Sashe 20
Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
qasan falon irin wannan gugar sau biyu zuwa uku,wannan ya sanya qamshi sosai ya kama wajen. Sun shaida masa tana samanta,sai yace su barta,ya sanya suka shirya masa abinci ya soma ci,sannan ya fidda wayarsa ya fara kiranta. *_GUDUN ADDARA_* *H U G U M A* PAGE 20 Ba jimawa ta sauko tana fadin "Wanne irin shashanci ne haka maina?,zaka taho ba zaka sanar ba?" Dan qaramin murmushi ya saki,har yanxu ama tana kallonsa ne kamar wani saddi "Banajin dadi ne ama,hakanan naji inason zuwa na ganku". Fuskarta tadan nuna damuwa,taja kujerar dake fuskarsa ta zauna idanunta a kansa cikin kulawa tana tambayarsa meke damunsa?. "Zazzabi ne sai dan ciwon kai bame yawa ba" "Subhanallah,Allah ya sawwaqe,to ya jikin yanzu?" "Alhamdulillah,da sauqi sosai" "Ma sha Allah" ta fadi dai dai sanda wayarta ta dauki tsuwwa. Fuskar wayar ta kalla sannan a hankali ta furta "Mariya?" Sai ta daga kiran ta saka a kunnenta. Sallama ta farayi sannan sauran maganganu suka biyo baya,tun tana maganar a hankali har alamun fushi suka dan fara bayyana saman fuskarta,kuma alamu sun nuna ranta ne ya far baci. Dukka maina yana ankare da ita yana diban abincin kadan kadan yana ci yana nazarinta "Shikenan na gode,Allah ya qara zumunci" ta qarashe fada tana katse kiran. Iska ta furzar daga bakinta tana hade yatsunta waje guda "Lafiya ama?" Ya tambayeta yana ture kwanon abincin daga gabansa "Wato shi zumuncin yanzu haka ya koma?,Allah ya sani ina bakin qoqarina gurin ganin na gina zumunci me qarfi tsakanina da 'yan uwana amma kowa sai ya watsamin qasa a ido saboda Allah ya jarabceni da son 'ya'ya mata kuma bai bani ba....." "Wani abu ya sake faruwa kenan?" Ya kuma fadi ransa yana sosuwa saboda yadda fuskar ama din ta sauya ta fara hada ja,alamun dake nuna inda zata samu sarari kuka ma zatayi "Mun gama magana da mariya zata bani bintu,ina ganin kamar diyata take tunda dan uwana ya hanani ita din 'yaruwatace mace zatafi fuskantata,har daki nasa an gyara mata an zuba furniture da nayo order dinsu daga turkey,an mata dinkin dukka kayan da zata saka,na siya mata foam zan canza mata ecole duka a nan,na ajjiye mata driver personal,na gama komai cikin satinnnan nake shirin zuwa Nigeria na daukota,shine yanzun ta kirani take gayamin wai abbanta ya hana,kakarsu tace ba zasu bada ita ba" ta qarashe maganar da alama abun ya sosa mata rai sosai. Kyawawan idanunsa ya lumshe yana jin ciwon abun shima,bawai kuma ciwon hanasu bintu bane,tunda ko ba komai,duk da auty mariya masu wadatane sosai suma din amma basu kama qafar ama ba,ama nada son yara da riritasu,cikin gidan kaf banda sultana baiga wanda baya cin moriyar ama din ba wajen kyauta da jan mutum a jiki,ya sani bintu din zata samu gata da kulawar da babu lallai ta samu a gidan mahaifinta. Bacin ransa na ganin damuwa me tarin yawa saman fuskar ama din,inda yana da hali da ya samar mata wannan abun da zai wanke wannan baqincikin da takeji a duk sanda ta nemi riqon diya cikin diyoyin 'yan uwanta bata samu ba. Matsowa yayi sosai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa,cikin tausasa murya ya soma magana "Kiyi haquri ama,daga yau kiyi haquri kibar musu diyoyinsu daga yau,ni na miki alqawarin in sha Allah duk sanda nayi aure zanyi addu'ar Allah yayita bani diyoyi