Sashe 17
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Taurin kai da zallar kafiya kawai ya hango cikin idanunta,wannan ya sake zafafarshi ya daga hannu zai wanke fuskarta da mari,abu daya da yake sanyawa ya samu sasaauci akanta. Har ta runtse idanunta tana jiran jin saukar marin,zuciyarta na ayyana mata muddin ya sauke tafukan hannunta saman fuskarta babu makawa sai ta haifar masa da dana sani,wannan wani alqawari ne data daukarwa ranta. A duk ranar da yayi kuskuren sake taba lafiyar fuskarta ya maretato a ranar sai ta sakashi yayi nadamar aikata hakan,wannan alqawarinta ne,muddin tana numfashi. "A'ah,ya haka maina?,kul......" Muryar bibi ta dakatar da shi tana takowa gurin tana daga qafarta da qyar saboda ciwon qafa da yake dan damunta lokaci lokaci. Hannu ta sanya tana karbarta daga hannunsa "A ina kuka samota?" Bibi ta fada tana riqeta da kyau tashin hankalin kan fuskarta yana bayyana qarara "Bibi bansan na fita ba nima,ciwon mara na dinga yi ni kadai cikin dakin,sai na dinga jin bazan iya zama ba shine na fita nasha iska" qaryar data sambado tayi daidai da sauka da idanunsa sukayi kan dogon wandon jikinta ruwan toka wanda da kadan top din jikinta ta rufe mazaunanta dake da wani irin shape da yake fita yanzu da kadan kadan saboda girma da ya fara zuwa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kawai ya fada yana kauda kansa. Ranar da nafessa ta fara menstruation ya tuna. Tana kwance a dakin bob cikin sutura da rufin asiri,kaf gidan babu wanda yasan da hakan ma,shi ta fara gayawa kuma shine ya fara mata tunin karatunsa da akayi musu a islamiyya. Har tayi nisa da farawa bibi ko (mamma/mahaifiyarta) basu sani ba. Yau ga diyar nafessa nata ya sameta tana gantali bisa kwalta,ya rabbb...... sultana kuwa idan akace zakka ce za'a ce anyi kuskure ko an fadi ba dai dai ba. Kasa jurewar tsaiwarsu a wajen yayi ga masu aiki,idan yanzun shi kadai ya gani waye da waye next da zasu iya gani?,wannan tunanin ya sanya ya warceta daga hannun bibi yayi gaba da ita,bai ko tsaya sauraren bibin dake faman qwala masa kira tana son tsaidashi ba. Tsoro ya sanyata kukan da bata shirya ba,tasan yau din ta shiga uku ta lalace. Abinda ya bata mamaki,duk yadda tayi zaton dokuwa zatayi ba haka bane,don dakinta ya wurgata ya juya yana barin sassan nasu. ********Karfe goma harda kusan mintuna ashirin da bakwai ta isa qofar dakin nasa. Sanye take da wani material me azabar tsada da daukar idanu,kamar yadda yake sunnarta ce sanya suturu masu tsada da daraja,ba kuma wai don alfahari ko fariya ba, a'ah ta isa ne ta kuma kai ta sanyasun. Tun asali da kuma tushenta ta fito ne daga gidan arziqi da kuma wadata,wadatar da taso ta zama sanadiyyar rushe aurenta da ABA. Karin maganar MATAR MUTUM KABARINSA itace tayi tasiri,ta kuma yi ruwa tayi tsaki wajej tabbatuwar aurensu,yau gashi harda zuri'ar samari uku a tsakaninsu. Kalar yadin ruwan sararin samaniya ne da aka yiwa ado da gold color,wannan ya sanya ta yane gashinta me santsi da golden mayafi. Kyawunta da ajinta ya fita sosai,hakanan adonta ya sake boye shekarunta. Sau biyu kawai tayi knocking qofar ya taso ya iso bakin qofar yana budewa,don qamshinta kawai ya isar masa da wacece "bonjour(barka da safiya)" maina ya fada yana fitowa zuwa falon nasa "Ka tashi lafiya?" Ta amsa masa tana takawa zuwa falon itama "Me yake damunka maina?,jiya bakaci abincin dare ba,yau lokaci yana neman gotawa baka fito ba" ta tambayeshi tana kallon idonsa. Hannu yasa ya murza goshinsa yana jin bacin ran dake ransa tun jiya har yanzu yana taso masa "suis d (am sorry),zan fito yanzu naci zan shirya" boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana juyawa "Ka shirya gaba daya don zaka kaini gidan dezatou,conducteur na(driver)baya nan" "d'accord(okay)" ya amsa mata yana dubanta har ta fice daga falon. