Sashe 23
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jero masa "Ka gani ko yaya?,baya magana fa,Allah muddin wani abu ya sameshi dasu da wanda ya kawoshi nan din sai ya raina kanshi" "Muje dai Omar " aba ya fadi yana sanyasu a gaba. Aba din yana shiga DPO din ya miqe cikin mamaki "Barka da zuwa yallabai,yau kaine da kanka a office dina?,bismillanku" murmushi kawai aba din yayi,yaja kujerar ya zauna sannan su oncle bashar suka zauna,banda maina dake a tsaye bashi da ko alaman tsaiwa,don bai qaunar dogon zama sam cikin office din mutumin,shi daya yasan me yakeji a zuciyarsa,shi kansa din ma bazai iya tantancewa ba. Bayason kallon fuskar mutumin sam,saboda tana tuna masa da mummunar lafazin da suka jefeshi da shi shida sultana,tana tuna tozarcin da yayi masa irin wanda ba'a taba masa irinsa ba tunda ama ta kawoshi duniya "Kada dai ace wannan yaronka ne?" Dpoya fada yana nuna maina "Eh yarona ne,nazo kawo cigiyarsa kuma muka sameshi a nan" "Subhanallahi" tiryan tiryan ya gaya musu yadda komai ya faru,sannan ya dora da cewa "Yaqi bayani ne yaqi fadin komai,ko kare kansa wallahi yaqi yayi,bansan ba mara laifi bane tunda baiyi yunqurin bawa kansa kariya ba" "Amma yarinyar wace a ina kuma take?" "Bansani ba tunda baiyi bayani ba amma dai ga unguwarsu ga kuma hotonta mun ajjiye report saboda gaba" ya fada yana miqa musu wani file "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,sultana ce,'yaruwarsa ce ai,'ya take a wajensa" oncle bashar ya fadi,yayin da aba da kuma oncle umar suka bushe a wajen suka kasa cewa komai. Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,a nutse aba ya daga kai ya dubeshi "Meye ya hada haka da ita?,a ina ka daukota?" Sai a sannan yadan motsa kadan daga tsaiwar da yayi kamar an dasa itacen bishiya,rayukan 'yan maza ne a dugunzume ainun. Dpo din ya fahimci muddin yana wajen bazaiyi magana ba,su dinma sun fahimci hakan,saboda haka oncle bashar yace "Maganar nan ta gida ce yaaya" "Gaskiya dai" DPO ya fadi. Dukkansu cikin mamaki da juya lamarin suke dukka su ukun,har zuwa sanda DPo da kansa ya rufe case din,ya kuma tattara musu dukkan wani document da ya shafi case din suka fice da shi. Ba wanda suka yiwa bayanin inda suka samoshi,saidai oncle umar daketa banbamin fada kaman zai ari baki,daga qarshe kuma "Zataci qaniyarta sultana wannan karon" har yanxun maina din bai cewa kowa uffan ba,don bayajin bakinsa zai budu har wasu kalamai su iya fita. Jikinsa dukka radadin cizon da sauro ya kwana yana masa a jiya,uwa uba tsabar tsantsami ya sanya yake masa qaiqayi jikin nasa,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka bayan ya watsa kayan jikinsa a dustbin,duk tsadarsu bayajin zai iya sake amfani dasu. Shi daya suka bari a shiyyar tashi,don yace yanason ya kwanta ya huta,ko abinci da ama tayi masa tayi cewa yayi baici ya qoshi. Da gaske bayajin abincin zaibi ta maqoshinsa,da bibi ma ta aiko dashi sawa yayi aka maida mata,ya rufe qofofinsa ya kwanta yana fatar yayi baccin da bai samu yi ba a daren jiya. Bayan ya kwanta din labari ne yasha banban. Duk inda ya runtse idanunsa ya juya ba abinda idanu da kunnuwansa ke jiye masa sai kalmar SATONI YAYI,FYADE ZAIYIMIN. "la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem" ya dinga maimaitawa. Futucin yaqi barin kunnuwansa......Ga tarin mamakin