← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 30

Sashe 10

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jurewa. Saboda cikin qwarewa da wani irin salo yake tsinto muryar sultana din tana biye da waqoqin turawan qasar faransa din,tamkar tare da mawaqan suka rubuta waqar,abinda ya bayyana masa zallar tadda take saurarr tare da biyar waqiqinsu kenan sau da qafa. Sake ture documents din yayi ya miqe fushi na soma cin zuciyarsa har ya soma tasiri saman fuskarsa. "Ina zuwa ama" ya fada yana ficewa daga falon. Baki ta sake tabewa tana girgiza kai. Yana daya daga cikin abubuwan da sukayi mata tsaye a rayuwa yadda mainan yayi tsaye cikin rayuwar yarinyar. Yarinyar da kaf gidan babu wani yaro da yayi miqewar qafar da tayi. Ko meye ne zatayi ba wani laifi nata fitacce da ake iya gani,ko yaushe tana da immunity,maina din kadai ne yake iya keta wannan immunity din. To amma me yasa shi din bazai sanya idanu kamar yadda kowa ya sanya ba?. "Saboda nafissa" wata zuciyar ta bata amsa,sai ta saki siririn tsaki ta ajjiye takardar ta dauki wayarta. Idan daga nesa kake ka kalli wajen zakayi tunanin wani gagarumin dinner party akeyi a wajen. Dukka kusan tsararrakinta ne a wajen,wadanda sukayi shekaru dai dai da nata,sai kuma wadanda suka dara shekarunta da kadan. Abun ban mamakin da kuma daure kan shine,kusan dukkansu maza ne tsararrkin nata,sai mace qwaya daya a cikinsu. Bayan tsananin baci da ranshi yayi harda tashi da hankalinsa yayi. Ba sau daya ba ba sau biyu ba indai idanunsa dai dai suke ganin yana ganin yaran kusan duk yammaci a farfajiyar gidan,saidai bai taba kawowa wai suna taruwa cikin gidan bane da zummar sunzo wajen sultana. Gaba daya tunaninsa na bashi gurinsu almu saddi da su atta suke zuwa. Yanzun kenan duk taron yarannan maza suna abota ne da sultana?. Tambayar data sake tunzura bacin ransa,ya qara sassarfar tafiyarsa,fatansa kadai ya isa ga gungunsu da basusan ma da tahowar tasa ba. Yayin da shugabar tawagar sultana tayi nisa cikin wata irin rawa data sake bashi mamaki. Yadda take lanqwasa jikinta zakayi tsammanin babu qashi ko daya cikin jikinta. Yadda kuma take rawar cikin karsashi kadai zai tabbatar maka hakan yana mata nishadi qwarai. Tsaiwarsa guda daya ta dakatar da tarin hayaniyar da sukeyi a wajen. Kaf dinsu ba wanda hantar cikinsa bata kada ba. Sanda yasa hannu ya yiwa mp din nata wani wawan duka ta dauke dif saida kowa cikinsu yaji kamar yayi layar zana ya bace. "Ku fice!" Ya fada da gigitacciyar fusatacciyar muryarsa. Babu shiri har wani na ture wani suka soma laluben babbar katafariyar qofar data iyakance harabar farko ta gidan da haraba da biyu,inda ainihin ginin gidan yake da kuma muhallin da suke a zaune din. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* Page 10 Yadda ya rakasu da kallo haka sultana ma. Saidai kuma abinda ke zukatan kowa tsakanin shi da ita ya banbanta da na danuwansa. Zallar fushi da bacin ran yadda ya wargaza mata dabarta data saba hada musu dukka qarshen sati ita da abokai da qawayenta. Suci su sha su kuma cashe ba tare da kowa ya matsa musu ko ya adabba musu ba. Sai gashi yau rana guda daya tak,daga fara zuwar musu hutun tsakiyar karatu yana neman ruguje mata abinda ya kusan zame mata al'ada,akan meye?,ba wanda ya taba yi mata hakan a gidan sai shi?. Ta gefan maina kuwa nashi fushin yasha banban da nata. Wani