← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 123

Sashe 98

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE Baki Khaleel yabude zaiyi magana yakasa kuka yazomai wuya, baida dauriya ko kadan when it comes to Hawwa, Hawwa tashiga kokarin kwace hannunta tace “nace ka sakeni” make mata kafada yayi Hawwa tace “Khaleel wlh wlh kaji nayi rantsuwa ko bazan zauna dakai bafa, listen Khaleel ni ba yarinya bace, nayi karatu I have a degree, I have masters, I still went ahead naje police school, currently running PHD dina but online, I’ve gathered years of experience from my field of work, I know men like you, narcissist! I’ve come across men like you, I’ve dealt with men like you, forget kama Babana kome kamusu da Ammi na da yan uwana suna sonka, but listen here basu ke zaman auren nan dakai ba, I am the one!” Hawwa tai ihu tace “I am the one in this marriage not them! I know in da ke min ciwo, I know abinda ke damunna, staying in this aure ko barinsa is completely my decision and I’ve decided nagama aurenka as of now, you married me for revenge dama duk wani abinda kakeso ka samu nothing is left, so no point nazaman auren da last last sakina zakayi dazaran ka gama moreni kuma naga ma ai kagama morewan, so ka sakeni Ibrahim I don’t want you! You’re not a husband material, you were never groomed to be a husband so I am out, I don’t want you, kai na tsaneka na tsani mai sonka ma!” Hawaye ne suka sauko daga idanun Khaleel ya lumshe idanunshi da sauri suka zubo suka gangara har gemunshi kirjinshi namai zafi sosai, Hawwa tace “bana kaunarka banama kaunar ganinka, I can’t stand the sight of you plus stink na alcohol danake perceiving a jikinka, Khaleel I hate you kasakeni!”Sake zubowa hawaye sukayi daga idanunshi, Hawwa na kallonshi ganin yaki magana kaman zata rufeshi da duka kawai dan yarike mata hannuwa ne, yanda baiyi magana ba yakara kunnata tace “Ohhkay bazaka sakeni ba?” Khaleel yasake shiru yaki cewa komi, zuciyanta na tafarfasa tace “fine! First thing idan gari yakarasa wayewa I’m going to shari’ah court to file for a divorce idan bazaka sakeni ba kotu zatasa kasakeni, idan kaki kotu zata raba auren!” Kuka dan kufcemai abaki yayi amman yayi maza yarike kallonta yayi cikin ido muryanshi yayi rauni iya rauni ahankali yace “okay!” Muryanshi sounds kaman mai mura tsabagen kuka sai kawai yasaki hannayenta yasauke su yawuce wajen kofa yabude yafice da sauri sauri Hawwa tabishi da kallo sai kawai ta duka tareda zama awajen ta rungume kafafunta tana kifa kanta akan kafafun wasu kalan hawaye na zuba daga idanunta gwanin ban tausayi.Da kyar Khaleel yakai dakinshi yana shiga yamaida kofan yarufe yazauna jikin kofan jikinshi har wani rawa yake ya rungume kafafunshi yafashe da kuka, he loves Hawwa so da baimasan daga ina yafara ba daga ina ya tsaya ba, baitaba tunani akwai ranan dazaizo wai shine ke tsoron sakin wata ba sabida he doesn’t wanna loose her.Har gari yayi haske Hawwa na zaune wajen nan da kyar ta lallaba tashiga bayi tadauro alwala tafito tai salla tazauna akan dadduman tana azkar bini bini tana share hawaye, 7 daidai ta share fuskanta tass ta mike tafada bayi, wanka tayi tafito tashiga closet ta shiga shiryawa cikin wani adire da aka mata dinkin bubu purple ta daura dankwali tadauki handbag tazari purple gyale da flat shoe tafito, babu komi fuskanta banda mai but tayi kyau, skin nata sai wani glowing yake wayanta tadauka takalli screen is 8:00 na safe flat shoe din tasaka ta warware gyalen tayafa tabude kofan ta daidai shima Khaleel na bude kofanshi suka hada ido, jallabiya ce ajikin shi fara daga gani bai runtsa ba idanunshi sunyi jazur sun kumbura, ko 3seconds Hawwa batayiba tana kallonshi tadauke kai kawai tafito abinta tana jawo kofan ba tsoro ko shakka, Khaleel ya tsaya chak yana kallonta hanyar staircase tayi tashiga sauka duk yana kallonta yakasa motsi zuciyanshi nawani irin abnormal bugawa, key motan jiya data bari a falo ta dauka yana wajen yaji tabude kofa tafita, wani irin iska Khaleel ya fuzar kaman wuta sabida zafi yana tsaye awajen yaji ana budemata gate kawai gabanshi yahau fadi, faduwa sosai, yaji jiri na dibanshi, kanshi na sarawa, dasauri yafara taba bango yana dukawa ahankali karya fadi ya lallaba ya danna wani bottun awayanshi saiga Salman yashigo dakin dagudu yace “Yallabai” yakirashi da karfi yana kallon ko’ina a falon shiru sai kawai yawuce sama ganin Khaleel gaban dakinshi akasa yasa yayi wajen dagudu yace “Sir I saw your emergency alert meke damunka”?Khaleel nawani irin nishi kaman mai shirin mutuwa yace “bring car nan banson su Momy su ganni, take me to My Doctor in our hospital” arude Salman yace “okay okay, Sir you will be okay kaji nothing will happen to you” Salman yatashi da gudu yafita waje mota yatada da kanshi yakawo har gaban flat nasu yashiga ciki yawuce sama a sume yasami Khaleel a shimfide awajen hannayenshi duka biyu a saman kirji kaman ya