Sashe 4
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
zube fes akan fuskar bibin. Cikin nutsuwar da tun yana mitsitsinsa ta zame masa dabi'a kuma halayyarsa yake magana "Amma why bibi?,me yasa za'a bari halaye da dabi'unta su canza?,ya akayi sultana ta canza?,ba haka na tafi na bar muku ita ba" ya fada har tsakiyar ransa yana jin radadin rushewar tubalin ginin tarbiyyar da ya fara yi mata,wadda tasha banban data qasarsu. "Duk wani iya bakin qoqari inayinsa mainassara,to amma kasan komai yana da alaqa da muhalli da kuma abokan mu'amala na yau da gobe" kansa ya girgiza yana furzar da iska me zafi daga bakinsa "Bibi,goumar ya fara fadamin,mais(but) na dauka kawai surutu ne irin nashi,certainement(definitely)banji dadin abinda idanuna suka tarar ba". Ajiyar zuciya bibi ta saki,itadai ta sani,babu ta inda tayi sake ko saakcin tarbiyyar,tun daga kan uwayensu ma ballantana su,kwadayi da son samun cikakkiyar tarbiyya ya sanya ta yiwa hamidou magana,suka tattara suka bar niamey izuwa maradi,maradinbda take kallo da hangen sunfi kusa,alaqa ta qut da qut da nigeria. A nutse take masa bayanin iya abinda zai iya fahimta. Kansa a duqe yana latsa wayarsa tare da sarrafa maganganun bibi cikin kansa,yana kuma son lanqwashe bakin matsalar da kuma yadda zai bullo mata. Nunfashi ya zuqa yana daga qawatattun idanunsa wadanda suke da wani irin shape,idanun da sultana din ta sakawa suna da yeux de lion(lion eyes) ya zubesu kan tafkekiyar TV plasma din dake maqale a bango,suna haska labaran dare a channel din niger 24tv. K'aramar yarinya ce da bayanta ya mamaye fuskan tv din,tana bayanin yadda wani matashi yayi mata fyade(rape). Kasuwa hankalinsa yayi gida biyu,fiye da rabin hankalinsa yana kan labaran,yayin da wani kaso dan kadan kunnuwansa ke ga bibi. A hankali wani abu ya soma tsaya masa a rai,bacin rai ya fara sauka a hankali saman zuciyarsa yana mamayeta. Maqurar bacin ran da hatta bibi dake zaune a wajen sai data fahimci hakan. Wani dogon tsaki mai matuqar sauti ya fidda,dai dai sanda tani shugabar masu kula da sassan bibi ta kawo tray na qarshe ta ajjiye "Miqo min t commande(remote)" cikin girmamawa ta rusuna ta juya ta isa ma'ajiyarsa ta dauko ta miqa masa. Channel ya canza gaba daya,zuciyarsa na wani irin quna da zafi,babu abinda yafi tsana a duniya a yanzu irin kalmar FYA E. A duk lokacin da aka haska wani mutum dauke da laifin fya e,yakanji inama za'a bashi damar hukuntashi,tabbas idan har ace zaya samu irin wannan damar,zaiyi masa hukunci ne mafi tsanani,wanda ko mace akace masa gata zai yanka da gudu ne ya gusa daga wajen,sakamakon azabar da shi daya yasan yadda take da zai ana a hannunsa. Harshensa har aci yakeyi sanda ya bu e baki yana magana da bibi "majorit ire iren wadan nan abubuwan akwai sakacinmu dake haifar dasu" warai kuwa,wasu abubuwan kuma addarar bawa ce daga sarkin mabuwayi" gama maganar bibi yayi dai dai da fitowar sultana. Da ido bibi ta bita tana kallon yadda fuskarta tayi jazur,sai kawai ta miqe a hankali tana sauka daga gurin dining din,abinda ya sanya sultana tsaiwa cak tana kallon bibi din,don ita ba zata yarda ta barsu a wajen daga ita saishi ba,ya sake taba lafiyarta ba gaira ba dalili "Ina kuma zaki tafi bibi?" Ta tambayeta tana karya wuya,hawaye nason taruwa cikin idanunta "Qaraso ki zauna" maina da idanunsa yake kanta ya fadi,fuskarsa a matuqar hade,abinda zai alamta maka babu wasa ko misqala zarratin a tattare da shi. Duban cikin idanunsa tayi,niyyarta tace ba zata zauna din ba,to amma kuma sai kalmar ta maqale mata saman harshenta. Kamar ba zata qaraso din ba,amma yadda kaifaffun idanunsa suka ritsata ya sanya ta sauya akalarta zuwa inda yake mata umarnin,zuciyarta kamar zata fashe,duk wani qaunar da take masa taji ta fara raguwa sosai cikin ranta,sai wani haushinsa da takeji. Tana matuqar qaunar lafiyarta,hakanan bata qaunar duk abinda zai taba mata lafiyar. Karo na uku kenan ana sauya mata makaranta saboda attempting din dukanta da aka taba yi sau daya a kowacce makaranta. Tsaki yaja dai dai sanda ta zauna saman kujerar,ta dafe hannunta tana saman kujerar tana gyara zamanta sosai saboda qafafunta ba zasu kai qasa ba,duk da tana cikin sahun yara masu tsaho. Tsakinsa ya sake qular da ita tare da bata haushi sosai,sai ta juyar da kanta gefe tana murguda bakinta tare da sakin qananun surutai qasa qasa. "Duba