← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 30

Sashe 28

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***Wani irin jiki ne da ita wanda baya qaunar zafi ko kadan,wannan ya sanya take da vest da wandunansu masu yawa da takan sanyasu koda kuwa bawai zafi akeyi a garin ba. A hakanma bibi din ta kwashe wasu ta bayar saboda ta fara girma baici ace tana ci gaba da sanyasu ba. Su hudu ne a falon,bibi din,deeja mai aikin bibi,tanja sai sultana din da tanja ta kama kan nata take gyarawa. Ana gyaran kan tana qorafi don ita sam bata son a taba mata suma. Yatsuntsa guda goman duka lalle ne aka saka mata. Idan akwai abinda takeso cikin ado kaf to jan lalle ne,shi dinma kuma bawai tana iya zama bane ayi mata qafa da hannu ba,saidai ayi mata iya yatsun qafa ko iya yatsun hannun. Sallamarsa cikin falon goye da qatuwar jakar 'yan makaranta ta tsaida numfashi na daqiqu daga jikin sultana,sannan tayi wani tsallen albarka tana miqewa,da sauri tanja ta riqota amma tuni ta zille,lallen kuma dake hannunta ya sabule yayi nasa guri,bata kuma tsaya ba ako ina sai daki. Dukkansu suka bita da kallo har ta qule cikin dakin. Wani abu ya hadiye yana qarasowa cikin falon. Karon farko da ranshi ya baci akan abinda takeyi din idan ta ganshi,ya karanci abun nata harda iskanci da iya shege,banda hakan daga sallama kamar wadda taga mala'ikan daukan rai. Bayan sun gaisa su tanja miqewa sukayi suka basu guri kamar ko yaushe. A yau din bibi ta sakar masa sosai kamar yadda suke a baya,har abun yadan bashi mamaki "Sai yau aka tuna damu?" Ta fada tana 'yar dariya "Sai yau akaga damar sakarmin fuska?" Ya fadi yana dage mata girarsa guda daya fuska a dinke tsaf. 'yar dariya tayi tana watsa masa daquwa "Ungonan ja'iri, gidanku" "Oho......ni gaskiya kenan na fada ai" ya fadi yana samun gurin zama sosai. Ya kusa awa guda gurin bibi din suna hira,amma ko motsin sultana bai sake ji ba har ya fita a sassan. Ya samu ama da baqi wajen mutum hudu,kuma dukkansu dangin aba ne,don haka daga tsaye suka gaisa ya juya zai wuce sashensa,saboda yau din a mugun gajiye yake,yanason kuma yadan fita bayan ya huta "Bikin ni'imatu akeyi fa aliyyu" ama ta fadi tana dan murmushi saboda tunawa da tayi da irin drama din da akayi akan ni'imatu din da maina. Tayi mutuwar sonshi kamar ba gobe,shi kuma yayi matuqar qin jininta,haka nan tun suna qananu. Yana da wani irin hali, zuciyarsa me girma ce ba kasafai soyayyar wata ke burgeshi ba. "Allah ya sanya alkhairi" ya furta a taqaice yana gyara maballin wuyan rigarsa da hannu daya "Zaka fito ne yanzu?" Ama ta sake tambayarsa "Eh to,bacci ne a idona da yawa,wai da inason nadan kwanta" "To qilan kafin ka tashi ka samu gidan ba kowa,don dukka zamu gurin kamun amarya" "Okay,sai kun dawo,amma zan dauki key daya na mota da ita zan fita" sai ya qarasa yana daukan key din da ya gani saman table yana ficewa. Yana yin wankan kuwa baccin yayi awon gaba da shi,bai farka ba sai bayan sallar la'asar,har sallar taso kubce masa. A gurguje ya daura alwala ya fice masallaci. Sanda zai dawo din yaga sun fara shirin fita,don masu mota a cikinsu sun fidda motocinsu daga parking space. Ya samu ama ta bada abinci a kawo masa,amma sai baici ba,ya duba lokaci,ya tabbatar idan yakai dare wajen masu mishi gyaran gashi zaya samu layi sosai,don