Sashe 8
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sanyata tsirar fushi da kowa cikin gidan,gefe daya kuma ta sake fakewa da wannan ta aske zuwa islamiyya. Hatta bibi batasan bata zuwa din ba,tanja kawai tasan da hakan,ita dinma kuma bata gayawa kowa ba,saidai tanata qoqarin lallabata da hikima da dabara akan batun zuwan. Cikin kafiya da taurin kanta tayi kunnen uwar shegu da tanja din,duk da hakan tanjan bata fasa hilatarta ba. Kwanaki uku kenan ya karanci kowanne yaro na fita islamiyya amma banda ita. Tun a kwanan farko yaso yiwa tufkar hanci,amma sai ya fasa ya zuba idanu yaga iya gudun ruwanta. A iya nata hasashen da gajeren tunanin tana tunanin kamar ya fita sabgarta ne,hakan ya sanya baya gane duk wani motsi nata kenan. *_L A H A D I_* Kimanin qarfe uku na yammacin ranar lahadin,ranar da kowanne yaro na gidan ke tafiya tahfeez,tun sha biyun rana sai qarfe biyar da rabi na yammaci suke dawowa cikin gidan. Dai dai lokacin da sultana ke cikin dakinta,tayi game yau din har ta godewa Allah cikin wata wayarta da uncle inoussa ya taba bata gift na birthday dinta. Shekara guda kenan wayar na ajjiye bata taba amfani da ita ba,sai a yanzu da maina ya talautata ya kwashe mata dukka abokan debe kewarta. Qishirwa ce ta dameta,ta bude fridge dinta babu ruwa,madararta ma sauran kadan ta qare. A kwanakin ta sha madarar sosai zaman da takeyi a dakin na awanni har batasan adadin guda nawa ta sha ba. Maida murfin fridge din tayi ta rufe,ta sauke lausasan siraran yatsunta qasa ta miqe tana daure gashinta dake da tarin yawa tsaho da santsi,baqi sidik da shi na asalin buzaye. Cikin takatsantsan take takowa zuwa falon don kada suyi kacibus da bibi,taji dadi sosai data fuskanci babu kowa cikin falon,wannan ya sanya kanta tsaye taci gaba da takawa zuwa ga babban freezer dake girke a wata kusurwa ta musamman dake cikin falon. Cikin nutsuwa jerin gwanon motocin ke kutso kai cikin tafkekiyar harabar farko ta gidan,wadda a nan aka tanadi wani tsararren parking lot da aka gina shi bisa tsari da kuma dacewa. Lafiyayyun motoci ne da suke lashe manyan maqudan kudaden da kai zaiyi ciwo wajen lissafin yawansu. Kowacce mota kuma mallakin hamshaqin attajirin dan kasuwa ne wato MUHAMAT MUHAMMAT MAYAK'I. Dan kasuwar da sunansa yayi wani irin fice yayi tambari ya kuma shahara cikin qasar NIJER dama nigeria din gaba daya. A nutse suka gama tsaiwa,mota ta qarshe a cikinsu seat din gaba suka bude. Wani farin matashi me tsaho da kuma kauri ya fito ya dawo set din baya ya bude murfin motar. "Bismillahir rahmanir raheem" shine abinda mutumin ya fada yana sako dogayen qafafunsa yana fita a motar. Tsayayyen ingarman ba'abzine fari sol sol dashi,giant ma'abocin tsaho da kuma qiba wadda tsahon ya tafi da ita,wannan dalilin ya sanya kai tsaye zaka iya kiranta da murjewar jiki. A duba na farko kawai zaka yi masa kasan cewa yana cikin jerin samarin da suka zuba kyau da kuma qasaita a zamaninsa. Dai dai lokacin maina ya qaraso gurin. Qarasawarsu kusa da junan ta haifar da wani kyakkyawan kallo na kyawawan halittu guda biyu masu dan shigen kamanni da juna. Maina din ruwa biyu ne,wani lokaci kamanninsa sukan juye zuwa na ABA,wani lokaci kuma sai kaga kamar kaga AMA. Isowar tasa ta fidda murmushi saman fuskar mutumin,bai iya jurewa ba ya miqawa maina din hannu "Likita bokan turai mainassara" siririn miskilin