Sashe 19
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsammanin sun tasamma shekaru sha takwas takwas ne. Sosai halinsu yazo daya,shi yasa abota a tsakaninku keda matuqar qarfi da tasiri,duk wanda yasan daya a cikinsu yasan daya,kowaccensu tana ji da gata da kuma sakewa,duk da cewa a cikinsun babu kamar sultana,wadda bayan fifikon gata data samu,ta samu wani irin fifiko na kyawun sura tun gabanin ta kammala cika mace. Ta mugun iya dressing kamar yadda yaren faransanci ya zauna daram a harshenta,hakan kuma baya rasa nasaba da zaman da tayi a waje cikin turawan faransa na tsahon wasu shekaru harta kammala primary dinta. "Ni so samu da magariba za'a fara birthday dinnan maganar gaskiya sai yafi dadi" sultana da ta qare karanta katin birthday din hanan ta fada tana maida dubanta ga fuskar rachida. Qaramar dariya rachida ta saki "Allah ya shiryaki kedai,duk wani harkar rawa kina gaba gaba" ido sultanan ta lumshe "Hmmm ke bakisan yadda rawa take da dadi bane,Allah ji nake kaman na fara takawa tun yanzu,ni hanan kin gama biyana,irin wannan birthday din nakeson yi qarshen shekarar nan" sultana ta fada tana tashi ta zauna sosai saman kujera,saboda tana hasaso yadda abun zai kasance "Idan yaa maina ya bari ba" bilkissou ta fada tana zuqe madarar hannunta. Harara sultana ta jefa mata "Kina daga kwance kina shanyen madara kina min fatar tsiya,wanne ya maina din da yanzu baya zaman gidan nan ma,saidai munafukai irinsu goumar su gaya masa" "Baqin buzu?,yana burgeni wallahi" hanan ta fada tana dan murmushi. Caa sukayo mata suna tsokanarta,yayin da sultana ke binsu da ido tana tabe baki. A rayuwarta haka kurum taji ta tsani koda zancan soyayya ma,duk da su din wannan ba fagensu bane dama,ba wani abu bane da sukeyin Maganarsa ba "Meye abun burgewa a wajen wannan?,kaf halin yaa maina daidaiku ya baro" sultana ta fada tana tabe baki "Wai ina su najma" "Kin kuwa tunamin,basu nasu card din" idanu hanan ta zaro "Ko kema fa lallabawa zakiyi kije baresu?" "Kada ki damu,sun jima suna cewa a gayyacesu idan za'a yi,barema duka date din da aka saka dodon nasu baya nan,kinga nima hankalina kwance zamuje mu dawo abinmu ba wanda zaya matsa mana,wannan babban hotel da dad ya kama mana hall a ciki ai ya gama mana komai" ta fada tana dariya. Sun jima suna hirarrakinsu suna sake tsara yadda zasuyi abinsu "Sauran abinda m ba zamu iya ba auntie haula tace zata tsara yadda komai zai tafi mana yadda mukeso" "Sai auntie" sultana ta fada tana dariya, tana jin dama itace cikin gidansu hanan,babu matsi babu kuma takura. Sallama sukayi da Bibi ta rakosu makeken parking lot dinsu inda suka zaunar da driver dinsu yana jiransu. Sai da suka fice a gidan sannan ta juya ciki tana gyara card din hannunta. Sassan uncle umar t soma shiga,ta samu mamma na sanya turaren wuta a falo. Gaidata tayi mamma ta amsa tana dubanta yadda ta shigo a wani mugun nutse "Najma fa?" "Suna daki ita dasu aminata" bata ko waiwayo ba ta zarce dakin da zumudinta,sai mamma ta bita da kallo har ta shige sannan ta dauke kanta tana ci gaba da zuba turaren wutan. Cikin sa'a dukkansu ta samesu a dakin,aminata najma yasmin da lamira "Kuzo kuga wani abun arziqi" ta fada tana rarraba musu card din. Karban nashi kowa yayi yana dubawa,najma ce ta fara daga kai "Birthday din hanan?,haka akeji