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi yana komawa ya zauna saman kujerar falon,jiya kwana yayi zuciyarsa na gaya masa ya bar sultana da su bibi suyi duk yadda sukaga dama,tunda hakannan suka tsarama rayuwarta,bashi kuma da wani mataimaki a cikinsu din da yake gani sune dukkan wani jigo kuma ginshiqi na rayuwarsu gaba daya. Idan yayi kamar yayi na'am da hakan kuma sai zuciyarsa ta tuna masa da NAFESSA,anya idan yayi hakan ya kyauta?,ya kumayi adalci?,hannunka yana rubewa ne ka yanke ka yar?. "Kada ka sake saka hannu kace zaka daketa,diya macace ita" Maganar aba kenan da suka zauna da shi bayan ya dawo gida a daren jiya "Zata daina,wani abun akwai quruciya a ciki,amma da sannu zata daina,tsanani baya tarbiyya mainassara" Kalaman aba ya sake dawo masa. Kadan yadan daki hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe yana komawa bedroom dinsa. Yaja lokaci a falo yana tariyar abinda ya farun jiya,don haka a yanzun adan gaggauce ya shirya cikin wata shadda gezner da aka yiwa dinkin zamani,ya zauna masa das a jikinsa ya kuma yi masa kyau,duk da cewa shi din ba ma'abocin sanyasu bane. Sassanyan turarensa na ko yaushe ke tashi a jikinsa,ya tsaya gaban madubi ya gyara sumarsa me santsi da baqi ya kuma gyara gashin fuskarsa. Fuskar ta fita sosai,ta bayyanar da zallar kyawu irin na buzun asali. Yana tafe yana daura agogon hannunsa tare da duba lokacin da ya kashe. Dab da zai gifa sassan bibi wanda tun jiya bai sake komawa ta can ba,daidai lokacin da sultana ke fitowa hannunta dauke da sabuwar game dinta tana nufo harabar gidan,da alama tana neman me saita mata ne. Kallonta yayi sama da qasa da wani bahagon kallo. Vest ce a jikinta me siririn hannu da iyakacinta gwiwa,sai wando ta ciki wanda bai qarasa sauka idon sawunta ba. Kanta a bude babu koda hula bare ayi batun mayafi,sai sassalkan gashinta dake reto har dokin wuyanta wanda yake daure cikin siririn ribbon. Tsaiwa tayo cak qirjinta yana bugawa. Duk tsaurin idanunka idan ya saka maka lion eyes dinnan nasa sai ya cire maka duk wani qwarin gwiwa taka. Taku biyu tayi baya saita juya da sassarfa tana komawa ciki. Qwafa yaja zuciyarsa na sake zafafa akan zafin jiya. Duk wani abu da za'a hanata ita kuma shi takeyi. A age dinta sam bai kamata tana fitowa koda veranda dinsu a haka ba bare ta kawo farfajiyar gidan. Ga security zaratan qatti dake kai kawo a wajen. Da wannan qarin takaicin ya jefa qafansa falon ama din nasa. Ya sameta tayi nisa a breakfast dinta don har ta kusa kammalawa. Kujera yaja ya zauna,daya daga cikin masu aikinta data fara tattara abinda aka bata a wajen ta matso da zummar serving nasa sai ya daga mata hannu yana dakatar da ita. Abu biyu kadai ya buda a ciki,sai ya bari ya soma zuba Black tea,sam bakinsa bakinsu babu wani dandano. Shi kansa yasan damuwa ce qasan ransa,ya sani yana da fushi