← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 30

Sashe 7

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

akan dukka issue din da ya shafi sultana ba "Lafiyarka Aliyyu?" Bibi ta tambayeshi tana kiransa da ainihin sunansa "Anya zamu iya sauke amanar sultana dake wuyanmu?" Yayi mata gajeriyar tambayar me dauke da tarin abubuwa masu yawa. Da idanu ta tsirashi tanason warware maganar tasa "Kamar yaya maina?" Ta tambayeshi tana sauqaqewa kanta dogon nazarin da kwanyarta ta tafi yi "Komai na sultana ba daidai yake tafiya ba bibi,komai ciki harda karatunta" ya fada yana miqa mata daya daga cikin litattafanta da yafi bata mata rai. Ta zauna shafi bayan shafi ta rubuceshi da waqar wani shahararren mawaqi a nan nijer dake waqar hip-hop da harshen faransanci. Bin littafin tayi da kallo don ba karatun boko tayi ba,saidai tana da ilimin muhammadiyya sosai "Tabbas sultana batason makaranta bata kuma qaunar karatu nasan wannan,amma ina dukka bakin qoqarina wajen ganin tayi karatun tunda nasan wannan shine burinku daga kai har nafessa" shuru yayi na wasu daqiqu,iya qoqarin tarbiyya da saita yara gidansu ya samu wannan shaidar,amma jarrabawar iyayensu yana kyautata zaton akan sultana take. Bai sake cewa komai ba ya miqe ya fara tattara dukka wasu teddies da games nata dake dakin. Sai daya rabata da dukkan wasu kayan wasa ya kammalesu guri guda sannan ya fita a dakin. Nannauyar ajiyar zuciya bibi ta sauke zuciyarta tana karyewa. Batasan me yasa duk sanda ta yunqura da nufin yiwa sultana hukunci me tsauri take kasawa ba,tana jin yarinyar har tsakiyar zuciyarta da wani irin zallar tausayi da soyayyar da batajin cikin jikokinta akwai wadda ya rabauta da kwatankwacinta. Kamar yadda take mutum ta qarshe dake fitowa ta shiga motar makaranta,hakanan ita ke kasancewa mutum ta farko dake fara fita a motar duk sanda aka iso gida. Tamkar motar tana cizonta haka take bude motar a gaggauce ta fice tana waqe waqenta,bata damu da qafar waye ta taka ko ta buge ba,saboda duk wanda yayi qorafi ko wani abu makamancin haka bakinta baya mutuwa,koda kuwa ita ke da laifi ba zatayi shiru ba sai inda qarfinta ya qare. Bata da wani qarfi ko na sisin kwabo,amma dukka qarfinta da qoqarinta ya tuqe ne a zuciyarta. Tana da wani irin taurin kai da kafiya wadda da qyar ake iya tanqwarata ko juyata. Yau dinma itace ta farko data diro daga motar,ta kuma wuce cikin gidan sassan bibin hankalinta kwance tana janye da jakarta. Tun daga falo kamar ko yaushe ta fara jefar da jakarta da qanqanin qanqanin hijab din da suke saqalawa. Cireshin kuma ya bawa lallausar sumarta da sam bata kitsuwa damar warewa. Takalmi zuwa socks dinta ta salube suma ta wurgar,ta zare rigarta da wandon duka,ba abinda ya rage mata sai vest dinta data kawo har cinya da kuma wandonta da ya tsaya iya gwiwa. Fridge ta bude ta dauki madararta me sanyi ta fasa ta fara sha sannan ta wuce dakinta bayan ta kalli agogo ta kuma qiyasce mintunan da suka rage da za'a dameta da batun tafiya islamiyya. Islamiyyar da ayau ta haqqaqe ko dambun namanta za'a yi yau din ba zataje ba,don haddarta ta jiya da shekaran jiya duka babu wadda tayi. Ba abinda ta tsana irin a bata haddar,a duk sanda malamin ya shigo ita kuma nata karsashin ya qare,ta gwammace ta nade cikin hijabi ta hau baccin qarya,ciwon kai ciwon ciki duka nata ne,tun malamin na tunanin hakanne da gaske har ya fahimci akwai lauje