Sashe 26
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mahaifiyarta ba ta nesanta tsakanin maina da mahaifiyartata?,ta hana UWA yanzu kuma 'YA zata maye wannan gurbin na UWAR?,ta yaya hakan zata faru?. Wadannan dama tarin wasu tambayoyin su ta dinga yiwa kanta ita qwallin qwal cikin dakinta. Batasan da waye zata tattauna wannan maganar me uban nauyi da tarin sarqaqiya ba,abun tana jinsa kamar a cikin mafarki ne kawai bawai a gaske ba,SULTANA?,MAINA?,to waye ya qulla?,......amsar dai daya ce,ta tabbatar bibi ce,da basu cimma nasara ba wancan karon shine a yanxun suka shammaceta?. Gwara nafessa sau malala gashin tinkiya NAFESSA tafi sultana nagarta nesa ba kusa ba,sultana din ALBASA CE wadda sam batayi halin ruwa ba,nafessa bata da wani aibu gabanta da bayan halayenta kaf,banda wani dalili guda biyu rak,bataga abun gufu ga nafessa ba,amma kuma sultana fa?,aibubbuka da abubuwan gudu gasunam birjik basu da iyaka "Karki matsantawa kanki da yawa,ina kikaga hadi tsakanin maina da sultana?,ko hankali ya bada haka?,barsu suyi iyakar iyawarsu,idan suka sheqa suka samu babu qwaya zasu warware da kansu" hajiya dezatou tace da ita. Daren gaba daya bata samu wani isashen bacci ba. Da safe da maina ya shigo suna breakfast kallonsa kawai takeyi tasan baisan abinda ke shirin faruwa cikin gidan ba,amma taji aba din yace idan ya kammala ya sameshi a baya ta gurin swimming na gidan,ta tabbatar zancan zaiyi masa. *_TOFA MASU KARATU,AKWAI TARIN TURKA TURKA CIKIN LABARINNAN_* "_akwai BAZATA masu yawan gaske_* *_inason na jaku zuwa wata kyakkyawar gaba da zata zame mana tamkar tsani ko shimfida na labarin da zamu samu bigire me kyau bayan sallah da zamu dora_* *_SHIN MAINA ZAI YARDA?_* "_SULTANA FA?_* *_IDAN HAR HAKAN YA YIWU ME ZAI BIYO BAYA?_* *_AKWAI WATA MURDADDIYAR QADDARA CIKIN LABARIN,WADDA KE ZAMOWA TAMKAR WATA GUGUWA DAKE WAJIGA ZUKATANSU DA ZUKATAN MUTANE DA DAMA_* *_AKWAI TARIN KUKA/NADAMA/SADAUKARWA/BA ZATA DA QARFIN DA QADDARA KE DA ITA CIKIN RAYUWAR KOWANNE BAWA_* _INA SAKA RAN GOBE NA BAKU SHAFUKAN DA ZASU ZAME MANA MURFI NA LABARIN IN SHA ALLAH,MURFIN DA ZAI RUFEMU HAR ZUWA BAYAN WATAN AZUMI_ HUGUMA CE *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* Page 27 Kamar yadda aba ya buqata,maina bai gusa daga gidan ba har sai da ya sameshi cikin balcony dinsa dake bada kyakkyawar iska tatacciya. Yana tsaye sanye da kaftan abaya me sulbi wadda yadinta ke fadin irin kudi da tsadarta. Hannunsa duke da daya daga cikin jaridun qasar nijer din yana dubawa ta cikin eye glasses din da ya yiwa kyakkyawar fuskarsa kyau,fuskar da har yanzu kyanta bai gushe ba,kyawun kuma dake bayyana adadin sharafin samartakar da aka sha a shekarun quruciya. "Zauna maina" ya fadi yana daga tsayen ba tare da ya zauna ba yana nuna masa kujera. Komawa yayi da baya ya zauna,yayin da aba ya ajjiye jaridar hannun nasa saman wani dan table,ya kuma goye hannayensa a qirjinsa yana duban idanun maina "Kasan me yasa na kiraka?" Kai ya girgiza a hankali,sai aba ya saki hannayensa yana gyara tsaiwarsa "Ranar juma'ar nan me zuwa zan daura maka aure kai da sultana,nace bari na baka labari kafin kaji a wani guri gwara kaji a bakina........don banason duk wani bore ko wani motsi na rashin amincewa,to kawai nake da buqatar ji daga bakinka" yakai qarshen zancansa yana qoqarin bude ruwan gora don yasha. Wani yarrrr