← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 30

Sashe 13

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

qafafunshi dake saman table qasa yana ajjiye wayarsa saman kujerar ya wuce zuwa bedroom dinsa. Kaftan abaya budaddiya ya zura navy blue,kalar data fidda sigar kyawunsa matuqa,haskensa ya fito sosai,ainihin zallar hasken cikakken ba'abzine. Kamar yadda yake dabi'arsa hannayensa zube a aljihun kaftan abaya din yana qissima abubuwa da dama cikin ranshi. Iskar bayan azahar tana kadawa kadan kadan me cakude da sanyi maras tasiri. Ire iren wannan yanayin suna masa dadi sosai kasancewarsa mutum ras son zafi ko kadan. Hatta da sutura ba kowacce yake sanyawa ba saboda baison abinda zai takura jikinsa. Da nutsatstiyar sallamarsa ya shiga parlor din bibi. Ta amsa masa tana karantar nazarinsa sanda yake basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba,daya daga cikin alamun fushinsa kenan. "Samu waje ka zauna" bibi ta bashi umarni kai tsaye,ita dinma yau fuskarta ba'a sake take kamar yadda ta saba ba. Kaman bazai zauna din ba sai kuma ya matsa sofa din gefanta ya zauna a kai bayan dukka wadanda ke zirga zirga a falon sun kau,don basu waje. "Aliyyu" bibi ta kirashi da sunansa na asali kai tsaye. Sexy eyes dinsa ya daga ya kalli Bibi sannan ya motsa bakinsa "Kada kace komai maina,mamaki kurum yanzu kake bani" ta fadi tana qare masa kallo tamkar tanason hange meye abinda ya canza a tattare dashi da ya sauya launin mu'amalarsa da sultanan tashi "Gaba daya ka canza maina,kamar ba kai ba,ka tashi daga mainan sultana ka koma aliyyu haidar,ka tashi daga fr ren sulty ka koma wani abu na daban,kana neman zamewa yarinya kamar wani dodo,kamar ba kaine ka raineta da hannunka ba?,kamar ba kaine kaci kashi da fitsarinta ba?,kamar ba kaine kake hana idanunka bacci saboda sultana na kuka ko tana rigima ko bata da lafiya ba,dukka ina wannan kulawar?,tsakaninka da ita yanzu sai kyara sai hantara sai tsangwama,sama da tsangwamar da kakewa kowa cikin gidan nan" bibi ta qarashe fada tana sauke maganganun nata hade da fitar sirrin numfashi,da alama daga qasan zuciyarta maganganun suke fita "Me yasa bibi?" Ya jefa mata tambayar,idanunta kadan ta qanqance tana dubansa alamun neman ba'asin tambayar da yayi matan "Me yasa bibi zaku barta ta sangarce bayan kowa cikin gidan nan tarbiyya bai daya ake musu,waye tafi cikin yaran gidan nan bibi?,sai abinda sultana ke so?,sai abinda ya kwanta mata a rai yayi kuma dai dai da raayinta?,bibi wannan ba soyayya bace sam ba qauna bace,ita din diya macace,gidan wani zataje,baki tsoron ta tashi a haka taje masa da dabi'ar da bazai iya ba a dawo muku gida da ita?,wala'alla ni din bana kusa da ku,kune zaku fini jin ciwon hakan,kuma kafin ni na gani ku zaku fara gani kune zaku fara karbar sakamakon" "Auzubillah......haidar me kake cewa haka?" Bibi ta fada fuskarta na nuna girman da zancan yayi mata. Ba komai saman fuskarsa kaman ma baisan me dame ya cewa bibin ba ya dage dukka girarshi biyu "Oui(yes)" "Dukka maza ne zasu iya daukan halin banzanta?" "Subhanallahi,da gaske ka sauya maina,ka canza,na tabbatar fr ren sultana bazai taba fadin haka a kanta ba......to bari kaji,kai din yaro ne da har yanzu bai wuce shekara ashirin da biyar zuwa da shida ba,a dukka matakan tarbiyya banjin kasan wani abu me yawa,bata haka ake yiwa yaro tarbiyya ba,tsanani da matsi basa kintsa yaro ko kadan,ka sanyawa