mata,zan fara addu'a tun yanxu,sannan na miki alqawarin ko diyoyi mata nawa na haifa naki ne har sai kince kin gani da riqon 'ya'ya mata". Wani qawataccen murmushi da ya bayyana kyau da sauran quruciyarta ta saki bs tare da ta sani ba "Maina,ta yaya zan gaji da riqon diyoyinku koda taron arfa zaku haifa?,ai saidai naci gaba da addu'ar Allah yaci gaba da baku masu albarka ya kuma hore mana abinda za'a kula dasu" daya hannun nata itama ta dora saman nasa "Na gode sosai,daga yau in sha Allah na haqura,zan kuma jirayi jikokina komai tsahon lokaci kafin zuwansu" Murmushin shima yadan saki yana jin dadin yadda maganarsa ta faranta mata. Agogo ya duba sannan ya miqe yana cewa "Zanje na karbo dinkunana ama" "Allah ya tsare,kada ka jima kaga bakajin dadi" "In sha Allah......Key din mota daya zaki bani aro" "Ya kamata kayi zuciya kayi motar kanka mana" ama din ta fada tana dan murmushi hadi da miqa hannu ta dauko key din motar da dazu goumar ya ara ya fita da ita ta miqa masa "Akwai lokaci ama,karatu,yanzun inayin mota ko banaso sai ta sanyani yawo,ko banyi ba su sultan zasu sakani" "Wannan karatu,Allah yasa a gamashi lafiya" ya amsa mata da ameen yana kaiwa qofa. Sai da yahau titi sosai sannan ya tuna ya cewa bibi zai dawo,don haka ya ciro wayarsa yayi kiranta "Bibi na wuce amma yanzu zan dawo" "To yayi,idan kana dawowa ka tahomin da tsiren yahaya,na kwana biyu banci ba" dariya tadan subuce masa "Kicemin kawai kwadayinki ne ya tashi" dariya tadan saki itama "Idanma shidinne ai kaine ka koyamin ko?,nidai a kawomin" "To in sha Allah" ya fada yana murmushi,sai ya katse wayar ya ajjiye a kusa dashi,ya dora hannuwansa duka saman sityarin yana fidda qotutuwar ajiyar zuciya idanunsa bisa titi "Kowa yabar gida gida ya barshi" ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa. Mintuna arba'in ya qarasa shagon telan nasa,ya samu kayan a kammale cikin babbar jakar ledar dake dauke da tambarin shagon. Ya qarasa gurin biyan kudi yayi musu transfer na balance dinsu "Yallabai ka duba mana" auwalu tela ya fada yana dan murmushi. Daukan ledar maina yayi "A'a,basai na duba ba a hanya nake" "To godiya mukeyi,sai mun sake ganinka" ya fada yana masa rakiya har bakin motar. Sanda yake dawowa cikin shagon muzammilu ya tareshi "Da alama kudi ka samu jikin sarmayin nan naga ka kasa zaune" dariya Auwalu ya saki "Ah na samu alhmdlh,kowanne kaya saida ya qaramun kudi akan ainihin kudin dinkin kuma yana sane,na jima banga matashi da kudi basu dameshi ba irin maina mayak'i" idanu muzammilu ya buda "Kai......kada kacemin family din MAYAK'I ne?" Kai auwalu da ya jawo wasu kaya zai yanka ya kada masa "Qwarai kuwa" "Amma gaskiya baka hadu ba,kuma kai banza ne,tsakani har ga Allah mutum irin wannan yazo wajen nan koni ka kasa gayawa na yagi wani abu?,yo aiko kudin cefani na sati na samu gurinsa ina laifi" harara auwalu ya jefa masa "Hauka nake na gaya maka ku zubar mana da mutunci?,irin wadannan basason roqo basason wargi,kai bakaga yanayin fuskarsa ba?, baya wasa,ni ban taba ganin dariyarsa ba,yana dai murmushi sa'i sa'i" "Ba komai,zamu hade nan gaba" "Kai ka jiyo" ya amsa masa yana zare tip na awo daga wuyansa. A nutse yaci gaba da tuqinsa tamkar bashi da wajen zuwa. Haka kawai weather din maradi din yau take masa dadi,sanyi sanyin nan dake nuna an fara bankwana