maina yaji tun daga saman kansa har yatsun qafarsa "Sultana 'yata aba?" Ya jefa masa tambayar cikin wata murya me cike da sanyi "Yar nafessa dai da mamuda ko?" Ya maida masa amsa kai tsaye,sai kawai maina din ya sadda kansa qasa. Bayajin komai akan hakan,shi kawai abunne yaji ya masa banbarakwai. Dukka shirin bibi ne wannan ya tabbatar,saboda ya gama karantar takunta fes,wai ita a lallai tsoronsa take kada ya bata mata jika. Tuna hakan da yayi ya kusa sanya dariya ma subuce masa,wannan auren ai kawai wahal da kansu su aba zasuyi,baiga ma abun tada jijiyar wuya ko daga hankali ba,ya fahimci auren fakewa ko auren jingina bibi keso ayi saboda tsabar bata sadaki da batawa mutane lokaci,shi da zai wuce makaranta ma ranar alhamis kuma sai an sake ganinsa?. Wannan tunanin ya sanyashi miqewa yana fadin "Allah ya sanya alkhairi" kawai a gajarce. Da ameen aba ya bishi,dama baya sanya ran maina din zai wani kawo matsala me yawa,ta inda ya zaci ma zai iya taurarewa saboda sabanin fahimtar da ya shiga tsakaninsa da yarinyar da qaqqarfar rashin jituwa. Yana saukowa ama na tararsa,tun daga qafar bene na qarshe "Me yace maka?,kaji abinda ya ballo kuma?" Tayi maganar fuskarta kwance da muguwar damuwa da rudani. Hannunta dukka biyun ya kama a nutse ya isa da ita saman kujeru ya zaunar da ita "Zauna don Allah ama ki daina damun kanki,wannan wani game ne kawai da bibi ta shiryashi,kada ki daukeshi wani abu me muhimmanci don Allah,ranar alhamis ma ni zan koma makaranta" ganin bai daukaki al'amarin ba shima sai taji hankalinta yadan kwanta,ta sakawa ranta salama kadan,saidai kuma abun yana damunta qasan zuciya. Wai a rasa kaf gidan da waye za'a masa wannan gantalallen daurin auren sai sultananan?,yarinyar da ta gallabi kowa?,ko su kuwa basa iya controlling nata?. Saita ajiye doguwar ajiyar zuciya tana mamakin yadda suka dauko al'amarin da bazasu iya warwareshi ba,don ko ita ina bata hango wata mafita ba sai sake dagula komai. Shirin komawa makaranta abinsa yaci gaba dayi hankalinsa kwance,don shi a wajensa wannan abun dai dai yake da buga wasanni,koma meye suka shirya oho,shidai ko meye ma a yanzun baida lokacinsa bashi kuma da plan dinsa sam sam. Sultana kam sanda bibi ke gaya mata wai za'a daura mata aure da maina ranar juma'a maida bibi tayi kaman wata nini dinta da take wasa da ita,ta dinga qyalqyala dariya harda buga qafa,su aminata dake zaune da yasmine sai suka fita hankali ma,su kansu kallonta suke saboda yadda ta maida lamarin wani abun wasa "Nice matar maina" ta fadi tana wani lanqwashe murya,sai kuma ta saka dariya "Allah ya sawwaqe,tabdijan,ni kuwa me zanyi da wannan mutumin?,dan iskan me cewa zaiyiwa mutane fyade?" Duka bibi ta kaiwa bakin sultana,ta tsani jin wannan kalmar daga bakinta,tadan sameta kuwa amma baiyi yawan da za'a zuzutashi ba,ai kuwa ta bare baki ta saki kuka "Na sake jin kin furta wannna kalmar a bakinki fasa bakin zanyi sosai,ba irin wannan shafar mai ba". Kuka tuburan ta zauna tana ma bibi,tun bibi din na shareta har kukan ya fara damunta,tanja tayi lallashi tayi lallashi har ta gaji,sai suka fahimci mafaka take nema saboda dama ranar Monday za'a karbo result na exams dinsu,tanja ta gama fahimtar kome,batayi abun arziqi bane shi yasa takeson ta fake da wannan. A dole bayan bibin ta gama shareta kuma ta dawo tana lallashinta. Suna tsaka da wannan ya shigo