sai yaji wata siririyar qwalla na fito masa ta gefen idonsa guda daya. Hannu ya sanya ya shafosu yana kalla,shi kam iya tsahon wayonsa da girmansa ya mance yaushe ne lokaci na qarshe da ya ga hawaye cikin idanunsa haka. Duk da ya karbi horo na sajoji masu matuqar wahala da azaba,amma basu taba sakashi dar ba bare damuwa har akai ga qwalla,sai gashi yau furucin sultana ya karya zuciyarsa har haka?. Haka ya wuni ya kwana,saida tursasawar ama yaci abinci zuwa dare "Wai ina ka bace?,me sameka da wannan mummunar damuwar take bayyana kan fuskarka?" Ta tsareshi da tambar tana kallon fuskarsa. Har ama din tayi ta gama itama bata samu amsa ba hakanan ta haqura tunda ta samu yaci abincin. Sultana kuwa tunda taji yaa maina ya dawo gida ta koma tamkar kazar da aka jefa da wuqa,wato kenan tasan wa'adin kwanakin rayuwarta a duniya qididdigaggu ne. Dukka saita tsargi kanta,ta rasa dukkan wani sukuni da walwala,ta yiwa kanta iyaka da kuma shamaki iya dakinta kadai. Tayi tsammanin games dinta da su nini zasu debe mata kewa,amma kowanne sai taji baya yi mata dadi,idan ta dauko game din sai taji batayi mata ba saita watsar,idan ta dauko nini din ta rungumeta kaman yadda takeyi a baya sai taji ta isheta itama saita ajjiye ta koma ta kwanta. Haka ta dinga juyi kafin daga bisani aminata da lamira suka leqo suna mata dariya tare da sake gaya mata tabbas ya maina fa ya dawo "To sai me?, mala'ika ne shi?,yayita dawowa,nidai ko banza ai an rama min marina" ta qarashe fada tana murguda baki sannan ta juyar da fuskarta zuwa bango abinta. **_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* Page 23 W A S H E G A R I* Idan ka hango yadda ta takure a quryar bango ta kuma cukuikuye cinyoyin Bibi saika dauka mala'ikan daukan rai ne daura da ita. Idanunta sunyi tsilli tsilli sanda maina ke maimaita yadda komai ya faru da wata iriyar saryayyar murya. Dukkansu suna wajen banda aba da tafiya ta kamashi niamy da sassafen. Idanunshi basu kan kowa saboda suna cike ne da wasu al'amura da shi kansa baisan iyakarsu da nauyinsu ba. A karon farko da yaji yarinyar ta fice masa fit daga kanshi gaba daya. Yana gama kaiwa qarshe shuru ya ratsa dakin,sai bibi dake sallalami tana qoqarin ture sultana daga jikinta "Ashe fitinarki har takai haka sultana?,ki daure dan uwanki kiyi masa mummunan qazafi irin wannan?,sultana?,babanki maina yake fa?,shine yaci kashinki yaci fitsarinki fa sultana?,anya?" Bibi ta furta cikin wani fushi da bata taba kwatantashi ga sultanar ba. Oncle umar kuwa waya ya ciro yayi kanta,saida oncle bashar ya tsaidashi da qyar "Ka banni yau jikinta ya gaya mata,ta dauka duk cikin gidan ba'a iya dukanta ne?" "Kada ku daketa" muryar maina da wani irin sauti ta cika falon. Waiwayawa sukayi suka dubeshi,har ya miqe tsaye ma abinsa "Ba fyade tace zanyi mata ba?,to tabbas ta rubuta ta ajjiye NI MAINA SAI NA YI MATA FYADEN,zatasan me ake nufi da ainihin fyade" "La'ilaha illa anta.......na shiga uku ni kubra" bibi ta fada da mugun qarfi tana zaro dukka manya idanunta waje,muryarta tana rawa "Aliyyu,maina.....me kake fada!,maina!!" Ta qwala kiran sunansa sanda yake dab da ficewa daga falon. Bai dakata ba bare yaji me take cewa ya sanya kansa yana ficewa,ba daga falon ba daga gidanma gaba daya. "Na shiga uku na lalace ni kubra,me yake shirin faruwa da iyalina?" Bibi