sosai da zuciya,shi yasa yake yawan kaucewa abinda duk zai bata masa rai. Duk yadda yake cakalar abincin ama tana ankare da shi,taso kawar da kai tayi banza da lamarinsa amma ta kasa jurewa,wacce jaraba ce ne wai irin haka?,har yanzu jinin nafessa baibar wahalar da rayuwarta ba?,wai sai yaushe?. Mug din tangaran din hannunta ta ajjiye,banguls din gold guda biyu dake hannunta suna bada sauti "Inaso ka shirya cikin kwanaki uku ka koma makaranta,bana kuma buqatar zuwanka a nan kusa" ta baiwa maina umarnin kanta tsaye tana kafeshi da kallo. Shima ita yake kallo kafin ya janye dubansa. Wanne irin umarni ne haka na kai tsaye daga wajen ama din?. Kamar tasan tambayar dake Kai kawo a zuciyarsa kenan ta dora da maganarta ba tare data damu da yadda yayi sak da jin maganar tata ba "Bana son ganin gilmawarka cikin gidan nan maina,ka fita a harkar 'yarsu,haka sukeson ganinta shin kai meye naka?, nafessa dai ko?,duk yadda kakai ga son nafessa ma wanda ya fika sonta ya dauke abarsa,ka rabu da nafessa ma bare sultana?...... abu na qarshe da zan gaya maka shine,nima ban yarda ka sake kai hannunka fuskar 'yarsu ba,diya macace data soma girma,banaso kada na sake ji ko gani" ta qarasa fada tana nunashi da yatsa kafin ta sauke hannun nata ta miqe tana tura kujerarta baya sannan ta fara sauka daga dining area din tana cewa "Zan shiga mu gaisa da bibi,ka dauki key din farar Ferrari na" daga haka tayi gaba taba qwalawa me aikinta kira kan ta dauko mata hand bag da mahadin shoe dinta. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 18 Dezatou din na daya daga cikin manyan abokan business na ama,sannan kuma qawa a gareta ta hannun damanta. Mansion House ne da ya cancanci wannan sunan,me dauke da manyan katangu da kuma gini na alfarma tsakiyarshi. Gate na biyu suka zarce kai tsaye bana sun samu tsallake gate din farko, already tasan da zuwansun,don haka maina yana tsaida motar tana isowa wajen. Gwanar fara'a ce da son mutane,don haka fuskarta wasai da fara'a take cewa "Wai wai,yau maina nake gani hamdee.......da kin gayamin tare kuke ai da na shirya tarbar baqo na musamman" dan murmushi ama tayi,tana jin dadi sosai akan yadda dezatou ke nuna qaunar maina a fili. Tadan kalleshi kadan,tasan cewa kawai ya kawota ne saboda fushinta na jiya. Har sunyi gaba dezatou ta juyo "Shigo mana maina,ya zaka tsaya a nan,kaimafa nan din gidanku ne" kansa ya girgiza kawai yana dan sakin fuska kadan "Zan jira nan cikin mota,akwai wayar da xan amsa" "Bazai shiga bafa dezatou,rabu dashi" ama ta fada tana yin gaba "Shikenan,zan turo meena ta kawo maka ruwa" ta fada tana bin bayan ama. Cikin motar yayi zamansa yana latsa wayarsa,shige shige kawai yakeyi cikin Instagram yana bibiyar pages din da yakeso yake kuma bin labaran da suke dorawa kullum. Wani dogon tsaki yaja ya sanya tafin hannunsa yana dafe goshinsa kamar wanda goshin nasa ke masa ciwo,sai ya maida kansa ya jinginar ga kujera yana lumshe idanunsa yana jin zafin abinda ya gama karantawa a wani page yanzu yanzu. Labari ne akan fyade da aka yima wata budurwa,sau da dama yakanyi dana sanin daukar wayarsa aduk sanda yaci karo da labari makamancin wannan,ba kalmar da ya tsana ya kuma qi jininta irin kalmar FYADE din. Knocking din glass din windown qofar da aka fara yi shi ya sanyashi bude lumsassun idanunsa a hankali. Tana tsaye daga