haka kawai yahau shiri da zummar idan ya dawo yaci abincin. Cikin wani red shirt me gajeran hannu ya shirya,yayi kyau ainun,hakanan gashin da ake cewar za'a je gyaranshi ba wani alamun buqatar gyara sam a tattare dashi. Nannadaddiyar sumar nan me santsi irin ta asalin abzinawa buzaye. Wani boot ya sanyawa qafarsa,gwanin saka boot ne sosai ko don saboda kyakkyawar alaqar dake tsakanin aikinsu da takalmin?. A dan gaggauce ya fito,mutanen gidan har sun fara fitowa,sai ya wuce abinsa kai tsaye yana duban key din motar da ya dauko yana nufar motar. Ita daya qwallin qwal shigarta ta banbanta da dukka shigar sauran 'yan uwanta,cikin high tummy plazo me rawa take da wata riga mahadinsa me gajeran hannu. Wando ne me azabar kyau da tsada wanda ta hadashi da wani high Hill shoe me madauri wanda yake mahadin qanqanuwar handbag din data saqale cikin yatsunts. Wasu irin fashion earrings ta sakawa kunnenta,wanda bai zuwa da sarqa saidai abun hannu da agogo da kuma zobe. Gashintannan me azabar tsaho da santsi an masa wani gyara na musamman,wani ya duba gaban fuskarta yabi ta gefen kunnnenta,ta hade da sauran na bayan ta matseshi cikin band me kyau da qyalli. Kallon daya idan kayi mata zaka iya rantsewa da Allah daya daga cikin diyoyin celebrities na qasar india ne,don muddin ba baki ta bude tayi maka magana ba,zaka kafe ne da cewa ko zo na kasheki bata sani da kowanne yare ba idan na indiyanci ko larabci ba,don sakkk kamanninta suka alamta hakan. Ba waje ba,iya cikin farfajiyar gidan kadai da ta tako dai data dauki hankalin kowa. Dai dai kuma sanda maina ke fiddo motar daga cikin jerin sahun motocin yana duba bayansa ta cikin madubin motar don ya fita da kyau ba tare daya taba kowacce mota ba idonsa ya sauka a kanta. Dukkansu najma kowacce doguwar rigar atamfa ne gown a jikinta,harda siraran mayafansu,to amma sultanar ko hula bai samu arziqin sanyawa ba bare aje ga batun mayafi. Har yaja motar gaba kadan yana dauke idanunsa daga kanta wani abu daya darsu a zuciyarsa ya sanya ya tsaida motar "Idan a baya baka da right,yanzu kana da cikakken damar da zaka hukuntata ka kuma bata kowanne kalar umarni da kakeso,babu me cewa don me,wannan abun da sukayi sun baka cikakkiyar dama ne a hannunka da zaka saitata yadda ranka keso ba tare da sunsan da haka ba" ya gamsu qwarai da wannan maganar,sai ya sanya hannu ya danne horn din motar tashi. Dukkansu aminata dasu yasmine dake tsaye hankalinsu yayo gurin harda sultanar,amma sai sultanan ta dauke kanta. Hannu yasa ya kirayi aminata. Gabanta yadan fadi sai ta hau raba idanu,sannan kuma a hankali ta fara takowa "Jeki kiramin SULTANA" ya fada yana bude aljihun gaban motar. Juyawa tayi da sauri ta koma gurin sultanan "To me zanyi masa?" Ta fada tana bata fuska tare da murguda qaramin bakin nan "Oho na sani?,sha'anin miji da mata?" Aminata ta fada cikin tsokana,uwa uba itadin tadan girme musu saboda haka ta fisu wayo a wasu abubuwan. "Kinga aminata banason iskanci, don ni ba 'yar iska bace,kije ki gaya masa bazanje ba" ama dake dan gaba kadan dasu maganar ta sauka a kunnenta,tasan dama za'a rina,amma sai tayi kaman bata ji ba. Idanu aminata ta fidda "Ni bazan iya ce masa haka ba wallahi". "To sai kiyita tsayawa a nan" sultanar ta sake fada tana juya mata qeya. Shurun da yaji yasan akwai walakin,don