cikin nadi,duk wata hikima da hukunci ba wanda baiyi mata ba amma sam ba abinda ta sauya. Batason karatun shi ya sanya ta sakawa ranta bata ganewa wannan yasa bata ganewar. Cak ta tsaya sanda ta tura qofar dakin nata tana bin dakin nata da kallo. Taku biyu baya tayi tana mutstsuke fararen idanunta tana sake kallon kowacce kusurwa ta dakin da kyau. Sakin labulen tayi sannan ta bude dukka siririyar muryarta ta soma kwarara sunan "Tanja!......tanja!......tanja!" Tamkar wadda sukayi kacibus da mutuwa. Kusan lokaci daya suka saki dukkan abinda sukeyi din suka durfafi dakin da wani mugun sassarfa. Daga tanjan da aka kira har bibi da ba'a ambaci sunanta ba a rude suke matuqa da kiran tanja da sultana keyi babu qaqqautawa. Zuciyarsa a tsinke da tunanin mugun abu ya sameta. Birki suka ja dukkansu suna kallonta,ta yaye zanin gadonta gaba daya ta kuma wargaza kayan closet dinta gaba daya "Ina nini na tanja?,ina games dina?,waye ya shigo ya sacemin kayana?" Ta fada idanunta na rau rau da hawaye,zallar tashin hankali ya bayyana saman fuskarta "Yanzu fisabilillahi saboda wannan ya sanya kika dinga qwalawa tanja kira?,dukka falukan gidan nan sai da suka amsa?" Bibi ta fada tana tsuke idonta akan fuskar sultana,tana ganin wani tashin hankali da muraran kan fuskarta,kai kace an sace mata wasu abubuwa masu matuqar muhimmanci ne ga rayuwarta. A wajentan masu matuqar muhimmanci ne,domin ninin na daya daga cikin abubuwan da tafi so cikin abubuwan data mallaka,hakanan games dinta suna a mazaunin manyan abokai cikin rayuwarta. Duk yadda take da surutu rawar kai da tarin tarkacen qawaye hakan bai hanata qin shiga shirgin kowa tare da ware kanta haka kurum idan taso cikin dakinta. Zata iya kashe awanni ita daya,rungume da nini dinta da kuma games dinta. Kai kawai bibi ta girgiza ta juya tana barin dakin "Waye ya daukemin nini na?" Sultana ta fada muryarta na rawa tana shirin fara sakin kuka. Itakam bibi ma bata waiwayo ba,sai tanja dake qoqarin kintsa dakin ta amsata "Mainasara ne sultana" "Maina?" Ta furta cikin cika da batsewa tana jin masifa fal zuciyarta. Da gaske dai rayuwartata yakeson shigar mata,qarfi da yaji yakeson shiga abinda take ganin bai shefeshi ba tunda tuni ya zare kansa daga sahun mutanen dake qaunarta har zuciyarsu "Wai shin me yayi ruwansa da kayana tanja?" Ta jefawa tanja tambayar cikin kaushi da zallar bacin rai "Karatu mana sultana?,maina yana miki sha'awar karatu ne" "To bazanyi ba,nace bazanyi ba,wani banzan maina bai isa ya takuramin ba bayan shi din ba ubana bane" ta fada cikin tafasar zuciya. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 07 Maganganun sai suka kwancewa tanja kai,koda cikin mafarki tayi mafarkin sulatan zata iya gayawa maina hakan lallai zata daukarwa ranta cewa gundumemiyar qarya ce mawai shaidan ya wassafa mata a mafarki don yayi wasa da tunaninta. Maina da sultanan da suka zama wani kyakkyawan madubi da kowanne uba zai kalla game da diyarsa?,yau itace ke furta masa hakan?. Ko kafin tanja ta sauke tunaninta sultanan ta fice a dakin a gaggauce. A falo taja tunga,don dama bibi take nema kuma ta ganta. Da jiqaqqun idanunta da suka gaza boye hawayen da taketa son shanyewa ta dubi bibi,don duk yadda taso ta shanye bacin ran maina amma ta kasa,saboda zuciyarta ta gaya mata nini dinta da games dinta sun tafi kenan,tafi kowa sanin shi din kaifi daya ne,kuma ya aikatashi zaiyi shi