rataye da jakarsa a baya wadda take set ce da luggage dinsa. Sultana ce ta fara barin falon da gudu gudunta ta wuce ciki bata ko waiwayi inda yake ba. Sai a yau ya sake fahimtar abinda yarinyar takeyi "Saina koya miki hankali "ya fada qasan ransa,saboda mugun haushi abun ya bashi,dukka su aminata suna wajen,waye ta gani ya firgita haka ko ya gudu?,sai ita?. Bibi din ya yiwa sallama kamar ko yaushe "A sauka lafiya" ta amsa masa da shi tana binsa da kallo sanda suke fita shida goumar,baki ta tabe tana jinjina kai "Miskili kafi mahaukaci ban haushi" ta fadi a fili qasa qasa,har yanzun bai nuna mata komai ba akan batun daura auren,so ko qi duk bata fahimci komai ba. To koma meye can ta matse masa,itadai da wata barnar gwara wata,hankalinta zaifi kwanciya idan sultana ta amsa sunan matarsa,ko mene zai biyo baya kuma me sauqi ne. Kamar yadda suka qudurta a ranar juma'a din aka daura auren SULTANA MAHMOUD MAYAK'I da angon ALIYYU MUHAMMAT MAYAK'I. Daurin auren da yayi matuqar daurewa dangi kai,saboda muguwar ba zata da ya yiwa kowa. "Maina din da ya raini sultana?,ya zame mata kamar uba ko wani shaqiqin yaya?,ashe shi zai aure kayarsa? Maganganun da suka dinga yawo kenan. "Ina almurin,ashe kansa ya yiwa kiwo" wata qanwar bibi ta fadi sanda ta iso gidan. Itadai bibi murmushi kawai tayi,domin kuwa ita kadai tasan dalilin da yasa hakan ta kasance,kuma ita daya take tunanin me gobe zata haifar?,ya zata kasance musu dukkansu a gaba?. Ga sultana kuwa a ranar ma suna sharafinsu ta sulale tayi ficewarta gurin rawar taron sunan maman qawarta da akeyi. Ranar ta jijjigi rawa yadda ranta keso,sai daga bisani wata maqociyarsu da taje taron sunan ta kamota ta jata gefe tana tsareta da ido "Halan bibi batasan kin fito ba?" "Eh suna can suna taro" ta bata amsa cikin halin ko in kula. Kai sosai fattu ta girgiza,batasan wacce irin zallar wauta ke damun sultanan ba "Kinsan me ake nufi da aure kuwa sultana?,zauna dai tukunna" fattu ta fadi tana gyara mata wajen zama. Bata musa ba ta zauna saboda dama ta gaji sosai saboda rawar da tasha. Ba abinda ta boye mata,ta warware mata komai game da abinda ake nufi da aure. Mugun baci ranta taji yayi,wato abinda bibi ke nufi kenan?,dama tasan abinda ake nufi din tace a aure mata maina din dan iska?,sun bashi damar yayi mata fyaden kenan,yama kasheta a cikin gidan kenan tunda daga yau yafi kowa da kowa dake cikin gidan iko da ita,to ita kuwa daga yau su zuba da yaa maina din,zai gani idan zai juyata yadda yakeso yake kuma buri. Driver dinta fattu ta sanya ya maidata gidan,bata qi ta fattu ba don ranta a bace yake,hakanan kuma jikinta a sanyaye yake,ta dinga juya maganganun da fattu tayi mata a ranta sanda suke hanyar komawa gida "Tabdijan" ta dinga maimaitawa lokaci lokaci tana gyada kai. Ita za'a yiwa irin wannan abun?,taga yadda hakan zai faru kuwa ita. Sanda ta koma cikin gidan ba wanda ta kula,ta wurwuce abinta har zuwa quryar dakinta ta kulle ta shiga hidimar data dameta. Ko bayan an watse fushi ta shiga yi da bibi,kusan kwana uku bata shiga sabgar bibi,saboda tana ganin ai an hada baki da ita ne za'a cuceta kawai. Saida bibi ta gaji da halin nunqufurcinta sannan ta isketa a daki ranar. Vest ne a jikinta da wandonsa iya cinya tanata game abinta,ta zare ribbon din kanta taqi ta hade sumarta waje daya,taqi kuma yarda tanja ta taje mata a gyara. "Ke me