sultana zafi da yawa,kana amfani da irin zafinka na halitta,ita diya mace kwata kwata bata buqatar zafafawar namiji,bare kuma yaran mata da yanzun suke tasawa tarbiyyarsu nada matuqar sulbi da santsi,don Allah maina.....banajin dadin canzawarka kwata kwata,ka koma fr re din sultanansa na baya". Idanunsa ya lumshe sannan kuma ya budesu, muryarsa a lanqwashe yace "Bibi na fiki jin rashin dadin dabi'un sultana,na kuma taras da ku ba masu goyon baya na ba wajen maidata hanya,bazan canza ba indai sultana ba zata canza ba,dole ta koma kamar kowanne yaro dake gidan nan" kai bibi ta gyada,tun ba yau ba tasan irin nasa halin. Yana da tarin kafiya da taurin kai akan dukkan abinda ya sanya a gaba ko ya furta zai aikata. Fadin zaiyi abu yana da wuyar ji daga bakinsa,amma muddin ya furta din to babu sauyi,komai dadi komai wuya. Sake gyara goyon school bag dinta tayi dake bayanta,tana jin kamar ta fada dakin ta rufe yaa maina da duka,ai ita batasan haka yayi nisa wajen qinta ba,batasan haka zuciyarsa tayi zurfi wajen son quntata mata ba,lallai Allah baya bacci da har kunnuwanta suka jiye mata komai. Indai yana tunanin iya tsare gidansa,daci da baqin ransa,fada da hararraminsa zai bashi abinda yakeson yaga ta koma din to tabbas zata tabbatar masa ita din ba tsoronsa takeyi ba,kuma bai isa tabuka komai ba "Sultana kibi a hankali,kinfi kowa sanin waye fr re" wani sashe na zuciyarta ya gaya mata sanda take qissima da irin salon da zata shiga falon "Idan garwashi ne shi ni wuta ce" ta baiwa kanta da kanta dama zuciyar dake gargadinta amsa,bata kuma sake tsayawa sauraron kowacce shawara daga zuciyarta ba ta sanya kai falon da waqar data zame mata madadin sallama. Idanunta saman fuskarsa tana nazarin furucinsa daya bayan daya,dai dai sanda siririyar muryarta dake cike da tsiwa ta isa ga kunnuwansu tana rera waqar ado isa gwanja _Allah ka aika munafukinmu qarshen nesa,tafiyar qasa koda lafiya ko babu,kaishi garin da ko kuyanga babu,barshi a can da arziqi ko babu,ni nasha tabara nasha yasin,kuma nasha rigakafin alatsine_ . Sai ta juya zuwa waqar wani mawaqin qasarsu ta nijer _Munafuki Alla kasheshi,koda safe koda rana ko ma dare ne_ Tana maganar ne kanta yana kallon lobby na dakunansu tana kuma nufar can,tamkar batasan da zaman mutane a wajen ba. Mutuwar zaune bibi tayi,ana kukan targade ga karaya ta samu,ana neman gyara ga sabon ruwa ya ballo. Ko waye kai,komai girmanka muddin ba iyayensa ba baka isa ka ratsa waje bakayi masa sallama ba,kamar yadda duk yadda yake da buqatar shiga guri muddin ba'a amsa sallamarsa a n kuma masa izini ba yana juyawa ne ya koma inda ya fito. Wannan ya samu asali ne daga cikakken karatu da tarbiyyar daya samu daga islamic school din da yayi masu kyau a Nigeria. Har ta kusa shigewa ya kirayeta cikin tsawa,kaman ta wuce ciki sai narkakken tsoronsa dinnan da take qoqarin binnewa ya motsa mata. Tunga taja ta tsaya kana ta waiwayo tana dubansu ba tare data iso inda suke ba "Koma ki yima mutane sallama" idanunta masu kama da digon zaiba ta dan juya tana bata fuskarta,ta motsa qaramin bakinta dake cike da tsiwa tace "Nifa na riga nayi sallamata ehe" daga wannan ta juya tana shirin wucewa dakin tare da sake maimato waqoqinta a sarari sosai saboda saqon ya isa gareshi. Wata baqar zuciya ce ta motsa masa,tabbas sultana dashi take,shi takewa wadannan waqoqin. Uwa uba yau shine zaiyi mata magana tasa qafa ta shure?,tama maidashi