da zafi. Sannu sannu har ya isa gurin yahaya. Gurin gashin nama ne na gargajiya sosai,mutum biyu bibi keson namansu yahaya ko yahuza. Ba ruwanta da wajen wani BBQ ko gashin engine da sauransu,takance ita tafi gane wannan,shi yasa koda cikin gida masu aiki sukace zasu gasa mata ba kasafai take ci ba,saidai ta aiko nan din ko wajen yahuza a siya mata. Yana ganinsa ya iso gaban motar tun kafin ya fito. "Yallabai,hala bibi tayo aike" fuskarsa adan sake ya gyada masa kai "Saqo ta bayar takanas" "Kayya,kuma ba'a zo da wuri ba yau,yanzu na gama hada kaya komai ya qare wallahi" ya fada cikin rashin jin dadi yana kallon bayansa "Babu komai,Allah ya qara albarkar kasuwa" maina din ya amsa yana laluba canjin aljihunsa ya miqa masa. Hannu bibbiyu yasa ya karba yana godiya,yana matuqar jin dadin zuwan maina gurin,koda bai siya komai ba zai cikaka da alkhairi ya barka a wajen kana godiya,yana tsaye har motar maina din tabar wajen. Har ya dauki hanyar gida yaga bai kamata ya shigarwa bibi din haka ba,ya tabbatar ta sanya rai tunda har ta bashi sautu,don haka ya juya akalar motarsa zuwa wajen yahuza dake bakin police station. A hankali yake gangarowa saman babban titin da ya kasance daya daga cikin manyan titunan na garin maradi din. Titine dake dauke da manyan hotels eatery da guest houses parks da sauransu. Wannan dalilin ya sanya baka rabashi da wucewar manyan motoci masu matuqar tsada da daraja saboda gurin na kai kawon baqi daga gurare daban daban,yayan masu kudi masu buqatar hutawa da sauransu,dalili kenan da ya sanya aka qirqiri police station a gurin saboda samar da tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya. Daga gefe ya tsaida motarsa,ya saka hannu yana dage glass din motar yana duban glass din yana jiran ya gama rufewa ya fita a motar. Kamar gilmawar walqiya motar tazo ta gotashi,idanunsa kuma sukayi masa kyakkyawan daukan wata sura cikin motar da tafi kama da SULTANA. Tamkar an sanya wuta an jashi haka yaji haka yayi fit ya fita a motar,daidai sanda motar ke sanya hancinta zuwa cikin katafaren hotel din dake girke a wajen,karkatawar da motar kuma tayi ya bashi damar ganin sultana din sosai zaune daga back set tana dariya. Wani mugun bugawa zuciyarsa tayi har sai da yaji kaman zai fadi. Bai qara koda second guda ba ya soma tattakawa cikin sassarfa yana dosar gate din. Kanshi tsaye ba tare da ya tsaya kulawa da security dake bakin gate din ba ya cinna kai ciki. Daidai sanda motar ta kammala tsaiwa qofofin motar suka bude wadanda ke ciki suka fito. 'yaran 'yammata ne kamarta su biyu sai matasan samari su uku harda driver din. Sanye take da wani tsadadden trouser da ya zauna daidai jikinta kamar yadda rigar tayi masifar dacewa da qirar jikinta,qafafunta saye cikin wani arnen Boot da aka siyeshi da CFA me tarin yawa. Kanta babu koda qyalle bare dan kwali,gashinta me matuqar tsaho da santsi an masa wani irin gyara da idan ka kalleta zaka rantse batasan zoka kasheni da yaren hausa ko buzanci ba,don gaba daya ta koma kamar wata balarabiya daga qasar qatar ko oman ko wadda ta fito daga qasar hindu. Iya kyau tako ina ita kanta tasan a yau ta yishi,tun sanda aka gama shiryata,su lamira da sauran friends dinta kuma suka tabbatar da hakan ta hanyar kodata. Batasan ya akayi ba,ta sama ne ta qasa ne oho,saiji tayi an finciki