← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baiga uwar da akayi mata ba,uwa uba ma hukuncin da zaiyi matan baiyi mata shi ba. Wannan ya tunzurashi ya taka a zafafe ya finciko hannunta yana tambayarta cikin tsawa kan abinda akayi matan. Wani ihu ta qwala kai kace ya karyata ne gida biyu. Ihun nata da yaja hankalin aba dake tattaki ta bayan gidan. "Lafiya?,ke sultana meye?" Ya kuma jefa mata tambayar yana isa gareta hadi da kamo hannunta. Kai kawai maina ya kawar yana hadiyar wani abu me cikin wuyansa,iya yadda take kukan kawai yana sake bata masa rai da tunzurashi. "Don nace bazan hau bus scoloire ba shine yakemin fada zai dakeni,ya kamamin hannu inajin ma ya karyani" ta fada tana miqawa aba hannun nata. Hannun ya kama yana dubawa da kyau hadi da jujjjuyashi,sai ta saki 'yar qaramar qara "Wayyo Allah na" ta fada hawaye shabe shabe saman fuskartata,kai kace da gaske karyata din yayi "Sannu sultana,ya isa,sannu" aba din ya fada fuskarsa na nuna alamun abun ya tabashi "Ina modu" aba ya fada yana duban sararin gurin "Gani ranka ya dade" "Jasu ku tafi makarantar,kai hassane......" "Yallabai" ya fada yana matsowa cikin girmamawa "Ka fiddo wancan motar,a wanketa a duba lafiyarta,daga yau ta zama ta daukan sultana" a dan hanzarce maina ya daga kansa ya dubi aba din,ransa yana motsuwa. Da gaske dukkan abinda takeso sukeyi mata kenan?,ya daga tayi hukunci irin nata sai a biye mata. Idanunsa suka hada da aba din,sai ya jefa masa harara abinda ya sanya maina sake kauda kansa kenan. Akan sultana babu abinda ba zasu iya yi ba kenan?. Ransa a matuqar bace ya soma barin wajen. Yayin da sultanan ta bishi da kallo dariya can fal qasan ranta,tana fatan inama zai waiwayo ta samu damar yi masa gwalo,ko ba komai yau ya gane matsayinta a wajensu aba din. Ya jima zaune cikin sofa din falonsa yana jujjuya abubuwa. Yayi dukka iya lissafinsa amma ya kasa bashi dai dai,ba haka yakeson rayuwar sultana ta tashi ba,to amma ta yaya zatayi saiti kamar yadda yakeso?,bayan wadanda yake da buqatar dafawarsu dukka su dinma idanunsu a rufe yake. Idonsa ya lumshe yana fidda iska daga bakinsa,yana qoqarin kawar da zuciyarsa daga yunqurin fara jin haushin yarinyar. Makaranta yakeson komawa,amma tunanin abinda zai bari idan ya tafin shike taka masa burki. Knocking yaji anayi,amma har aka kwashe wasu sakanni ya gaza bada umarnin a shigo din. Sai bayan da ya tabbatar ba za'a daina masa knocking din ba sannan ya motsa bakinsa yana tambayar waye "Goumar ne" ya amsa masa daga wajen "Entrez(shigo)" ya amsa shi yana sauke qafafunsa qasa tare da qoqarin saita yanayinsa. A nutse ya murda qofar yana shigowa,goumar baqin buzu kamar yadda sultana ke kiransa kai tsaye,sunan kuma ya soma bin bakunan wasu 'yan gidan. Shine d'a na farko ga Oncle bashar qani ga aba wanda shike binsa. Kusan shine wanda yabi maina sawu da sawu,ya dauki dabi'unsa da yawa bawai ta siffar kwaikwayo ya siffantu da dabi'ar haka kawai ba,a'ah bibiyace ta jini kamar yadda ake iya samu daga kowa cikin kowacce zuri'a. "Ama tana kiranka,tace votre petit d jeuner est pr t(abincin safenka ya kammalu)" qafafunsa dake saman dan table din mulmulallen katakon ya sauke yana dan sake ciki da idanunsa tamkar bayason budesu gaba daya "Zauna goumar" maina ya buqaci haka daga gareshi. A nutse ya samu seat ya zauna,sosai mainan ya gyara zamansa yana kallonsa "dites-moi(ka gayamin)iya lalacewan da sultana tayi" a