Sashe 21
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hannunta. Sanda ta waiwayo taga shine sai da taji tamkar jinin jikinta ne tsaf ya qone,wata mahaukaciyar razana tayi,amma cikin qasa da minti guda wannan zuciyar ta yunquro ta kuma fara haska mata tarin tozarci da asarar da zaya janyo mata matuqar bata jajirce ba. Wannan ya sanya ta turje sanda yake qoqarin riqeta da kyau ya kuma janyeta daga cikin gurin. "Ka sakeni mana,me nayi maka?" Ta fada tana bata fuska da turo baki gaba cikin tsiwa da rashin kunya. Yana waiwayowa abu na farko da ya fara yi sauke mata wani zazzafan mari da tunda ya soma dora hannunsa saman fuskarta bai taba mata irinsa ba. Marin da ya sanya ta gigice gaba daya ta kuma tabbatar da cewa ashe a baya qaryar jin zafin marinsa takeyi,yanzunne ta tabbatar da ainihin abinda ake nufi da mari,yanzu ne kuma ta gasgata gaskiyar zafin da yake dashi na gasken gaske. Mari na biyu daya qara mata shine ya cisge duk wata kafiya tata da taurin kanta,bakin cewa ya saketa ta koma ya mutu murus. Ya janyeta da zafi zafi tana gurdewa saboda tsinin takalman qafarta,bai kuma saketa ba ako ina sai cikin motar sa,ya maida murafun ya rufe ya murza key ya kulleta. Hannayensa ya zuba duka cikin aljihun wandonsa yana kallonta sanda take rusa kuka yana kuma furzar da wata zazzafar iska. Shi kadai yasan me zuciyarsa ke raya masa a kanta. Sultana a hotel?,tafiyarsa har ta sake sanyata ta kuma lalacewa haka?,me bibi takeyi?,aikin me aba yakeyi?,haka ake gata?,sudin haka akayi musu?. Qafa ya saka cikin zafin rai yadan daki gaban motar sai ya juya yana nufar wajen yahuza wanda baisan ma yazo ba,cikin ransa yana rantsuwa da Allah yau kam za'a kawo qarshen komai,duk da ama taja kunnuwansa akan sabgar sultana din,amma yanzun an fara kaiwa shingen da idan basu tsaya ba zasuyi kuka dukkaninsu da idanunsu,tunda zuwa yanzun ta fara kaiwa shekarun girma,shekara goma sha uku nan da shekaru biyu budurwa za'a yi kiranta. Koda yaje yadan samu layi,ba mutum ne shi me take doka ba,duk da akwai sanayya tsakaninsa da yahuza ta regular customer da business owner amma sai yabi layi kaman kowa. Saman kujerar roba dake wajen ya zauna,saidai sam bashi da walwala ko sukuni,saboda wani irin zafi da zuciyarsa take masa. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 21 ______________________________ *_KUSAN FA MU DUK TA GEFEN DA QAMSHI YAKE MUNA WAJEN ,AHTO,KU MATSO KU GA WANI ABU*_ _ADVERT MKBEES PERFUMERY _(GIDAN KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_ _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, _KAI DAKA FESA KAJI DADI NAKUSA DA KAIMA YAJI DADI.TOH KU MAR-MATSO KUSA_ _MUN KUMA ZUWA DA KAYAYYAKIN_KAMSHI MASU SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI _*KU GARZAYO MKBEES PERFUMERY _DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN CHADI DA SUDAN AKWAI OIL PERFUMES,AIR FRESHNER, CARPET SPRAY DA TURARUKAN MOPPING DANA WANKA DANA GADO,LABULE DA KUJERU , BANDAKI DA DRAWER . _AKWAI TURAREN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DAHANA TSAMIN GASHI DA KUMA LAUSHI. AKWAI HODAR HAMMATA ME TAIMAKAWA WAJEN HANA WARI DA TSAMI ACIKIN LOKACIN ZAFIN NAN,AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYEN DAYA DAYA. _ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._ _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN MKBEES PERFUMERY. KO