← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 30

Sashe 6

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lunch bag da sauran tarkacen kayan makarantar sultana din dake ajjiye yana jiranta. Kai ta girgiza tana sakin qofar gami da qarasa shigowa dakin. Wata baiwa zata iya cewa ko meye zata kira hakan?,har yau bata tabajin da haushin sultana ba,kokuma taji ta qosa da halayyarta ba ko guda daya. "Sultana" ta kirayeta cikin lallabawa. Shuru babu amsa kamar yadda ta zata,duk da tayi imanin idanunta biyu,saboda tana hango hasken mayatacciyar game dinta data jinginar a jikin NINI dinta tana yi. Sake kiran sunan nata tayi a karo na biyu,wannan lokacin bata damu data amsa ba tace "Kin sandai lundi(monday)yau,sannan kuma examine zaku fara,yanzu haka nasan kowa yana can ke yake jira" sosai ta tura baki gaba tana ji har cikin ranta tanja ta dameta ainun ta kuma uzzura mata,saidai bata tankawa tanja din ba sai shura qafafunta da tayi taci gaba da game dinta "Sultana" "Don Allah tanja ki barni,na riga na gayawa bibi bani da lafiya,kuma nasan zata gayawa kowa haka,bazanyi wani examine ba ni" "Ai shikenan" tanja ta fadi tana miqewa. Iyakar qoqarinta itama din tayi,tana jin sultana kamar jininta dukka silar nafessa,ba zata tabawa mantawa da nafessa ba kamar yadda batajin zata gajiya da sultana da kuma dabi'unta. Tana jan qofar taku biyar kacal maina ya sanyo kai. Tadan rabe gefe suna gaisawa. Ba ma'abocin son gaishe gaishe bane, gaisuwa daya tak ya tambayeta "Ina sultana?" "Tana ciki,amma bata da lafiya" bai qarasa jin statement dinta ba ya zare idanunsa daga kanta ya doshi qofar dakin,saboda a cikin jikinsa yakejin bai gamsu da rashin lafiyarta ba. Cikin zumudi ta qara speed na game din nata,saboda tana stage na qarshe a game din data dauki dogon lokaci batakai wannan stage din ba,mintuna qalilan ya rage mata takai gidan qarshe. Tayi mugun nisan da bataji shigowarsa ba,ba kuma lallai da idanu ta ganshi ba,saboda ta nutse sosai cikin comforter tana buga game dinta hankali kwance. Gyara tsaiwarsa yayi sosai yana kallon yanayin kwanciyarta cikin comforter din. Yana da wani irin kaifin ji da kuma kaifin gani,saboda haka yana iya hangen haske ta cikin comforter din. Mamaki yaso saukar masa,me yakai haske cikin abun rufarta?, tambayar da ta sanyashi miqa hannu yana yaye comforter din,dai dai sanda motsin bargon yayi silar faduwarta a game din,cikin sakannin duka ta hasala ta bude bakinta cikin tsaiwa zata sauke kwandon bala'i dukka a tunaninta tanja ce "Wai nikam ana dole tanja?,nace bani zuwa meye ne naki a ciki idanb........" Gaba daya maganar tayi wani irin juyi ta tsaya mata a maqoshi. Dukka idanunta biyun dake wani irin haske da sheki cikin taqaitaccen hasken dakin ta zuba masa su cikin matuqar tsoro da razanar yadda ya risketa. Sauke idanunshi yayi ga gadon,ba komai saman bedsheet din sai tarin ledojin madararta bila adadin. Biscuit da chocolate masu dan banzan zaqi da suka raineta da su kuma har yanzu suke ci gaba da bin jini da kuma rayuwarta. Zare idanunsa yayi daga 'yar kallo kallon da sukewa juna tsakanin idanunta zuwa shinfidarta wani bacin rai yana lasar zuciyarsa ya maida kan tanja dake shigowa dakin kanta a qasa,tana jin nata laifin na idar da abinda ba haka bane zabi ne na sultana din kawai "Na bata minti biyar kacal ta fito,ki bata lunch bag dinta ta fito da ita kamar