da ita aka kama mata wannan babban hall din?" Dariya sultana tayi "Don hall kawai?,sai kinje ma kinga yadda aka tsara gurin" "Zuwa kuma sultana?" Aminata ta fada tana zare ido. Da wurwuri sultana ta jefeta da harara "Eh mana,hanan ce fa,kuma idan ya maina kuke tsoro ai baya nan,hasalima shekaran jiya duka duka ya tafi,shi kuma da sake dawowa sai wani satin nan da kwana goma ma,kunga hankali kwance zamuje mu dawo" shuru suka danyi suna kallon juna "To ta yaya zamu fita su mamma basusan birthday muka tafi ba?" "Karku damu da wannan kun manta ina da modu?" Dariya suka saki plan din nata yana musu dadi. A nan suka sake suna maida yadda abun zai wakana. Tun daga ranar take shirya kaya da shigar da zatayi. Duk da dimbin suturunta da suka kusa kala dari biyu amma sai taga sam basuyi mata ba. Ta tashi hankali har sai da aba yasa aka dauketa taje ta siya abinda ranta yakeso da sunan wani taro zasuyi a makaranta. Ba wanda ya qaryatata tunda makarantarta daban data sauran. *_THE DESTINY ||_* *****Wadatacce kuma yalwataccen daki ne wanda a qalla yake dauke da manyan katifu masu azabar tudu da taushi guda uku. Turkey carfet ne malale a qasan dakin wanda ya dace da curtains dake maqale jikin manyan windows da qofar dakin. Ba wani tarkace a dakin,domin kuwa komai yana tsare ne bisa muhallinsa cikin tsaf da kuma wayewa. Akwai babbar cupboard ta jikin bango wadda daga samanta akwatune masu kyau a qalla sunkai shida mallakin samarin dakin. Daga gaban murfin cupboard guda daya maina ne a tsaye yake dauko wankakkun kayansa dake shimfide a ciki suna fidda qamshin sassanyan mayataccen turarensa yana jerawa cikin wata kyakkyawar madaidaiciyar luggage milk color da torches na Navy blue a jikinta. Daga yadda yake zaro kayan yana jerasu a ciki zakayi tsammanin yana yine saboda tsabar yanga da kuma salo irin nasa. A'ah,a yau din ba haka take ba,domin kuwa tun daren jiya ya tashi baya jin dadin jikinsa sam,wani irin kasala da mugun ciwon kai harda tsarabar guntun zazzabi su suka tayashi kwana. Zuwa wayewar garin yau kuma yaji babu abinda yake da buqata irin yaje gida,duk da cewa suna tsakiyar karatunsu da ya soma daukan zafi da gaske. Wani matashinne kamar shi yayi knocking qofar sannan ya turo ya shigo dauke da jakar leda dake dauke da tambarin wani gidan abinci dake nan kusa da ecole din nasu. A bayansa wani matashinne da dukkansu shekarunsu zasu zo guda. Kadan ya waiwaya yana amsa sallamar tasu sannan yaci gaba da qoqarin zuge zip din luggage din "Ami(aboki)Me nake gani?,ya da hada kaya cikin bagage(luggage)?" Ya fada yana neman daya daga cikin sofa da suka qawata dakin da ita ya zauna akai idanunsu dukka su biyun suna kan maina din. Idanunsa yadan lumshe kadan yana jin kansa yana dan sarawa kadan duk da yadan samu sassauci "Gid nikeson zuwa,amma gobe ma zan dawo ko lundi(monday)" "Kace dai kawai raki zaka nuna da langwai,kanaso kaje ama tayi jinyarka" murmushin gefen baki kawai yayi,da mahadi da sultan din dukkansu gwanayen tsokana ne,ana cewa sai hali yazo daya ake abota,to amma su a kansu abun ba haka yake ba,akwai banbacin halaye da dabi'u masu yawa tsakaninsu. Kusan dukkan abokansu dake shigowa dakin mahadi da sultan ke kawosu,don ta maina kam shi daya ma zai iya qare zamanshi. Yana jinsu sunayi masa tsiya ya wuce toilet dinsu dake