← Book details Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Gudun Kaddara Book 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

me girma na zuciyarsa,ta kuma taba masa wani gurbi da bayason ta taba masa din har sai da ya dan lumshe idanunsa kadan ya bude,wanda yayi dai dai da sake magantuwar ama "Tunda na haifoka ruhinka ke walagigi a hannunsu,tun kana da shekara sha biyar ka fara fuskantar qalubale duk don saboda su,da jajircewata da tsaiwata akan rayuwarka na kawo qarshen komai,a yanzun bayan komai ya shude da shekara kusan goma shine kakeson dorawa daga wata bautar da wahalar?" Tayi masa tambayar data sanyashi sake lumshe idanunsa kawai. Cikin tsakiyar zuciyarsa yake bawa kansa qwarain gwiwa,ya saisaita kansa zuwa harshensa sannan cikin tarin nutsuwar da tun yana qanqaninsa ta sanshi da ita "Ni da nafeesa da sultana duka abu guda ne yayi mu,idan ba jinin nafeesa a jikina ama akwai jinin sultana,ita din qanwata ce halak malak,uwa daya ce kawai bata haifemu ba,amma uba daya muke ni da........" "Aliyyu!" Ta kirayeshi da ainihin sunansa "Banason kaci gaba da gayamin wannan labarin qanzon kuregen......". Yankewa maganar tata tayi sakamakon shigowar kira wayarta. BIBI ta gani,sai ta dauke dubanta daga kan wayar ta maida akan maina,sanann ta sake kallon wayar a karo na biyu kafin ta daga "Okay" kawai ta fada a taqaice,sai ta sauke wayar sannan ta maidata gefe ta ajjiye "Maina" ta kuma kiransa,ba tare da ya amsa ba yayi qas da kansa "Duka duka shekarunka ashirin da hudu ko da biyar a duniya,karatu nakeso kayi,ka zama mutum kamar kowa,banaso ka harmutsa rayuwarka cikin matsalolin da ba naka bane,bakai bane tilashinsu,kabar masu matsala suji da matsalarsu,so nake kayi karatu,ka zama wani,domin kaine madubin qannenka,kuma kaine gobe na" Yadda tayi maganar kadai zai fahimtar dakai zallar qauna da soyayyar da zuciyarta ke gwada masa. Ya sani,ama tana masa wata soyayya ta daban,wadda tasha banban data qannensa ma,bai sani ba,shin ko soyayyar an fari daban take da a zukatan iyayensu?. Wani qaunar ama ne ya sake saukar masa,tabbas duk abinda takeyi yasan tana yine saboda soyayya da qauna irin ta a da uwa,to amma shi in ta yaya zaya zuba ido ya bari tarbiyyar sultana ta samu rauni?,yarinyar da tunda sanarwar haihuwarta ya shiga kunnuwansa yakeji a jikinsa kamar shine mahaifinta?,kamar rayuwarta da ha in kula da ita ya hau kansa kacokam. "In sha Allah zan kula iya bakin ari na,ba zaki sameni da wani abu da bakiso ba" "kaje bibin tana kiranka" ta fa a da sautin da zai nuna maka akwai hushi dan are cikin ranta. *ZAFAFA BIYAR FAMILY* *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba* *_ZAFAFA BIYAR_* *_SABUWAR SHEKARA_* *_SABON TSARI_* *_SABBIN LABARAI_* *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_* *_CAKWAKIYA_* *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_* *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_* *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_* *_KWANTAR DA ZUCIYA_* *_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_* *QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA* *KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo) *TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul) *AMEENATU* (Mamuhghee) *GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma) *_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_* *_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_* *TSARIN