kowanne yaro" ya qarasa fadin maganar yana fita a dakin ba tare daya waiwayo ta ba. Wani uban tsalle ta daka tana direwa tsakiyar gadon nata "Ke kika kiramin shi,kuma Allah ko meye zaiyi bazanje ba,ni ba tsoronsa nakeyi ba" abinda sultana din ta sake fadi kenan tana juyawa zata koma gadon. Tarota tanja tayi,cikin lallashi hilata ta samu ta shawo kanta da qyar ta watsa ruwa tunda already tun asuba take nata wankan,ta fara shiryawa tanayi tana mita,baki abun magana,abinka da mutum me baki kwata kwata taqi yin shuru. "Sultana,kinfini sanin halin kawunki,idan yayi magana baya canzata,kibar ganin yana sonki yana nuna miki fifiko cikin yaransa,to amam kada ki manta ainihin halayyarsa tana nan fa,bashi da sauqi muddin akan harkar karatu ne" ita kanta ta dade da haddace wannan saidai ta yiwa wani tuni. Amma a yau din maganar ta zama kamar tunasarwa ce a gareta,tilas ta gama shirin ta kuma dauki lunch bag din da tsabar gata kullum kwanan duniya sai an rakata da ita,amma yau yaa maina din yace baison ganin wannan. Gaba daya a taqaice maina din yana son zame mata wata barazana kenan?. Ta yiwa kanta tambayar dai dai sanda ta isa gaban motar. Yadda kowa ya tsirata da idanu ya sake hassalata,wannan ya sanya tana sane tabi takan qafafunsu ta kuma tsallake kowa sannan ta zabi seat din da yayi mata. Kowa a cikinsu yanason yayi qorafi amma hakanan yaja bakinsa ya kulle saboda maina din,wanda ya tashi motar ya kuma figeta da gudun nan nasa dake sawa mutum nutsuwa koda bai shirya hakan ba. *Yar uwa kinsan illar dake tareda infection kuwa?**,*to bari kiji kadan daga cikin illar da infection yake da ita*,*kinsan cewa infection* *yana hana haihuwa* *yana hana ma'aurata jindadin mu'amala* *yanasa warin gaba kowane irin tirare kika sa bazai hana wannan warin fita daga jikin kiba* *fitar farun ruwa* *kaikayin gaba* *tusar gaba duk suna daga cikin illar da infection yakewa lfyr ki* *Ina masu fama da* *ulcer,Asthma,sickle,ina matar dake fama da fibriod,matsalar rashin haihuwa ko bushewar jiki da fata shin kiba kareki kikeso ki koma yar chas chas ko tumbi ne ya hanaki gayu ku garzayo kuma ku kwada ku gani da ikon Allah da izinin Allah,munada blood circulature machine vip chais kedai kira number nan domin karin bayani ku tuntubeni kai tsaye ta nan* https://Wa.me/2347035275119 *Masu tambaya muna maraba daku* 09113542209 *Mun gode* *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 06 Sai da ya ajjiye kowa,ita kadai tayi saura cikin motar amma yana ankare da ita sam babu damuwa a tattare da ita bare gudun kufcewar lokaci ya dameta. A nutse cikin sassanyan muryarta ma take bin waqar dake fita ta radion motar wadda suka sako bayan kammala labaran safiya daga radio alheri. A hankali ya sanya hannunsa ya kashe radio din gaba daga. Sai tayi d'if tamkar me nazarin wani abu,kafin daga bisani ta tabe baki ta kuma maida dubanta kan titunan da suke wucewa wanda ke da qarancin zirga zirgar jama'a ainun. Da kallo ya bita sanda ya sauketa,har zuwa sanda ta shige sashen gine ginen ajujuwansu. Janye idon nasa yayi,kana ya sanya hannu ya zare belt din jikinsa sannan ya kashe motar ya kuma bude murfin ya fito. Hakanan kawai yaji yana da buqatar bincikar motsinta da duk wani performance nata na makaranta. Kyakkyawar tarba ya samu daga office din principal din saboda sunsan waye shi daga kuma wanne gida ya fito. Cikin