manne cikin dakin,ya fiddo brushes dinsa da toothpaste da sauran kayan wankanshi ya dawo ya qarasa hada kayanshi. Order yayi na mota har cikin makarantar,ta iso bakin hostel dinsu sultan da mahadi sukayi masa rakiya har ya tashi. Lamo yayi cikin motar,bai motsa ba har sai da kira ya shigo wayarsa. Da ya duba da kyau sai yaga meena ce,yaja siririn tsaki yana maida wayar silent ya jefata cikin jakar hannunshi da ya zuba qananun tarkacensa. Yadanbi jakar da kallo,shi da yace gobe ko jibi zaya dawo,besan me ya sanyashi debo kaya haka ba. "Alhamdulillah" ya fada a nutse sanda ya sauka tsakiyar farfajiyar gidan yana duba yadda sassan gidan yayi shuru. Sake duba wrist watch din hannunsa yayi wanda ke dauke da sunan kowacce rana yanason ya gani ko yayi kuskuren tunanin yau din weekend ce saidai kuma koda ya kalla dai dai lissafinsa ya bashi. Bai tsawaita tunaninsa ya janye luggage dinsa kansa tsaye ya wuce sashensa,don duk cikin mutanen gidan yasan ba wanda yasan da zuwansa. Ko yaya yaje makaranta ya dawo bai iya zama a daki haka,mafi yawan lokutta ma ama na sanyawa a gyara masa ne tun kafin ya iso din saboda saninsa da tayi da shegen tsantsami da tsaftar tsiya. Yau ba wanda yasan da zuwansa bare yayi masa wannan tanadin,don haka ya zage ya gyara dakin nashi yadda yakeso sannan ya shiga wanka. Yaji qwarin jikinsa sosai,kamar ciwon dama yana jira ya baro makarantar ne. Wannan ya bashi damar shiryawa cikin trouser silk shirt me gajeran hannu. Ainihin cikar zati da surarsa suka fito muraran,kyakkyawan ba'abzinen matashi aliyyu haidar mayak'i. Da salon nutsuwar nan tashi ya wuce zuwa sassan bibi. Duk yadda sukayi fada ko suka samu sabani,duk yadda sukaso share juna ita dashi amma hakan bai yiwuwa,shi yasa sam ba'a shiga fadan bibi da haidar maina,idanma ka shiga din kaine da jin kunya. Sai daya dan kalli sassan amansa kadan kafin ya shige,ya san muddin taji ya shigo gidan ba ita ya fara nema ba saita nuna masa fushinta koda da kalaman baki ne,sai ya qudirta a ransa bazai jima wajen bibi din ba,zai fito yaci abinci a wajen ama din nasa. Dab da zai shiga saqo ya shigo wayarsa,sai ya rage sassarfar da yakeyi yana dubawa. Tailor dinsa ne yake gaya masa ya kammala dinkunansa duka,zaiyi tafiya zuwa diffa,idan baya gari ya aiko daga gida a karba masa,kada ya buqacesu shi kuma baya nan. Saqon ya rufe yana rayawa a ransa zai fita idan ya gama cin abinci ya karba,ko miqe qafarsa ya danyi qila ya sake jin qwarin jikinsa. Baki bibi ta sake da ganinsa,abinda basuyi tsammani ba tunda duka duka wancan satin ya tafi,kuma a yanzun yakanyi sati uku ma baizo gidan ba "Hala kewar matarka ta isheka kazo ganina ko?" Bibi ta fada tana dariya. Fuska yadan yamutsa kadan yana dubanta sannan ya nuna qirjinsa da yatsanta "Ni maina?,Allah ya kiyaye,na barwa su saddi" wasa ne da ba kasafai suke yinsa ba ita dashi,amma duk sanda kaga ta jashi da wasan to tabbas tana cikin nishadi ne da jin dadin ganinsa. Suna gama gaisawar bai jima ba ya miqe "Bari na qarasa ciki" "To,saika fito". Kyakkyawan falon da ko yaushe yake cikin tsafta da kyau,komai nashi bata taba bari ya tsufa ko kyansa ya disashe. Ba kowa cikinsa sai masu aiki guda biyu dake yayyafin turare suna gohe marbles din dake shimfide a qasan falon. Wannan din kusan al'adarta ce,kowacce rana sai anyima