basu kawo a ka ba ma. Allah sarki, Allah ba Ya barin wani dan wani ya ji dadi.