Sashe 2
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nufin sassauci da kulawar da yake nuna mata sun fara gaya mata cewa zata iyayin komai ba komai bane?!. Bata ankara ba sai ji tayi ya fusgo qafafunta,sai gata tana Shirin direwa daga saman gadon zuwa qasa,abinda yayi matuqar razana ta ta saki wata razananniyar qara. Qarar data sanya bibi sakin matajin da take taje doguwar sumarta da har yanzu ke da tsananin tsaho,duk da tarin shekaru ba abinda ya canza daga gareta sai furfurar data jirkita ainihin baqinta. Kai tsaye dakin ta banka gabanta yana wani irin faduwa. Tun sanda ya shiga dakin taji zuciyarta bata kwanta Mata da hakan ba,to amma mu'amalarsa da sultana din ya sanya taji ta dan nutsu ta wani sashen kuma. Dab da bakin gadon yayi mata burki,ya qara taku biyu zuwa gabanta hadi da jawo stool ya zauna yana dubanta da rinannun idanunsa "Bariki kikeso ki fara?" Ya jefa mata tambayar fuskarsa na wani irin hucin da shi kansa yasan fushin dake cikin zuciya da gangar jikinsa ya banbanta da na ko yaushe,jinin NAFEESA CE FA?,shine abinda ke amsa kuwwa cikin kwanyarsa. Cikin tauri da dakewar zuciya tace "Ni me nayi?" Haushi da takaici suka sake turnuqeshi,ido cikin ido sukayi da ita,amma yanzun shi take tambayar wai me tayi?. Tana masa magana kuma cikin confidence da soyewar zuciya "Ki gayamin me ya kaiki nan wajen?" "Ni fa ba abinda naje,ba a kwance ka samenib......." Bai barta ta qarasa ba ya sauke mata mari saman fuskarta,abinda yayi matuqar razanata,ya kuma razana bibi dake shigowa ta fado dakin da mugun sauri kamar zata kifa. Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin......... *ZAFAFA BIYAR FAMILY* *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba* *_ZAFAFA BIYAR_* *_SABUWAR SHEKARA_* *_SABON TSARI_* *_SABBIN LABARAI_* *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_* *_CAKWAKIYA_* *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_* *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_* *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_* *_KWANTAR DA ZUCIYA_* *_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_* *QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA* *KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo) *TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul) *AMEENATU* (Mamuhghee) *GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma) *_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_* *_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_* *TSARIN SHINE KAMAR HAKA* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *THANKS FOR CHOOSING US* *_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* PAGE 02 Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin "Ashsha,ashsha,haba maina,me ya hadaku da zafi har haka?kai da nace maka baka ta lafiya?" Ta qarashe maganar idanunta saman fuskar sulatana da tayi jazur. Har cikin tsakiyar ranta takeji kamar ana fusgarta,saboda yadda zallar madarar zafin marin ya ratsata yadda ya kamata. Kai tsaye zata iya cewa ta manta da wani abu mai suna mari bare yadda zafi da radadinsa yake,sai gashi yau ya zama mutum na farko da ya tuna mata da wannan "Ta gaya miki yaushe tabar dakin nan ta tafi gurin raye raye a tsakiyar maza ba tare da saninki ba" abinda ya furta kenan yana nunata da yatsa,ya sauke hannun ya juya yana fita a dakin cikin tsananin qunar rai. Fuskar sulatana din bibi ke shafawa tana qoqarin rarrashinta,saidai ko a jikinta wai an mintsini kakkausa,kuka take sakewa kamar wadda aka yanki naman jikinta "Wallahi radadi fuskata takeyi bibi,Allah bazan yarda ba,bazan yafe masa ba" sosai maganar ta daki zuciyar bibi din,tabi sultana da kallo wadda ruwan hawaye ya dade da gama jiqa mata fuska "Sultana,mainanki ne fa?" "Shi din bibi,mugu azzalumi,kawai don naji ana kida na tsaya rawa sai ya biyoni ya mareni?,me nayi masa?" Sosai jikin bibi ta mutu,bata taba tsammanin akwai ranar da zata zo da wani sabani me kama da wannan zai gilma tsakanin maina da sultana ba,sultanar da ko ita ba kasafai yake bari tana yi mata fada ba,bare duk da batasan yaushe ne lokaci na qarshe da aka daketa din ba. Sultana din da bata cin abinci ba tare da maina ba,bata iya bacci ba tare da maina ba,komai ma na rayuwarta maina ne,yau rana tsaka kamar wadanda aka yiwa farraqu suke neman sauya halayya ita da shi gaba daya "Amma dai sultana sau nawa ina jan kunnenki akan zuwa wannan gurin?,saboda gujewa rana irin wannan?,ranar da maina din zai san kina zuwa?" "Wallahi bai isa ya takuramin ba,shi waye ya takura masa?,kawai don yaga ina masa biyayya?,ai ba tsoronsa nakeji ba" ido da baki gaba daya bibi ta bude tana kallon sultana din. Mainan da ya zamewa kowa dodo cikin gidan?,koda a boye basu iya hirarsa bare a zahiri irin haka amma ita take sake masa magana?. "Anya sultana?,me yake cikin kanki?,kina girma kina cin qasa?" "Ki rabu dani tunda goyon bayansa