murmushi ya walqa saman fuskarsa,cikin matuqar girmamawa ya furtawa aba din kalmomin maraba da shiryayyu kuma taqaitattun kalmominsa,sannan ya matsa gaba kadan yana karbar briefcase din aba din daga hannun daya daga cikin yaransa. "Ka shaidawa bibi isowata" aba ya fada don yasan abinda maina din ke son fara yi kenan. Kansa tsaye ya tunkari sashen bibi din yana takawa cikin nutsuwar nan tasa data girmewa shekarunsa. Yana bude qofar tana sakin gorar ruwan hannunta,hantar cikinta tayi wani mugun kadawa lokacin da idanunsu suka gauraya waje daya,tsoro ya bayyana sosai cikin idanunta,yau kam tasan ta kade,batasan kuma me qwatarta ba bayan ubangijinta. Shanyayyun idanunsa ya zube mata yana fara hukuntata da kallonnan nasa da a baya su kadai suna iya fahimtar da ita umarninsa ko haninsa. Ya raineta da irin wannan sigar da ta sanya basai ya furta komai ba take iya gane me din yake nufi. Duk taurin kanta da dakiyarta a yau jikinta ya kasa shanye wannan tsoron daya kwanta saman zuciyarta. Dukka jikinta yadan soma rawa,ya ajjiye briefcase din aba ya goye hannayensa a qirjinsa ba tare da ya dauke idanunsa a kanta ba ya jefa mata tambayar "Ina islamiyya?,me kikeyi a gida?" Kwata kwata dukka wata amsa ta dauke a bakinta,musamman sanda idanunta suka hangi bibi tsaye daga bayansa baki sake tana mamakin ganin sultana din itama a gida "Ina islamiyya nace miki!" Ya sake fada cikin tsawa,tsawar tasa data kusa ruguza ragowar nutsuwarta. Cikin harshensa daya gauraye da hausa faransanci da kuma yaren buzanci yayi sallama a falon,sallamar tasa da tayi dai dai da saukar rahama da wani irin farinciki a zuciyar sultana. Dayan madogarartata ya dawo,bango abun jinginarta,wanda a yanzu tana da yaqinin shine ya maye gurbin matsayin yaa maina din a ranta da zuciyarta,ta tabbatar kuma a yau ta kubuta daga dukkan wani hukunci da muguntar da maina ya tanadi yi mata. Bata qara koda second biyu ba ta qarasa gareshi da hanzarinta. Kaman wadancan shekarun ta tarbeshi,saidai a yanzun ita kanta taji kunyar fadawa jikinsa sai hannunsa data kama,qwayar idanunta dake da wani irin maiqo koda babu hawaye a cikinsu sun sake sheqi saboda qwallar data tara a cikinsu. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 08 Dukka kafadunta ya dafa yana kallon fuskarta dake tuna masa abubuwa masu tarin yawa da suka shude "Meye haka?" "Yaaa maina ne" ta fada tana qarasa tsinkewa da kuka kamar abinda take jira kenan dama. Tsaf aba ya dinke fuskarsa yana dubansa. Mamaki yana ratsashi shi kansa,dama akwai wani lokaci da har wani zaiji rigima tsakanin maina da sultana?,alaqarsu data zarce ta mahaifi da d'iyarsa?. Kallon da yayi masa ya tabbatar kallo ne na tuhuma,sai ya jaye dubansa daga b'arayin da aba din yake "Ya kwashemin Jeux(games)dina,tablette(tab) harda nounours(teddies) dina gaba daya aba" ta fada hawaye na tsargo mata,da alama sosai da gaske tayi missing teddies din nata. "assez(ya isa),zauna maza" aba ya fada yana jan hannunta zuwa saman daya daga cikin kujerun falon. Dukkansu suka zauna,saidai shi maina din yana tsaye harde da hannunsa. A nutse aba ya daga kai ya kalleshi "asseyez-vous(zauna)" gaba kadan ya matso ya zauna daura da bibi "Me yasa maina?" Aba ya jefa masa tambayar yana dubansa "Batason karatu aba,bata iya komai cikin karatunta ba sai tarin shirme,batason makaranta" "Me yasa sultana?" Aba ya maida duba