SHINE KAMAR HAKA* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *THANKS FOR CHOOSING US* *_GUDUN KADDARA_* *HUGUMA* PAGE 03 https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz Har ya kusa fita ya dakata,ya waiwayo yana dubanta. Kallon jaridar kawai takeyi amma da alama bata iya ci gaba da karanta komai ba "Don Allah ama almu ko atta,wani yayimin kiran najma ta dawo ta sake gyara dakin nan baiyi ba" fararen idanunta ta daga ta kalleshi dasu "Ba d'iyar wadda zan kira ballantane ayimin gorin rashin diyoyi mata,ko wannan gyaran ma atta na saka yayi maka,suma a hakan zasu koya,tunda ko yanzun ma wasu abubuwan sukeyi min,banga abinda diya mace zatayi wanda zai gagari namiji yayishi ba" Dan qaramin miskilin murmushin nan nasa da yafi kama da motsa baki yayi. Abu guda daya tal da yasan ya jima yana ciwa ama tuwo a qwarya shine rashin haihuwar 'YA MACE,shi kuma ya jima da ciwa kansa wani alwashi game da hakan,alwashin da ita kanta bai sanar mata ba har yanzun "Kiyi haquri zan saka a turota tazo ta gyara" kai tsaye ta sake dubansa "Ka wuce ka tafi,kafin ka dawo zan shiga na gyara maka da kaina" kansa ya girgiza da sauri "Karkiyi wahala,zan sake gyaran" "Nidai iya abinda nace maka kenan" ta bashi amsa a taqaice tana maida kanta ga jaridarta. Har ya isa sashen bibi zuciyarsa bata huta da tarin tunani da son gano laifin da nafeesa ta yiwa ama ba wanda har yake shafar SULTANA a wajenta,nafeesar da har tabar duniya bata da abokin fada,nafeesar da har ta gama rayuwarta badai kaji ance an kawo qararta ba,nafeesar da har tabar duniya ko musu bata iya ba bare sa'insa da wani. Laifin nafeesa daya ne LALURARTA indai har lalura da ciwo suna iya zama laifin dan adam......indai har suna iya zama kuskuren mutum da har Allah ya zabi ya dora masa ciwon,banda wannan shikam bazai iya adar da komai ba. Kaf tunaninsa ya yanke lokacin da ya isa dakin sultana din,ya samu masu aikin gidan da su lamira sun cika dakin suna mata magiyar ta fito. Ransa ya baci lokacin da yaga bibi zaune a gefe,itama tayi magiyar tayi magiyar har ta gaji. Shigowarsa kadai ta sanya muryoyinsu daukewa,kowa ya shiga taitayi da nutsuwar sa. Shurun kuma shi ya isarwa da sultana cewa tabbas maina dinne ya shigo,shi daya ke da wannan fitinanniyar kwarjinin dake karya lagon kowa. "Ni wallahi bazanji tsoronka ba" ta fada qasa qasa tana jan qwafa hadi da hararar qofar bandakin tamkar shine tsaye a wajen "Duk ku fita" ya basu umarni yana takawa zuwa bakin bandakin. "Anyi magiyar anyi lallashin amma taqi ta bude,tunda ta shiga take zaune a ciki,kamar wadda ta samu dakin gyatumarta" bibi ta fada hankalinta adan dage tana kallon maina da ya sanya wani dan scissors yana qoqarin warware lock din qofar. Kanzil bai ce da bibi ba. Sultanan na zaune daga ciki,amma tana iya jin kusur kusur dinsa jikin qofar. Sake hararar qofar tayi,don ta tabbatar bai isa yace zai bude qofar ba muddin idan ba itace tayi ra'ayi ta bude ba. Kadawa hantar cikinta tayi sanda taga ya tura qofar ya bude,ya kammala warwareta tas kenan. Tsam ta miqe daga saman toilet seat din tana kallon qwayoyin idanunsa data jima da sanyawa suna da LION EYES,ta fada ta sake fada,a duk sanda yake kallonka irin haka,idanun nasa basa mata kama da idon kowa sai idon zaki sanda yake