BAKU SIYA KAYA BA KUYI SAVING NUMBER DINTA KUFADA MATA TAYI SAVING NAKU DOMIN KOYON DUBARUN KASUWANCI KYAUTA A STATUS DINTA. _NAMBAR WAYAR SU: 07011113951,07032456061. INSTAGRAM :Mkbees_perfumery. _YOUR NUMBER ONE PLUG FOR KOMAI KAMSHI A TRIAL WILL CONVINCE YOU. _______________________________ Kuka takeyi sosai tana murza fuskarta dake mata wani irin mahaukacin radadi,baya ga zafin marin babu abinda yake zuciyarta illa asarar zuwa birthday din dake tunkarota tunda tayi amanna zuwa yanxu sha'ani yayi nisa,kuma dukka su lamira aminata da yasmine suna ciki. Yaushe ma yazo garin bayan kwanansa nawa duka da tafiya?. Me yasa bashi da aiki sai marinta?,abinda wani halitta be taba yi mata ba sai shi?. Wata irin mahaukaciyar qiyayyarsa da tsana me qarfi ta sauko mata sanda taga fuskarta a jikin mirror,ta hada wani mugun ja,shatin dogayen yatsunsa kwance akan fuskarta. "Wallahi daga yau ba zaka sake marina ba,bakaci bulus ba" ta fada a fili cikin muryar kuka "Tome zaki masa ki rama?" Ta tambayi kanta da kanta. Gilmawar wani dan sanda ta bakin motar yana nufar can wajen yahuza saita zame mata tamkar amsar tambayar ta,cikin sauri ta koma bakin window din,akwai sauran space da bai qarasa rufewa ba don haka ta saka kanta ta wajen ta fara sharara ihu tana kallon saitin policestation din. "ku taimakeni!,wayyo Allah,don Allah wani ya taimakeni!!" Ta fadi tana kallon gate din policestation. Shuru ba kowa ta wajen,abun da ya tabbatar mata sai tayi da gaske,kuma tana buqatar tayi komai da sauri kafin maina ya cimmata,don haka sai ta qara bude dukka muryarta da qarfi tana fadin "Ku taimakeni a taimakeni wayyo Allah wani ya taimakeni!!!,ku taimakeni don Allah SATO NI yayi!" Maganarta ta qarshe tayi dai dai da dawowar police din dake riqe da wata qaramar baqar leda,da alama wani abun ya siyo. 'yan sanda ne tsayayyu da sukasan abinda sukeyi cikin kulawa da haqqin kowa,ba batun cin hanci ko rashawa burinsu dai kawai aikin da hidimtawa zuwa ga qasarsu NIJER. Da sassarfa ya nufo gurin,sai sultana din ta qara bude murya da kyau tana sake sakin ihun neman taimako "Ke!,menene?" "Me motarnan ne ya satoni"ta fadi cikin kukan baqinciki ya bata mata ranar gaba daya. "Sata?" Bai gama jiran amsarta ba ya waiwaya yana qwala kiran inoussa da idrissa. Cikin qasa da second biyar sai gasu sun iso,fitowar tasu da tsaiwarsu a wajen suna cigiyar waye mamallakin motar ya fara jan hankulan jama'a ta wajen. "A gaida hajjaju don Allah" yahuza ya fadi yana miqawa maina ledar naman "Zataji" ya amsa da sauri don yana burin ya isa gida kan sanda aba ke dawowa. Da mamaki yake kallon motar tun kafin ya qaraso yadda 'yan sanda suka baibayeta "Duk yadda akayi me motar yana ta nan baiyi nisa ba,ku bincika" gabansa ya tsinke dajin abinda suke fadi,ko wani abu ya faru da sultana dake cikin motar,wannan ya sanya ya qarasa da sassarfa yana fadin "Gani,nine me motar" yadda dukka aka zuba masa idanu yasa yasha jinin jikinsa "Kaine me motar?" "Eh" ya gyada kai "Satar mutane da ranar Allah kuma don rashin kunya ka daukota ka aje cikin jama'a kusa da hukuma saboda ka maida polisawa shashashai?......idrissa,karba maqulli ku sakata a ciki shima ku shigo dashi yayi bayani". Gaba daya kansa ya qulle,baima fahimci komai da suke fada ba. Ta gefen sultana kuma sai taji hakan baiyi mata ba,ba ciki taso a shiga ba,a nata plan din zasu budeta ne ta