dan rude kadan goumar ya daga kansa yana duban maina din re(haka yake kiransa wasu lokutan) lalacewa kaman yaya?" Qaramar Ajiyar zuciya ya sauke idanunshi akan goumar "Eh,na fara tsorata da tarin halayenta,ina tsoron kada ya zama maza sun hure mata kunne......" Kai goumar ke girgizawa "Ban taba ganin abu mai kama da wannan ba fr re,banajin kuma haka" gyara zama maina yayi yana dan jin nutsuwa kadan "Amma ka gayamin,wanne kallo za'a yima mace me irin halaye da dabi'un sultana?,idan a nan qasar ba aibu bane a sauran wasu qasashe fa?" Shuru goumar yayi ba tare da yace komai ba. Halayen sultana suna bashi mamaki ta yadda sukayi matuqar shan banban da na sauran yaran gidan,to amma kuma fadin hakan ga maina kamar qarawa fetur wuta ne. Shurun goumar ya sanyashi miqewa kawai. Sai da ya biya ta bedroom dinsa ya zare takalman qafarsa ya maida gurbinsu da slippers sannan ya fito. Har kullum sassan Ama din nasa daban yake da sassan sauran matan gidan ba,bawai don tana mahaifiyarsa ba a'ah,zai iya cewa kaf duniyarsa,a kuma 'yar taqaitacciyar rayuwarsa bai taba katari da macen da tayi tsananin sanin ciwon kanta irin ama din ba. Masu aikinta ne qwara hudu rak da bata tana sauyasu ko ragesu ba keta kai kawo suna sake gyara tsarin dining din. Kai tsaye za'a iya kiran ama din da ruwa biyu,'inda ana tsotsar boko to tabbas za'a iya cewa ita kam ta tsotsi boko daga jinin mahaifinta. Ta wani kuma idan kace bafaransiya ce shima bakayi kuskurenba,saboda yadda abubuwa da yawa na qasar haihuwar mahaifiyarta ya kama jikinta ya kuma zame mata jiki. Kamar kowanne lokaci yau ma tana saman qawatattun kujerun da aka kewaye falon da su har rukuni uku. Hankalinta ya tafi sosai kan system dake kan cinyarta,ya kuma tabbatar abinda ya shafi business dinta ne. Fararen idanunta ta daga tana amsa sallamarsa gami da dan binsa da kallo,har cikin ranta tana jin wani abu mara dadi yana motsa ranta. Damuwarsa bata taba boyuwa a wajenta koda kuwa yayi qoqarin yin hakan. Duk abinda ya faru dazun saman idanunta akayishi,ta kuma tabbatar yana daya daga cikin abinda ke damun ransa yanzu hakan. "bonjour ama(barka da safiya ama)" "matin" ta amsashi a taqaice tana gyara zaman eye glasses dinta. Sai da ya zauna sosai sannan ta dauki qaramar wayar dake gefanta tayi kira zuwa kitchen,magana tayi na mintuna qalilan sannan ta ajjiye wayar. Sake maida dubanta tayi a kansa "petit-d jeuner(breakfast)naka wa ka barwa?" Bai amsa mata ba sai shafa lallausar sumarshi kawai da yayi da daya hannun nasa yana jin damuwa cikin qirjinsa "Ba kowa ama" dan shiru ya ratsa tana danne dannenta a laptop kafin ta sake magana "Yaushe zaka koma bakin karatunka?" Tayi masa tambayar tana zube masa idanunta. Qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya gyara zamansa yana cewa "Yau kuma ama?" Kai ta gyada cikin basarwa "Oui(eh)......" Ta fada kai tsaye "pourquoi?(me yasa?) Ama,ko kin gaji da nine?" Yayi tambayar cikin salon tsokanar da ba kasafai ya fiya yinta ba a tsakaninsu,duk kuwa sa cewa akwai sakewa qaunar juna da kuma fahimta,amma halinsa na miskilanci ya sanya ba komai yake iya yi ba "Eh......na gaji da ganinka a haka kana ragaita tsakanin abinda ba zaka iya gyarawa ba......ba sultana ce ba?, itace ta tsaidaka ko?" Tayi masa tambayar idanunta tsakiyar nasa. Zare idanunsan yayi sannan ya motsa labbansa a hankalin cikin son kare sultanar,kada ta sake baqi cikin idanu da zuciyar ama din "Non ama(a'ah ama)" "To menene?.....sultana ce haka sukeson su ganta,haka suka tsara mata ta taso ta kuma rayuwa,to kai a suwa?. Don kawai kana yaya ga mahaifiyarta?,duka duka shekarunka nawa maina?,tu as beaucoup faire dans ta vie(kana da abubuwan yi da yawa cikin rayuwarka) ka fuskancesa ka barta tayi rayuwa yadda suka tsara mata,ne perds pas ton temps(karka bata lokacinka)" ta qarashe fada cikin zafi zafi. Shuru yayi yana sauraren sautin muryarta,zuciyarsa na sake motsawa,gaba kura baya sayaki,ta yaya zai iya bari sultana ta taso a haka?,duk kuwa da cewa abune da da yawa daga cikin al'umarsu suka taso suna ganinsa,kusan ya zame musu ruwan dare,ba kuma komai bane,amma kuma shi cikin jininsa ya tsani wannan tarbiyyar tasu sam,yana qyamatarta qwarai da gaske,da kuma gasken turawan France sun musu illa qwarai,sun shiga tarbiyya al'ada da kuma dabi'unsu "suis d (am sorry)" ya fada kawai a taqaice don bashi da wata kalma da zai iya furtawa bayan wannan a yadda yaga ran aman ya baci. Wannan duka ya hadu ya dinga damunsa cikin rai. Duka duka abincin bai iya ci me yawa ba ya tashi,abinda ya sake bata ran ama kenan. Tana ganin duka ya tattara damuwar sultana ne a ransa,wanda koda shine ya haifeta iya abinda zaya nuna kenan. Yayin da shi nasa damuwar tafi karkata ga yadda soyayya da zallar gata da su bibi ke nunawa sultana keson zamewa tarnaqi cikin samuwarta da maidata cikakkiyar mace wadda yakeson ya raina. Cikakkiyar macen da duk mijin da Allah ya bata zaiyi alfahari da zamowarta matarsa. Mace daya tamkar da dubu da tarbiyyarta zata fita daban da sauran mata cikin al'ummarsu. ********** A nutse bibi ta shafa addu'arta kan fuskarta da dukkan tafukan hannayenta guda biyu. Can qasan ranta abun yana ci gaba da tsinkular ranta,fargabarta tana sake qaruwa kan sha'anin sultana da maina. Ta gaza fahimtar ina ainihin matsalar take?,sai ya dafa qasa da dukka hannuwanta tana tashi daga saman lallausar farar dardumarta. Babban falonta ta fito cikin nutsuwa da kamalar data cika fuskarta. Akwai dattako sosai akan fuskarta da kuma cikar dattijantaka. Hakanan tsarin halittarta yake,tana da nutsuwa qwarai cikin komai nata,SULTANA CE kadai rauninsu. Tanja kadai ta samu zaune cikin falon tana kallo. Lokaci ne na hutu ga dukka ma'aikatan gidan,bata kuma tsawwalawa ga kowanne ma'aikaci dake qarqashin sashenta,suna walwalarsu tamkar kowanne mutum cikin gidan. Kusan ma'aikatan sashenta ma sunfi na kowanne sashe samun 'yanci. "Sannu da fitowa" tanja ta fada tana lanqwasa qafafunta "Yauwa tanja,ko zakiyimin kiran maina don Allah?" "Maina kaman ya fita shi da alhossain" "Indai tun dazunne na tabbatar zuwa yanzu ya dawo" bibi ta fada tana zama saman daya daga cikin kujerun hadi da ambatar sunan Allah "To" tanja ta amsawa bibi tana miqewa ta gyara dankwalinta sannan ta nufi waje. *HUGUMA* *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 13 Waya ta sameshi yana yi. Dogon wando ne fari qal a jikinsa da singlet fara itama,sai ya ajjiye wayar yana duban tanja data tsaya nesa da falon "Mainasara bibi ce take kira" "d'accord" ya amsa can qasa da muryarsa me sanyi. Ko daya baiyi niyyan shiga sassan bibi din ba,ya sanyama ransa ma sai tayi cigiyarsa kafin ta sake ganinsa,saboda yana ganin cewa suna da tagomashi wajen lalacewar ginin da ya fara yiwa rayuwar sultana. Saidai kuma bibi din ta wuce ta kirashi yaqi zuwa,don haka ya sauke
Chapter 12 · 0% Book details