haka ya fito da kansa. Tun kafin ya qaraso suka dare daga wajen,banda sultana din dake tsaye,duk da zuciyarta nata faman bugawa amma ba zata nuna masa tsoronta ba har ya qaraso "Ita bibi din tana kallonki kikayi wannan shigar?,wuce ciki ki saka atamfa ta mutunci kamar kowa" ji tayi duk duniya kawai ya gama raina mata hankali,ta yaya ta gama target dinta zaice ta wani canza shiga?,ita sam bataga ma ta inda zata cire wadannan kayan ba. "Atamfa?,zafi fa akeyi,ni zafi takeyimin a jikina" ta fada tana tura baki gaba "Zaki wuce ko sai na tattaka wuyanki a gurin?!" Ya fada cikin matsananciyar tsawar data sanya dole ama ta qaraso gurin,fon tasan tabbas akaci gaba da haka to zasu raba abun fadi a gurin,gashi akwai sauran mutane a farfajiyar gidan "Ya isa maina,ke sultana jeki canza din kizo ku wuce,ki daina musu kai kuma ka dinga sassautawa fushinka" bata sake musantawa ba ta juya zuwa ciki din,abinda bata taba tunanin akwai wanda zai sakata tayin ba,sai gashi ta canzo atamfar. Haka kawai take masifar ganin kima da kwarjininta,tasan cewa kwata kwata bata cikin jama'ar dake takura mata cikin gidan,zaiyi wuya tace mata yi ko bari wannan ya sanya takejin ko meye tace mata tayi din zatayi shi. Qin fita yayi kaman yadda yayi niyyar yi da farko,sai ya koma kawai cikin motar ya zauna yana monitoring dinsu,har suka kammala shigewa motocin suka fice. Haka kawai yakejin sai yayi da gaske,kuma babbar dama ce tazo hannunsa na saita komai,don haka ya kunna motar ya tasheta yabi bayansu. Babban event ne me tsada girma kyau da kuma tsari,akwai babban majigi daga waje da zaka iya ganin dukka abinda ke faruwa a ciki. Sai ya samu gurin parking cikin motocin al'umma dake wajen ya ajjiye motar tasa,ya kuma sauke dukka glass din ta yadda zai iya ganin dukkan abinda yake faruwa da kai kawo a wajen. Jinsa yake a takure gaba daya a gurin,kasancewar sam baya son hayaniya,kuma irin wadannan guraren ba wajen zuwansa bane. Kujera motar yadan kwantar kadan ya maida bayansa jiki,ta qasan ido yake ci gaba da kula da komai,har zuwa wani lokaci da yaji ihu sowa da kuma tafi sun cika wajen. Dubansa ya maida ga allon majigi din dake waje,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani. Sultana a tsakiyar fili tana ta cashar rawa,mayafin da ya tilasta mata sakashi ma baya ko a hannunta bare kanta. Tsam ya tashi ya zauna yana dubanta,family and friends sun rude dayi mata tafi,masu liqi kuma sunyi,sai step din ya fara cika da mutane saboda ita. Wani irin salon rawa da tunda yake bai taba ganin irinta ba,bai kuma taba tunanin ta iya rawa haka ba. Daga gefe ya hangi isowar ama,ta saka hannu a dabarance ta janyeta daga gurin. Hannunsa ya nutsa saman sumarsa yana rufe idanunsa,wani takaici yana cika mishi zuciya. Iska me zafi ya furzar yana ji har cikin ransa lallai tabbas dole ya dauki mataki tsatstsaura a kanta,matakai take buqata masu tsauri,baiga ta inda sassauci zai gyaro sultana ba,bayan kullum qara girma takeyi kuma sake sangarcewa takeyi. A zafafe ya tayar da motar yana barin wajen ransa yana sake dugunzuma. Da irin wannan bacin ran ya isa wajen askin. Dama can bame yawan magana bane,don haka har akayi aka gama yabar wajen ba maganar da ta hadashi da kowa. [5/13, 10:00 PM] RM Fatima Shehu Musa : *_GUDUN ADDARA_* *H
Chapter 28 · 0% Book details