fita,ita kuma sai ta samu ta koma gurin birthday din,sauran kome zai faru idan sunje gida wannan wani abune na daban. A nutse kuma cikin zallar mamakin daga inda batun satar mutane ya bulla ya shiga motar ya kunnata ya kuma gyara tsaiwarta ya gangara da ita cikin police station din. Su suka nuna masa inda zai ajeta ya ajjiye din kuma ya fito yana bin bayansu zuwa cikin station din. Gurin zama yayi musu a gurin da ake daukan statement,har a lokacin tunaninta gaba daya yana wajen birthday din burinta daya suce ta tashi tayi tafiyarta ta samu cikakkiyar damar zuwa ayi sha'anin da ita "Kikace satoki yayi daga ina?" DPO ya jefawa sultana tambayar yana kallonta. Da sauri tana kuma sharbe hawaye ta gyada kai "Satoni yayi zaiyimin FYA'DE" Ta fada da confidence tare da nuna tsoro zalla saman fuskarta. Wani mugun duka zuciyarsa tayi,irin dukan da bata taba yi masa irinta ba iyakacin tsahon rayuwarsa. "Sultana!?" Ya kirayeta da wata madaukakiyar tsawa fuskarta cakude da wasu al'amura masu nauyi da suka hada da razani da kuma firgici me yawan gaske "fermez-la(shut up)" shima dan sandan ya dakawa maina tsawa cikin nuna bacin rai qarara "Bude mata ido zakayi ka hanata fadin gaskiya?, idan har kai me gaskiya ne ka bari ta gama jawabinta sai kayi naka" ya fadi yana muzurai idanunsa akan maina,kamar yadda shima maina din ya kafeshi da nasa idanun,maqoshinsa yana sama da qasa,idanunsa kuma sauya launi a hankali a hankali,saboda wata muguwar suya da kalmar FYA'DE ZAIYIMIN din data fada ke yi masa. "Kin sanshi dama kenan?" DPO ya sake tambayarta yana maida hankalinsa kanta. Ga tarin mamakin maina saita girgiza kai da sauri "Ni bansanshi ba,bansan wayeshi ba,ban taba ganinsa ba sai yau,a hanya ya ganni ya satoni,yanata qoqarin min fyade din......." "Sultana!" Ya kuma kiran sunanta jin tana sake yunqurin dangantashi da kalmar fyade "vas-tu te taire ?(zakayi shuru ko kuwa?" Dan sanda da tasa budaddiyar muryar me kauri data lullube ta maina ya fada yana tashi kaman tsaye kaman zai rufeshi da duka,kasancewar ko a girme ya girme masa. Zuciyar 'yan maza ta motsa,ya mance sam sam wai a gaban hukuma yake, idanunsa rufe ya soma zazzagawa dan sandan masifa "Ta yaya zaka zauna yarinya qarama ta dinga tsara maka qarya abinda bai faru ba ehhh?" "Au qarya ma takeyi?,wannan marukan na fuskarta duk na meye?,ko ku baku gani ba?" Ya fadi yana tambayar sauran Yan sandan dake wajen "Gaskiya ne Monsieur(sir),dama duk sanda zasu aikata hakan saisun mammare fuskar yara harda duka na rashin imani" wata police mace dake tsaye a wajen ta fada cikin hasala,da alama itama akwai adawa me qarfi tsakaninta da fyaden "fermez-la(shut up),kina sanye da kaki amma baki iya banbance tsakanin me gaskiya da me laifi,kuna hukunci da abinda aka baku labari!" "Zaginmu zakayi?" DPO din dake tsaye a daura dashi ya fada cikin hasala "Bazan zageku ba amma na raina iyawark......." Baikai qarshen zancan ba DPO din ya zuba masa lafiyayyen mari saman kyakkyawar farar fuskarsa. Tamkar gilmawar walqiya,tamkar kuma gizo sultanar taga saukar mari kan fuskar maina. Tayi muguwar razanar da har sai data miqe daga saman kujerar da take zaune a kai "Koma ki zauna,ai tunda kike nan tu es en s curit ,bai isa yayi miki komai ba,mara gaskiya kawai,ba daka mata tsawa da hanata tona maka asiri zakayi ba,d fendre kanka zakayi kaima indai kai me gaskiya ne,ka gaya