kallonka cikin fusata,tun ranar da sukaje zoo tace wai ta tantance hakan. Tun su chafa'atu na mata dariya har suma sukayi amannar hakanne. Yadda ya qureta da kallo ya zuba mata ido itama hakan tayi masa,abinda kaf rayuwarsa yafi tsana kenan,kayi laifi sannan ka tsare mutane da kallo kamar sa'anninka?. Duk wani yaro da ya girma ya taso a gidan yasan baya son wannan dabi'ar,sun kuma kiyaye,abinda ya zaunar dashi da su lafiya kenan "Zo ki fita a gurin" ya fada mata a tsawace,tsawar da taji kamar zata tarwatse da kwanyarta,ta gigitatata har sai data kulle idanunta gaba daya hadi da qanqame jikinta guri daya. TSAWA na daya daga cikin abinda ta tsana,saboda muddin kayi mata ita ka gama birkitata kenan. Duk da kafiya taurin kai da zafin zuciyarta kuwa. Idanunsa ya lumshe had'i da budesu,yadda tayi din ya tuna masa da naffeesa,abinda ya sassauta ranshi da zuciyarsa kenan,ya kuma sassauta muryarsa "Fita nace tun kafin na sake kai hannuna kanki" "Taho muje,ya isa hakanan" muryar bibi ta ratsa toilet din. Ita ta sanya hannu ta jawota ta fito da ita daga bedroom din,ya tako a hankali ya biyo bayansu yana sake karantar canjin halaye matuqa daga gareta. Musu,taurin kai,tsiwa,rashin kunya da rashin tsoro "Saketa bibi,ta canza kayanta ta fito taci abinci,kuma wallahi kika wuce minti goma sai na zane miki jikinki,dukan da ban taba kwata yi miki shi ba" ya fada yana juyawa yana fita a dakin. Da jiqaqqun idanunta ta bishi da harara tana jin kamar zata hadiye da zuciyarta "Wai shi me nayi masa?,daga dawowarsa yabi ya takura mutane?,kuma ai da ba haka yake ba,salon muguntar da aikin sojin suka fara koya masa kenan?" Dafe goshinta bibi tayi,gaba daya sultana din ciwon kai takeson bata "Ke bakiga kin canza ba,kin zama mara kunya,ana gaya miki kina musu?,idan akace ki bari ba zaki bari ba,to na godewa Allah da dawowar tasa,shi kadai ne maganinki ai" wani baqinciki ya mamayi zuciyar sultanan,kamar ita za'a ce wai wani zaiyi maganinta?. "Ki gaya masa ya fita a hanya ta to,ai zama yaya da qanwar ba dole bane,kuma bai isa yayi maganina ba Allah,saidai muyi maganin juna" ta fadi tana soma zare kayan jikinta. Zata shirya taje din bawai don tana tsoronsa ba,saidai don kawai bata qaunar duka,bata qaunar abinda zai taba lafiyarta sam,daga lokacin daka saka hannu a jikinta to ta daura da kai kenan,ba ita babu komai,saidai kuma ka shiga uku a gurinta. Bibi tana tsaye har ta gama shiryawa abinta,riga da wando ta sanya,skinny jeans mara nauyi,sai shirt dinsa me gajeran hannu,sako sako lallausar sumarta da tsahonta ke sanyawa saidai ta lanqwasa ta sau biyu tayi,don ribbon din dake kantan saboda bala'in da takeji bata ko tsaya gyarashi ba. Light blue ne kayan,sun yi masifar yi mata kyau,sun haska jar fatarta qwarai,idan ka kalleta zaka dauka ta fito ne daga yankin india ko qasashen larabawa. Tun asali kyan sultana na dabanne,wanda akayi ittifaqin ita daya ce tal ta dauko ainihin kamannin LAILA babar kakanninsu. Har yanzu daidaikun tsofaffi da manyan dake cikin unguwarsu dake tushen jaharsu ta AGADEZ basu manta da LAILA ba,tarihinta bai goge ba,macen data zuba kyau daya banbanta da kyawun kowacce 'ya mace da tayi rayuwa arni guda da ita. A saman kujerun dining din suke zaune,biyu cikin masu aikin gidan na kaikawon shirya abincin daren a samansa. Ysatsunsa cikin na juna,idanunsa
Chapter 3 · 0% Book details