← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read

ko tuna cewa laifi zata aikata dingimeme ba. Tun kafin lokacin karatunshi da ita ya cika ya kammala komai ya sallami su najma da yakewa lesson kaman yadda ya saba duk sanda yake nan,musamman subjects din da yafi qwarewa akai su kuma suke basu wahala. Tun yana duba lokaci har ya sauke qafafunsa qasa yana jawo wayarsa. Momma ya kira matar oncle bashar yace ta turo saddi yayi masa kiran sultana. Minti uku kacal saddi din ya nemi izinin shigowa sashen nasa ta hanyar yin knocking "Entrez(shigo) ya fada yana gyara zamanshi. A nutsen ya shigo yana duban maina. "yaa maina....bata nan" idanunsa akan fuskarsa saddi "Bata nan?,da darennan a lokacin karatu?,ita da wa suka fita bayan time ne na karatu?" Kai ya girgiza "Ba'a sani ba,bibi dinma batasan bata nan ba" idanu ya qanqance yana jin zancen banbarakwai "comment a se fait?(garin yaya ya faru?)" "je ne sais pas(ban sani ba)" ya fada a ladabce. Wani iri yaji maganar tayi masa,kaman yaya za'a ce ba'a ga sultanar ba?,kuma ba'a san ina take ba?,duk girma da fadin gidan da yawan security din dake cikin gidan?,idan bata nan ina taje da daren nan?,lokacin da kowa ke cikin gidan. "Jeka" ya fada yana miqewa daga zaman da yayi,ya lalubi wayarsa ya saka a aljihunsa ya zura baqaqen slippers dinsa yana ficewa a sashen nasa. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* Page 16
Chapter 15 · 0% Book details