bahagon kallo yake jifanta da shi cike da zallar bacin rai dake cin zuciyarsa ainun. Abubuwa iri daban daban zuciyarsa ke qiyasta masa ya aikata mata da zai zama makwafi na daukan mataki ko kuma hukuntawa a gareta. Saidai kuma ta wani fannin ta qarfin tuwo yake danne zuciyar tasa,tare da sake gayawa kansa wacece sultana a garesa,sultanan nafissa ce,sultanan kamar d'iya take a wajensa. "Wuce cikin gida tun ban tattakaki a wajen nan ba" ya fada a mugun tsawace. Har tsakiyar kwanyarta taji sautin qaqqarfar husky voice din nasa dake cakude da fushi,fushin da zuwa yanzu ta shiga sahun jerin mutanen da suka sakan qarfinsa da kuma illarsa. A nutse kuma a hankali ta juya zuciyarta na wani irin raurawa. Kuka takesonyi na yadda ya bada ita gaban friends dinta,amma dakakkiyar zuciyarta na gaya mata "Akul kada ki fara,kada ki yarda yaga lagonki kamar yadda yaga lagon su lamira" Da idanu ya rakata daga nan inda yake tsaye yana hadiyar bacin ranta,tabbas inda yasan tafiyarsa da kuma yin nesansa da gida haka zata sake tabarbara al'amuran sultana....... haka zata sake maida sultana......haka komai zai sauya da ya haqura da tafiyar,da ya nemi afuwa daga wajen aba,yaci gaba da roqarsa ya barshi yaci gaba da lallaba karatunshi a haka. Sai data fara nisa sannan ya ankare da shigar dake jikinta,shigar qananun kaya trouser da shirt inner da top. Sosai kayan suka zauna mata a jikinta wanda yake a murje tsaf.....zallar hutu da kwanciyar hankali sun bayyana muraran a tattare da ita,ko ina nata ya soma cikowa alamun da hasken gaske dai girma ne yake cuso kai cikin qananun shekarunta da duka duka basu haura sha biyu ba. Duk yadda yaso ya daure don kada sanya baki akan lamuranta su yawaita amma ya kasa,saboda shiga ce da ya haramtata baki daya cikij gidan,ba kuma yanzun abun ya faro ba,tun zamanin da nafissa kawai ke rayuwa cikin gidan a matsayin diya mace,har kawo yanzun da diyoyi matan cikin gidan suka sake yawaita. Sake quluwa tayi ta cika fam sanda taji yana qwala mata kira sunan "Ke!" Sunan da duk duniya tafi tsanar ka kirata dashi. Bai umarci tazo ba,da kansa yake takowa inda take tsayen. Sai ta samu zuciyarta da bugawa cikin tsananin tsoron wanne laifin kuma tayi?,saidai kuma taurin kanta da zuciyar nan tata maras tsoro na sake qarfafar dukka gabbanta akan bata aikata masa laifin komai ba. "Sau nawa zan gaya miki na hanaku irin wannan shigar?,ina atamfofin da AMA ta raba muku?" Yayi mata tambayar yana tsareta da lion eyes dinsa da a yau suke cike da fushi. Baki takeso murguda masa ko ta maida masa amsa me ciwo,don dai ita zuwa yanzu tuni ta cireshi daga sahun mutanen da take jin nauyinsu take kuma ganin kima martaba da darajarsu "Ni ban iya sakasu ba,kuma ma zafi garesu" "Kalleni nan" ya fada cikin zallar tsare gida. Kasa duban idanun nasa tayi,duk kuwa da yadda takejin a yanzun bawai kallon idanunsa ba,har zagi tanajin zai iya fita a bakinta a yadda takejin ya matse rayuwarta haka da yawa. "duk ranar da na sake ganinki da wadannan kayan ki tabbatar saikin raina kanki,abu na biyu muddin na sake ganin qafafun wadannan cikin gidan nan a tare dake......basai na gaya miki abinda zanyi ba,bacemin a gun" ya fada a kausashe kuma a tsawace. Wani irin fushi da tarin haushinsa takeji kamar tayi me?. Me zatayi masa ne ta huce wannan abun da yayi mata?,me zatayi masa ta rama?,kawai sai ta bude