da tambayarsa a kanta "Ina zuwa abba Allah,kullum ma,kuma ko yau naje ka tambayi su najma" . Idonsa ya qanqance yana jin zafi har tsakiyar qirjinsa. A duk sanda tayi qarya sai yaji kamar ya tsinko zuciyarsa,ya raineta saman qin qarya da fadar gaskiya komai dacinta kamar yadda tasa dabi'ar take,amma dare daya ta sauya tamkar wahainiya. "to amma islamiyya fa?" Aba ya tambayi sultanan yana kallonta. Shuru tayi kamar yadda falon ya dauki shuru kowa yana jiran amsarta,sai mutsu mutsu data fara da hannayenta da qafafunta tabbacin rashin gaskiya kenan. Haka aba ya gaji da jiran amsarta ya zame hannunsa yana gyara zamansa sosai "Kina jina sultana?" Kai ta gyada a sanyaye,amma zuciyarta wani zafin haushin ya maina take mata "Karatu shine mutum kinji?,dukkanmu nan da kike ganin gajiyarsa muke ci kuma darajarsa muke ci,Aliyyu ba matsa miki yayi ba,yana sone yaga kinyi karatu sosai kamar yadda yake shine burin nafissa,Allah baiyi zatayi karatu me zurfi ba ya dauki abarsa" ya qarasa fada alamun suna nuna har yau furta sunan nafisa a bakunansu yana tuna musu da dacin rasata da sukayi "Zanyi aba" ta fada a sanyaye da kuma zummar katse fadan da aba yake mata a gaban ya maina din "Allah yayi miki albarka,kije ki gayawa tanja ta rubuta abinda dukka kikeso wanda baki dashi" murmushi ne ya qwacewa sassanyar fuskarta dake lullube da wani irin kyau dake garwaye da sauran quruciya "Aba,madarata ya kusa qarewa" "Carton nawa ya rage?,tanja ta rubuta ki kawomin a qaro miki" . Wani wawan tsalle ta buga tana sake riqe hannun aba da kyau,kai kace duka duka shekarunta basu haura uku ba rci aba" sai kuma ta saki hannun nasa tana zarcewa ciki da sauri sauri. A duniya tana iya jurewa daina shan komai amma banda madararta wadda ta zame mata kamar jini da hanta,hakan kuma baya rasa nasaba da cewa madarar itace ta zame mata tamkar uwar raino a lokacin da ta rasa dumi da gardin nonon uwa da kowanne yaro ke mararin samu a harshe da cikinsa. "Aliyyu" aba yayi kiran maina wanda ke zaune cikin amintacciyar nutsuwarsa kansa a qas. A zahiri yana latsa wayarsa ne amma can cikin zuciyarsa cike take da wata irin fargaba. Yayi tsammanin aba din zai zama mutum na farko da zaiyiwa sultana fada kashedi da kuma jan kunne da kakkausar murya,amma kuma sai yaga akasin hakan,bayan yayi mata fadan kuma ya buge da wanke laifinsa ta hanyar bata tukuicin madara,wai shin a haka sukaci gaba da rainonta dama bayan ya gusa daga gidan?. "Ka maida mata kayanta maina koda ba yau bane,kayi haquri da wautarta,duka canje canjen da kake gani na wani dan lokaci ne,tana girma gaba kadan zata qara hankali ta watsar da komai" "Sai yaushe kenan aba?shekara ta sha daya cikin ta sha biyu sai yaushe hankalin da girman duka zasu zo?" Ya fadi can qasan ransa,amma a fili sai kawai ya gyada kai. Daga aba har bibi babu wanda baisan halin maina din ba,farin sani suka yiwa halaye da dabi'arsa tun gidan babu wasu yaran bayan shi da abokan haihuwarsa da ya bawa 'yan shekaru kadan "Qarasamin da briefcase dina ciki,ka gayawa mammanka na iso yanxu xan qaraso" aba din ya fada. Tsam ya miqe yasa daya hannun nasa da babu komai a ciki ya dauki jakar. A nutse ya fara tattakawa yana barin qawataccen falon bibi din zuciyarsa a quntace. Duk yadda yaso ya zabge bacin da ranshi da zuciyarsa tayi amma hakan ya gagara. Yayi zaune a falon ama yana games bisa wayarsa,duk da