ta sake fadi cikin rudewa da tashin hankali. "Kinga bibi,kada ki wani dagi hankalinki fa" "Kasan maina ne?,kasan duk furucin da zai furta yana nufin abinda ya fada din,kasan halinsa kaifi daya ne,kasan baya fada ya canza ko?" "Ai bashi ya haifi kansa ba bibi" ama da sai a sannan ta samu fusgo tata nutsuwar ta fadi tana matsawa kusa da bibi din don ta taya su oncle bashar rarrashinta. Duk yadda sukaso kwantarwa da bibi hankali ta qiya,hasalima kuka takeyi "Ina tsoron halin maina na kafiya akan magana da cika magana idan ya fadeta,ina tsoron kada da gaske din ya lalata rayuwar marainiyar Allah" "Ba zata faru ba bibi don Allah ki kwantar da hankalinki" ama ta sake fadi cikin nata tashin hankalin da rudanin. Sun dauki dogon lokaci kafin su samu bibi ta tsagaita kukan,tace amma su nemo mata maina tayi magana dashi. Sam ranar maina din qin zama a gidan yayi,kamar yadda ya kama wayoyinsa duka ya kashe,bai kuma shigo gidan ba sai qarfe sha biyu saura na dare. Yana shiga ama tana sanya qafafunta,tamkar dama tana biye dashi. A mamakance ya waiwayo yana dubanta "Ama,bakiyi bacci ba?" Dubansa take da fuskarta a dinke tsaf "Ta yaya kake tunanin mahaifiyar da d'anta yayi irin wannan mummunan furucin a gabanta zata iya kwanciya ta runtsa?" Tayi masa tambayar da salon da ya sanyaya masa jiki "Zauna" ta bashi umarni kai tsaye. Bai musa ba ya koma a hankali ya zauna yana kallonta "Aliyyu,ina dukka hankalinka da tunaninka suka tafi?,ina iliminka?,kasan illa da munin iqirarin da kayi?,ta yaya zaka dauki wuqa da kanka ka dabawa cikinka?" Ta dakata tana maida numfashi "A gaban kowa kayi iqirari irin wannan?,inda kana da qanwa uwarku daya ubanka daya da ita wani ya fadi haka a kanta zakaji dadi?" Idanunsa ya runtse yana jin ciwon dukka kalaman a karan kansa "Inaso ka janye wannan iqirarin,ka kuma baiwa bibi haquri,don banason ma zancan yakai kunnen mahaifinka,bana so kuma hakan ta sake faruwa ko da wasa" "In sha Allah,kiyi haquri ama" ya fada a tausashe. "Ya wuce,zan turo saddi da abincinka" ta fadi tana fita a dakin. Ya jima zaune a wajen yana juya lafazin nasa,har zuwa sanda saddi ya riskeshi da karagar abincinsa cikin warmers na alfarma masu tsananin kyau kamar yadda yake kusan hakan al'adar ama ce,komai nata me kyau da tsada ne. Ko kusa ko alama bata taba daukar kalmar SAI NA MIKI FYADE da ya maina ya furta din zata zame mata wani abun damuwa ko barazana ba,abinda kawai yafi mata dadi da bai taba lafiyarta ba ya juya kuma yabar gidan. Ga tarin mamakinta sai gashi a sanda dare ya fara yi kalmar tana dawo mata,ta rufe idanunta ta rungume nini da kyau ta kuma nutse a blanket dinta amma sai taji maganar tana dawo mata. A hankali labarai akan fyade suka soma dawo mata cikin kwanya. Labaran da bata taba basu muhimmanci ba cikin rayuwarta,wasu ma ta mantasu sai gasu suna dawo mata daya bayan daya. Sannu a hankali tsoro taji ya fara shigarta. Tunda take bata tabajin tsoron kwana cikin dakin ba sai a yau,tanaso ta miqe ta fice ta tafi dakin bibi amma tsoron ya hanata motsi. Qarar rufe kitchen da tanja tayi tayi mugun kada mata ciki,sai zuciyarta kawai ta bata yaa maina ne yazo zaiyi abinda yace din,abinda ya qarasa firgitata ta saki qaramin ihu hade da hawaye "Wayyo bibi,ki taimakeni" muryarta tanja dake niyyar wucewa taji,abinda ya dawo da ita kenan,ta murza