mahaukaci?. Daga sultana har bibi babu wanda yasan lokacin da ya isa dakin. Dai dai sanda take wurgi da komai na makarantarta kamar yadda ta saba tana sake sakin waqoqinta cikin harshen faransanci,ranta fes tana jin ta fara samun nasarar rage haushinsa cikin ranta. Cire hijabinta yayi daidai da dauketa da marin da yayi,babban dukansa shine marin,bai iya wani duka ba idan ransa ya baci bayan shi. Sanin darajar da fuska take da shi ya sanya bai cika yin dukan ba,zaiyi wuya kaga ya daki wani cikin qannensa,amma wajen iya bada horo su kansu sun tabbatar babu na biyunshi kaf cikin family. Wata irin gigitacciyar qara ta saki tana dafe kuncinta da hannayenta bibbiyu ba tare data fuskanci meye ya sameta ba. Sautin muryarsa saman kanta kwanyarta tayi saurin ingizo mata me yake faruwa da ita,saidai kafin ta gama daidaita tunaninta ya sake aje mata wani Marin hade da qatotuwar tambayar da batasan da wanne zataji ba,marin ko amsa masa tambayarsa "Saikin gayamin wanene munafukin cikin gidan nan" yayi maganar yana zare belt din dake jikinsa. Dukka jikinta rawa ya fara yi,saboda ganin fushi muraran saman fuskarsa,uwa uba tunda take bazatace ga ranar da aka sanya madoki aka daketa ba,shine ma mutum na farko kaf fadin rayuwarta da ya taba taba lafiyarta tunda tazo duniya,wannan ya sanya take matuqar razana duk sa'ilin da ya shimfide mata dogayen yatsunsa saman fuskarta "Waye munafukin nace?!" Ya maimaita tambayarsa yana ware mata lion eyes dinsa da suka sake gigitata,sai ta ware dukka muryarta tana qwalawa bibi da tanja kira "Wayyo Allah na bibi,zai kasheni,zai kasheni,wayyo na shiga uku" Yatsansa ya dora saman lips dinsa yana sake fidda mata idanunsa dake danqare da bacin rai "Kika sake buda bakinki a nan sai na miki dukan da ba zaki qara iya daga yatsarki ba,tais toi idiot(shut up idiot)!" Ya qarasa fadi a tsawace. Dole qanwar naqi ta sakaya ihunta,duk da tana jiyo bibi na bugun qofar hadi da kiran sunanshi da bashi umarnin ya bude,saidai kuma bata da ikon cewa komai. Stool dinta ya jawo ya zauna a gabanta,ta qanqame jikinta guri daya tamkar me jin sanyi. Ba sanyi takeji ba,tsantsar tsoro ne ya sanya jikinta ke shivering,amma batason yaga hakan daga gareta,hawaye kwance saman fuskarta,ilahirin fuskar tata radadi take mata "A fr re dinki kika sanni ko?,to daga yau ki saka a ranki maina nake a wajenki kamar yadda nake a wajen kowa na gidan nan,zan fiddo miki ainihin kalata tunda na fuskanci kin zama graduate a fannin rashin kunya *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 14 "Dago kanki ki kalleni!" Ya gaya mata da wata a tsawace "Baki isa kifi qarfin kowa a gidan nan ba,idan ma kinfi qarfin nasu ne ni bakifi qarfina ba,zan iya tattakaki nayi miki dukan da ba'a taba yi miki irinsa ba kuma babu abinda zai faru,daga yau zan kafa miki dokokin da idan kika tsallake guda daya a cikinsu ki tabbatar da kin shiga uku" ya fada yana murza yatsunsa. Idanunta ta runtse tana jin sautin yatsun nasa,wani sabon hawayen ya balle mata,yau ita ya maina yake yiwa haka?,ita ya sanya a gaba yake yiwa wannaj tijarar?,ita ya yiwa irin wannan titsiyen da babu mahalukin da ya taba yi mata irinsa?. Kimanin minti talatin yana gindaya mata sharudda da qa'idoji,sultana din tana zaune a gabansa ba tare data motsa ko ta furta komai ba. Duka maganganunsa basuyi tasirin komai a ranta ba face wani mugun qulli data yi masa,haushi
Chapter 13 · 0% Book details