Sashe 27
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
yake damunki ne sultana?" Bibin ta fada cikin fada fada "Ni ki qyaleni,bayan an hada baki dake za'a kasheni a gidan nan" idanu bibi ta fidda waje "Kisa sultana?,ashe baki da hankali" "Allah bibi,kawai sai ku auramin maina?,idan aurenne saiku bari na sake girma naga wanda nakeso ba wannan....." "Ya isa,kiyimin shuru haka haba" bibi ta dakatar da ita kafin ta sake ballo wata maganar,don a yanzun dole a hankali a hankali ta soma nuna mata yadda zata darajta maina din,tunda ko banza igiyar aure nauyi da girma gareta. A nan tayi borenta ta gama suka kuma shirya da bibi,don dama tsakaninsu ba'a shiga. Ganin bai sake waiwayar gida ba kuma babu gilmawarsa saita sake abinta sosai,taci gaba da sakalcinta cikin gidan,duk da a wannan karon abubuwa da dama bibi tana tarota,tayita zuba ido taga ko ama zata nuna wani abu ko zata dinga sanya baki cikin sha'anin sultana din amma sai tayi kaman bata cikin gidan,koda a gabanta sultana zatayi abu kaman da can baya dauke kai takeyi ta wuce abinta. Bawai don bata sane ba,tana sane da komai tana kuma biye da komai,ta watsar dinne saboda kama girma da mutuncinta kamar can baya. *_FAREWELL_* _But_ _A new chapters unfold_ ********** Satittika har guda gudu cur yayi babu shi ba labarinsa cikin gida. Haka kawai yaji baya sha'awar komawa gidan,sai kuma abubuwa sukayita shigowa na uzururrukan makaranta da suka sake riqeshi,don haka ya fidda batun ma zuwa gida,har sai da aka shiga sati na biyar. Satin da yazo da wata GAGARUMAR QADDARA......QADDARAR da ta zama sila ta wanzuwar komai. Qaddarar da dukkanin ahalin mayak'i basu taba koda hakaitota cikin tunaninsi ba. Qaddarar da ta d'aid'aita farincikin wasu da dama ta qulla wasu alaqoqi ta wargaza wasu........ta nesanta na kusa ta kuma kusanto da na nesa. Ta jefa ALHINI TARIN BAQINCIKI NADAMA DA TAKAICI ME TARIN YAWA A ZUKATAN WADANSU. _NAYI AJIZANCIN NAWA,A YAU NASO NA BADA DUKKA SHAFUKAN SAI WASU HIDIMOMI SUKA RIQENI,AMMA A GOB E IN SHA ALLAH ZAN BADA WANDA YA RAGE DIN_ _KARKI BARI A DORA TAFIYAR GUDUN K'ADDARA BAKI KASANCE DA GROUP DIN BOOK DIN NA HALAL BA_ _JAZAKUMULLAH_ [5/13, 10:00 PM] RM Fatima Shehu Musa : *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* Page 28