kikeyi kema" ta fada tana ture hannun bibi dake cinyarta,sai kawai ta nufi toilet dinta ta shige ta maida qofar ta kulle,ta zauna a toilet seat taci gaba da rera kukanta kamar wadda sautin yakewa dadi. Baki sake tabar bibi a zaune a wajen,cikin matuqar mutuwar jiki ta dauke kallonta daga bakin qofar toilet din,tasan halin sulatana da tsananin kafiya da kuma taurin kai,duk yadda taso ta fito a yanzun idan ba niyya tayi ba zata bata bakinta ne kawai "Allah ya kyauta,yayi mana maganin wannan sabuwar matsalar kuma" bibi ta fadi ta yunqura tana miqewa. Sai a sannan taga jakar makarantarta dama doguwar rigar uniform da hijabinta a yashe a qasa. Tasa hannu ta kwashesu ta juya tana barin dakin. Tsaye tayi gaban mudubin bandakin nata tana kallon fuskarta,sosai fuskar takeyi mata radadi,tasha ji a bakin su lamira cewa yaa maina din yana da zafin hannu,amma bata taba tantancewa ba sai yau,tunda bai taba kai hannunsa fuskarta ba. Hannu ta sanya ta sake shafar kuncin nata da yayi jajur,abinka da farar fata "Dama haka zafin mari yake?" Ta tambayi kanta da kanta can qasa,saboda iya rayuwarta da kuma wayonta ba zata iya tuna lokacin da aka daketa bama bare a mareta "Allah ya isa na" ta fada qasa qasa wasu sabbin hawayen suna zubo mata. Da baya da baya ta koma,tayi zamanta saman toilet seat tana ci gaba da fitar da sheshsheqar kuka. A iya marin da yayi mata yau kawai sai takejin wani mugun haushinsa irin wanda bata taba ji ba. Yaa maina din,shalelenta itama shalelensa,ba wanda ke tabuwa a wajen dan uwansa,amma yau sai taji ko fuskarsa bata son kalla. Da zazzafan ruwa sosai yayi wanka bayan ya gama dukka uzururrukansa na ranar,da dan wuri yaso shigowa gida saboda yanayin sanyi da ya fara busawa,amma kuma daukan karatun da ya tsaya yi a zawiyya yasa lokacin shigowarsa gidan ya dan ja. Yana shiryawa yana bin tsarin dakin nasa da kallo,yaja tsaki lokacin da ya bude wardrobe dinsa yana bin shirin kayan da kallo. Hannu ya saka ya zaro wata turtle neck sweatshirt me dogon hannu baqa,wadda ta fidda zallar hasken fatarsa da kuma narkakken kyau da yake shimfide a fuskarsa,wanda ke cakude da qyalli da sheqin samartaka. A nutse ya shirya,idanunsa saman agogon dakin nasa ya dauki wayarsa yana shirin ya fita. Kamar jira wayar keyi ta dauki tsuwwa,sai ya dakata ya maida hankalinsa kanta. 'BIBI NA' shine sunan dake yawo saman screen dinsa. Daga wayar yayi yana ci gaba da shirin fitar. Muryar Dijama ce, cikin d'ari d'ari da takatsantsan take gaya masa saqon bibi "Okay" kawai ya fadi a taqaice yana katse kiran. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa "Me ya faru ne bayan tafiya ta?" Ya yiwa kansa da kansa tambayar da shima neman amsarta yakeyi. Gaba daya sauyin halayya da dabi'u yake gani daga yarinyar. Yarinyar da ya bata dukkan wani minti da awa dake cikin rayuwarsa wajen ganin ya raineta rayuwa me kyau,ya bata tarbiyya da tasha banban da ta kowa,ya kuma killaceta fiye da yadda ake killace kowacce diya mace dake jahar maradi,sai gashi tafiyarsa da waiwayo gida da yayi komai ya kwabe ya canza. Iskar ya sake fesarwa,sai ya soma fita a dakin a gaggauce,can qasan ransa cike da tunani tare da son gano ina matsalar take?. Zaune ya sameta cikin parlor din nasu,sanye da sassauqar doguwar riga me gajeran hannu,kantan nan yasha gyara qwarai,hannayenta dake sanye da wasu siraran warwaraye riqe da jarida tana dubawa. Farar ba'abziniya,wadda ke tafe da tsaho da qiba dai dai gwargwado. Tana da wani kyau na musamman wanda shekarunta basu kai ga boye shi ba. Sallamarsa ya sanyata daga kanta ta dubeshi,sai ta sauke qafafunta da suke a harde a dazun ta gyara zamanta sosai tana amsa masa sallamar. A gefe ta ajjiye jaridar tana dubansa har ya qaraso. Cikin girmamawa ya zame ya tsugunna a gabanta "Barka da wuni" "Barkanka,tun dazu nake maka aike ka fito kaci abinci amma hakan ya gagara" agogo ya sake kalla,tabbas yana toilet yaji shigowar almu har sau biyu "Wanke nakeyi,ina kammala shiryawa kuma na fito" "Saika qarasa kaci abincin ko?" Ta fada tana miqa hannunta da nufin daukar jaridarta. "Zanje sashen bibi,yanzu zan dawo sai na zauna gaba daya" tsaiwa tayi da abinda takeyi,ta kalleshi yanayin fuskarta yana canzawa "Me kuma zakayi a sashen bibi bayan na tabbatar tun safe bakaci komai ba?" Cikin lanqwasa murya da salon lallashi irin wanda ita daya yakewa duk duniya yace "Yanzun zan dawo AMA,zanyi magana ne da sultana" "Sultana?......kai dawo ka zauna" ama din ta fada tana sake sauke qafafunta qasa. Yadda ta buqata haka ya koma ya zauna sosai yana lanqwashe qafafunsa,zama tayi sosai ta zuba masa idanu tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta,ME YASA TAKETA GUDU AMMA KAMAR K'ADDARA NA BIBIYE DA ITA?. "Wai sai yaushe zaka san cewa ba ahalin su NAFEESA na haifawa kai ba?,sai yaushe zaka daina bautawa abinda ya shafi nafeesa da rayuwarta gaba daya?" Maganar ta sauka a wani muhalli