ban girma principal din ya gabatar masa da document na sultana kamar yadda suke da tsarin ajjiye document na kowanne dalibi tare da rubuta abubuwa da suka shafi rayuwarsa cikin makarantar,sannan ya dauki wasu takardu ya fice don ya bashi damar dubawa a nutse. Tun kafin ya kammala dubawa ransa yayi qololuwar baci,ya sauke document din daga fuskarsa yana ajjiyeshi saman table din. Tsai yayi a wajen tamkar bazai tafi ba sai kuma ya soma takawa yana fita a office din ba tare da ya jira ko ya nemi kowa ba. A gaggauce yake tuqin saboda zuciyarsa da ta motsa. Baiga komai na kirki cikin karatu da shaidar da sultana ke samu a takardunta ba,komai nata poor,babu wani abu da yake EXCELLENT idan ka dauke tsaftar uniform dinta. Sanda ya isa gidan kai tsaye sassan bibi ya wuce. Baiko kula da gaisuwar hadiman bibi din ba ya zarce dakin sultanan. A hankali ya murda qofar dakin ya kuma turata. Duk da haske bai wadaci dakin ba amma yana iya kintacen yadda aka gyare dakin tsaf kamar ba shine dakin dake hargitse dazu dazun ba. Hannu ya sanya ya kunna fitilun dakin,haske ya gauraye ko ina. Wannan dakin na sultana wanda shi da ita suka rayu tsahon shekaru tara a ciki yana kula da ita,yana rainonta,yana mata ginin da yake da tabbacin zata zama cikakkiyar mutum kamar kowa,cikakkiyar mutum data banbanta kuma da kowa din,amma a yanzun yana ganin take take na idan baiyi da gaske ba tabbas mafarkinsa zai gushe ne ba tare da ya maidashi cikin zahirinsa ba,burin nafessa kuma zai shafe kamar yadda a yau ya shafe daga doron qasa. A nutse kuma a hankalce yake qarewa dakin kallo. Cike yake da teddies tako ina tamkar don su take rayuwa. Baby doll kala kala. Daga can wani table din kuma tarin games ne iri iri,tab da spare din wayar hannu. Qarasawa yayi qaramar drawer dinta ya sanya hannu ya bude. Tarin biscuit da chocolate kamar wani qaramin store. Ya matsa yana buda fridge dinta qarami dake dakin. Madara ce kamar ko yaushe danqare a fridge din tun daga sama har qasa. Tamkar wata ruwan sha,tamkar ba madara bace me tarin daraja da tsada wadda sai anyi takakkiya tun daga niamy an kawota ba. Rufeshi yayi,ya qarasa ma'adanar litattafanta ya fara saukesu a qasa. Zaman dirshan yayi saman lallausan carfet din dakin yana bitarsu daya bayan daya "Ya salam.......ya ilahee" shine abinda bakinsa dake motsawa kadan kadan yake furtawa. Kusan za'a iya cewa ba komai a cikin litattafan nata me bare a iya ganin me ta shuka,tabbacin bata note bata assignment bata kuma homework ko class work. Shafukan da ya dace da samun rubutu kuwa ba wani rubutun arziqi bane a ciki. Komawa yayi kan litattafanta na islamiyya. Nan ma dai duka sammakal,sai ya tattara litattafan ya jayesu gefe yana dafe da goshinsa zuciyarsa na wani irin bugawa cikin zallar bacin rai. Wato tana rayuwa ne a duk yadda taso kenan?,babu wani me monitoring dinta?. Kamar Bibi tasan tambayar da yake yiwa kansa kenan ta murda handle din qofar ta shigo. Idanu ya bita da shi kamar yadda itama.ta bisa da nata idanun "Tanja tacemin kana ciki tun dazun" kansa ya gyada mata a sanyaye yana lumshe kyawawan idanunsa da suka dan sauya launi kadan. Daya daga cikin alamun dake nuna yana cikin bacin rai kenan "Bibi...." Ya kirayeta yana tusa kalaman da zaya gaya mata kada zafin dake ransa yasa yayi maganar da bai dace ba,don ba kasafai ya fiya control din kansa
Chapter 6 · 0% Book details