nan" ya fada yana tattara dubansa a kanta. Tilas tabar kallon hagunta ta dawo da kallonta zuwa gareshi "Wannan kayan.......ban hanaku sakasu ba?,kun dauka a french muke?" Ya tambayeta a kausashe,har cikin ransa yana jin haushi da takaici. Zuwa lokacin alamomin girma sun fara bayyana a jikinta,tana da girman jiki wanda yake da saurin bayyanar da girman d'iya mace,hakan kuma yasan yana da alaqa da rayuwar jin dadi da tsantsar kula da jikinta ke samu na dukkan wani abu da zai inganta lafiyar jiki data fata ya kuma tabbatar da girma na dan adam a lokaci qanqani. Ya sani kusan da madara aka raineta,har ya tafi akan shan madara ya barta,duk da bashi da tabbacin har yanzu tana sha?,yana ji a jikinsa ma lokaci yayi da zata ajjiye duk wasu dabi'u na quruciya,ta fuskanci girma wanda yake dab da iso mata. "Last zuwan ama Nigeria na qarshe ta kawowa kowaccenku wadatattun atamfofi da zata dinka,sannan dukkaninku kuna da abaya wadatacciya,wannan shine gargadi na farko kuma na qarshe,kada na sake ganinki da irin wadan nan kayan a jikinki" ya fada yana kallon idanuwanta. *ZAFAFA BIYAR FAMILY* *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba* *_ZAFAFA BIYAR_* *_SABUWAR SHEKARA_* *_SABON TSARI_* *_SABBIN LABARAI_* *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_* *_CAKWAKIYA_* *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_* *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_* *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_* *_KWANTAR DA ZUCIYA_* *_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_* *QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA* *KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo) *TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul) *AMEENATU* (Mamuhghee) *GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma) *_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_* *_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_* *TSARIN SHINE KAMAR HAKA* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *THANKS FOR CHOOSING US* *_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* Page 04 https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr Haushi kamar zai kasheta,wai shikam yaa maina yana kallonta ne har yanzu a little sultana da ya bari shekara hudu baya?,itafa ba zata dauki ire iren wadan nan abubuwan ba bayan tana kallon yadda sauran qawayenta na makaranta ke rayuwarsu cikin 'yanci. Kaf cikinsu ma bataga me saka wata aba wai atamfa ba,meye hadinsu ma da ita?,sai ita zai bullowa da sabon tsarin doka?. "Ni ban iya daura zane ba" ta amsa masa tana turo baki manyan fararen idanunta na kallon shinfidadden gilashin dining din,ji takeyi kaman ta mangareshi,har yanzu tana jin radadin marinsa akan fuskarta. 'Dan dukan table din yayi da tafin hannunsa "regarder(look),ki iya ko baki iya ba duka zaki koya ne,muddin kinaso kiga ainihin mainassara kici gaba da yimin musu da kuma dan banzan kafiya da taurin kan da kika koyo" "Kai kuma shegiyar masifa da bala'i da baqinciki da bacin rai kamar tsohon kuturu" ta fada cikin ranta. Baiji abinda tace ba,amma yaga sanda jajayen lips dinta suke motsawa "Me kika ce?" Ya jefa mata tambayar data kusa sakata fadowa daga kan kujerar da take zaune akai din. Da sauri ta daga fararen idanunta ta kalleshi dasu tana motsa baki '"ni?,ni bance komai ba" idanunsa ya lumshe kadan ya budesu. Ya tabbatar tayi magana,akwai abinda tace,amma cikin sabon halin da ya fuskanci ta sake kota koya harda iya fadin qarya kanta tsaye. Bayajin zaiyi wuya ya sake tafiya niamy haka ya zauna,gwara duk sati ya dinga tahowa maradi yana hutun qarshen makonsa a nan. "Dauki abinci kici" ya fada yana nuna mata tsadaddun warmers din dake jere saman dining din "Mari!,mari!!" Ta fara qwala kiran sunan kamar zata saki kuka. Da kallo ya bita yadda ta narke kamar me ciwo tana kiran sunan mai aiki,tana nufin ita zata zuba mata kenan,zubawar ma bata iyawa?. "Ya isa haka karki kashemin dodon kunne" ya fada yana wurga mata wata iriyar harara wadda bata taba ganin ya mata irinta ba. Da kallo ta bishi ranta yana baci,sai taji idanunta na marmarin juyewa itama ta mayar masa da hararar da yayi mata din,to amma yana kallonta ta dauke kanta gefe,zuciyarta tana sakeyin zafi,haushinsa na sake cikata "Nidai wallah ba zai takuramin ba,mutum ba ubanka ba ba komi ba" ta fada qasan ranta.