ne gaba gadi,babu kuma sauyi ko canji a hukuncinsa "Bibi ki gaya masa ya dawomin da kayana" ajjiye cup din hannunta bibi tayi,daga tsayen da take ta maida dubanta kanta "Zai dawo miki dasu,amma saifa idan kin maida kai ga karatunki,na tabbatar idan yaga hakan ko bakice ba zai dawo miki da kayanki gaba daya koda kuwa ba'a ce masa ba" "ni kawai ki gaya masa ya dawomin da kayana tunda dai ba shine ya siyamin ba" tayi maganar da alamun kuka yana son balle mata. "Ai sai kije ki karbo da kanki" bibi din ta fada cikin gatse. Bibin na direwa sultana tayi hanyar falon cikin dakiyar zuciya,cikin zuciyar tata tana fadin "Aiba ubana bane,ba kuma mala'ikan mutuwa bane da zanji tsoronsa". Kaman ko yaushe,ma'abocin rashin son hayaniya ne da kebe kansa guri guda a mafi yawancin lokuta. A yanzun ma hakan take. Shi daya ne a farfajiyar gidan,yana sanye da wata lallausar shirt da trouser dukkansu royal blue ne da dan ratsin blue din kadan a jikinsu. Ma'abocin karance karance ne sosai,yana daya daga cikin hobby dinsa. Ko yanzun ma littafin wani shahararren marubuci ne a hannun nasa dan qasar faransa. Idanunta a kansa tun daga nesa ta tsareshi dasu,sannu a hankali take qara kusanci a tsakaninsu. Wani irin kwarjininsa ke dukan zuciyarta yana neman cire mata dukka wani qwarin gwiwa da ta fito da ita,saita ta lumshe zuciyarta na sake bata qwarin gwiwar tunkarar nasa ta kuma zazzage masa dukka bacin ranta da abinda ke cikin zuciyarta. Maimakon ci gaba da samun qwarin gwiwar isa gareshi din,a duk sanda tayi taku daya sai qarfin gwiwarta ya ragu da wani kaso me yawa. S hankali ta tsaya cak kamar wadda aka yiwa burki sanda take dab da isa gareshi,kwarjininsa gaba daya ya gama cikata,tayi imanin tayi kadan ta isa inda yake din duk da confidence din da ta fito da shi a dazu,wannan baqincikin ya sanyata juyawa da sassarfa me hade da gudu tana komawa sassan bibin. Sam baisan da tsaiwarta a wajen ba,don shi din mutum ne da bai fiya mai da hankali da idanu akan abinda bai shafeshi ba,yaji motsi da taku duka lokaci daya,ya daga shanyayyun idanunsa yana bin hanyar da kallo. Baici nasarar ganinta ba,saidai yaga shigewar mutum sashen bibi,sai ya dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi. Da kallo bibi dake zaune cikin lafiyayyun kujerun falon ta bita. Ta sake baki kawai sanda ta zube saman daya daga cikin kujerun tana sakin qarfaffan kuka "Oh.....oh ni maryamu,yau naga abinda ya isheni" "Alla......Allah sai ya dawomin dasu,Allah bibi kiyi masa magana" abinda sultana din ke maimaitawa kenan cikin kuka. Ta tafasa sauke bibi bata sake cewa da ita ba sai maida kanta da tayi ga abinda takeyi,saboda tayi imanin zata bata bakinta ne kawai,don babu abinda zatace da sultana da zai sanyata tayi shuru. Kuka sosai tayi cikin kujerar kamar wadda aka yiwa mutuwa,irin kukan data jima batayishi ba,har ranta bibi kejin kukan amma tayi banza da ita,saboda ita kanta ta tabbatar dauke kayan shine maslaha. Tanja ce ta dinga fama hade da jelar lallashin sultanar amma babu abinda ya canza. Zuwa wani lokaci tayi shuru,shurun da ya tabbatar tayi bacci. Blanket tanja ta dauko tana jan qafafunta ta gyara mata kwanciya,zuwa yanzu sultanar tayi girman da ba zata dauketa ba,ba kamar shekarun baya ba da idan ta gama rigimarta kamar haka tayi bacci tanja din ke daukarta ta kaita dakinta ta kwantar da ita. Wannan abun da ya farun
Chapter 7 · 0% Book details