zazzaqar muryarta ta fara jera waqoqinta hankali kwance tana wucewa zuwa sashen bibi _Bamu damu da kowa ba kar wanda ya damemu......baka bani ban baka to hushin na menene?,ashe zaman duniya iyawa ne_ Da mugun sassarfa ta soma tafiya me hade da gudu da kuma sauri,saboda ta tabbatar abinda tayi din babu wani makawa da zai hanata karbar hukunci mafi muni daga hannunsa. Cikin kunnen nasa dukka baitocin waqoqinta suka sauka. Wani irin mamaki ne ya kasheshi,zuciyarsa tayi wani mugun yunquro masa,har a cikin ransa yakejin yau din dole ya ajjiye duk wani dubayya da yakeyi ya hukuntata yadda ya kamata. Kusan lokaci guda suka isa parlor din bibi. Daidai lokacin da take zaune saman daya daga cikin qawatattun kujerun turkey da suka sake daga darajar parlor din har set biyu mabanbantan kaloli da suka dace da juna. Hannunta na dauke da tasbaha da bata rabo da ita tana ja,musamman lokutan da take ita daya irin wannan,yayin da rabin hankalinta yake kan tv france dake gudanar da wani shiri dake nuna ainihin zallar al'adun gargajiya na qasar nijer din. Lallausar rigar wani farin zaren ulu ne a jikinta,wanda yake da adon ja jefi jefi,budaddiyar rigar ta asalin saqar qabilar abzinawa. Tun daga yanayin jikinta zuwa suturarta zaka fahimci sukunin rayuwar da take ciki da kuma zallar kulawa da take samu. Bata kawo shigowar kowa a cikinsu ba a lokacin,don haka a dan firgice ta daga idanunta tana saukesu daga bakin glass door din parlor din nata. Tun kafin ta gama rarrabe tunaninta akan abinda ke faruwa sultana din ta fado,kafin takai ga dauke idanunta a kanta ko kwanyarta ta warware mata komai maina ya biyo bayanta. Taku daya tak ya sakeyi ya cimmata,wanda duka duka tazararsa shi da ita da kuma bibi din baikai taku biyu ba. "Kul maina!,menene haka?" Muryar bibi ta dakatar dashi daga saukewa sultana zaratan hannayensa da yayi niyyar yi saman farar fuskarta. A hankali ta sauke kallonta daga kan dogayen yatsun mainan ta maida kan fuskarsa "Zauna maina" Ta fada cikin wani irin mode dake nuna tsoro da fargabar da suka cika zuciyarta. Ji yayi sam bazai iya zama din ba,sai ya sauke hannayensa ya xubesu zuwa cikin aljihunsa,ranshi a mugun bace yana jin yadda jijiyoyin jikinsa ke harbawa saboda tsananin bacin rai. Bibin ta sani,koda ta tambayeshi ba'asi a yadda fushinsa ya hau zuwa matakin da tasan ya kusa kaiwa qarshe,koda zata dige tana tambayar nasa ba zaya ce komai ba,don haka ta waiwaya ga sultana data dade da yin garkuwa da bayanta,ta dunqule ta kuma cure a bayan nata,manyan idanunta na runtse gam,abinda ke bayyana ainihin asalin tsoronta "Me kikayi kuma sultana?" Tambayar da bibi ta jefo mata ya bata tabbacin ta samu tsira daga hukuncin ya maina din,wannan din ya sassauta tsoratarta da kuma fargabarta,ta zame ta zauna sosai tana kallon bibi kamar ba itace ke boye a bayanta da razananniyar fuska ba "Nima bansan abinda nayi masa ba bibi,hakanan kawai ya biyoni zai bigeni" kyawawan idanunsa ya hada ya lumshesu guri daya yana furzar da iska daga bakinsa. Wani baci ransa yake sakeyi,bayan zallar rashin kunya harda qarya?,abar da yafi tsana kayi masa? Yana daya daga cikin abinda yasa wasu ke masa kallon tsatstsaura,saboda shi din yana cikin jerin sahun mutanen da kwata kwata basu iya qarya ba. Kome dacin abu,komai girman abu idan zasu fada zasu fadi maka ne kansu tsaye kuma
Chapter 10 · 0% Book details