mutu.EPISODE Cikeda jarumta Salman yadaga Khaleel chak yafice dashi yasashi abayan mota yashiga gaba yaja motar sukabar gidan….Kusan 40mins drive yakai Hawwa shari’a court, shiga tayi tai parking motan a parking space tayi shiru tana kallon ko’ina saikuma ta kifa kanta tafashe da kuka sosai kusan 5mins tana abu daya sai kuma ta dago fuskanta ta sauke mirror tana goge fuskan tace “why am I even crying sabida Khaleel sai kace sonshi kike? In the first place auren gambling yayi da ke yanuna miki he can acquire kome yakeso he’s a rich kid” gyale tasa ta gyara fuskanta saita dauki bakin glasses din tasaka tabude kofa tafito tashiga ciki tabiya kudi ta karbi number itace number 3, kusan 10min tana zaune akakai kanta tashi tayi tashiga office din wata dattijuwan matace sanye da hijabi looking very decent and modest, glasses Hawwa ta zare daga idanunta tace “good morning” matan tabita da kallo tana nunamata chair ta zauna tace “me kikeso?” Dan kallonta Hawwa tayi saikuma ahankali tace “inaso nai filing divorce ne, mijina yaki sakina” anatse matan na jawo wani drawer tace “can I know your reason?”Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma tai shiru matan ta kalli Hawwa tace “idan bazaki iya bamu dalili mai kwari ba kotu bazama ta dauki karan da kika kawoba balle harmu mishi sammaci” cikin wani irin murya kaman na marainiya Hawwa tace “uhmmmm ban…..bana sonshi ne” cigaba da jawo drawer matan tayi tace “auren dole aka muku ne? How long da aurenku yanzu? Sannan mesa baki sonshi? Tun yaushe kika daina jin sonshi tun dane ko yanzu?” Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma ta runtse idanunta kuka na neman kufce mata tadan fuzar da iska sannan ta kalleta tace “dole saina amsa all this tambayoyin nan? Ni yar sanda ce, I think bana sonshi alone is enough reason na nemi kotu taraba auren cus islamically ya halasta” Hawwa tadanyi shiru chan tace “Ma’am can you just tell me how to go about it batare da all this questions dinba kawai banson Khaleel” sosai matan ke kallon Hawwa sai kawai tace “okay” tazaro wata paper tayi signing akai tasaka stamp tace “fill this form ki bani nasake signing da stamping then it’s done idan har yanzu a gidanshi kike zamu baki takardan sammaci ki bashi da kanki idan ba’a gidanshi kikeba maybe kina gidan iyayenki zaki bamu adreshin sa ko inda z’a sameshi akaimasa” tabama Hawwa paper hakanan sai hannun Hawwa datakai zata karbi paper yashiga rawa sosai matan tabi hannun Hawwa da kallo, da kyar Hawwa ta iya karban takardan Matan tabata pen Hawwa ta tsaya tana kallon pen din takasa karba matan tace “karba mana” ahankali Hawwa tasa hannu ta karba hannunta yashiga rawa sosai zata fara rubuta a paper takasa wlh, duk matan tana kallonta kusan good 3mins Hawwa takasa saka ko A akan paper ahankali tadago kanta takalli matan tace “I need a moment please zan iya fita na cike a waje saina kawo?” Gyadamata kai matan tayi tace “sure tashi kije” ahankali Hawwa ta tashi tafito tawuce parking space tabude motan ta shiga ta zauna tarufo kofan takai pen kan takardan still takasa rubutu what is wrong with her? Idanunta sukai jazur, knocking motanta akayi wlh saida ta zabura dasauri ta juyo Baban Yaseer tagani yana sanye da wata faran shadda mai kyau ya kafa hula akai yayi kyau faduwa gabanta yayi ganinshi dasauri ta ijiye paper da pen a jaka tai maza ta gyara gyalenta tana kara rufe wuyanta da kirjinta da kyau like matan aure tasauke glass na motan kasa, murmushi Baban Yaseer yamata yace “Hajiya Hawwa rai kanga rai” adan kunyace cikeda jin nauyin sa tace “ina yini Baban Yaseer” anatse yace “Alhamdulillah ai tunda naji kinyi aure bansamu mun hadu namiki Allah ya sanya alkhairi ba, ai tundazu dayake nazo ne Boss dina ya aikoni nazo nasami yarsa anan na karbi this” yanuna mata wani file dake hannunshi yace “na karba zan shiga mota kenan sai gaki kin fito kin shiga ciki baki lurada ni ba, this is my car” yanuna mata motanshi dake next to nata yace “shine na tsaya na jiraki dole mu gaisa” dan gyadamai kai Hawwa tayi anatse tadan sauke kanta tace “yaya su Yaseer Da Yasmeen da Maman su?” Murmushi Baban Yaseer yayi yace “Hawwa kenan wato ko banjin za’a taba samun mace mai halinki aduniya ba, ace duk abubuwan da Ni’ima tamiki you are still asking yatake” yayi murmushi yace “anyways mijinki yasa an fito da ita daga prison bayan sati daya bayan tayi signing undertaken if anything yasameki in the next 5years itane, an mata iyaka dake wai ko layinku takara zuwa za’ayi inviting nata for questioning cus basu da yan uwa alayin, bata baki, toh shine fa su Mama da Yan uwan marigayi Babanta da iyayena sun shiga maganan na yafemata sabida yaranmu wlh, so she’s at home waiting for license nata da har yanzu basu dawo mata dashi ba and it serves her right, alhakin ki ne” shiru tayi Hawwa batace komiba, Baban Yaseer sai kallonta yake kaman zai hadiyeta da idanu, kasa daurewa yayi yace “why are you here? Me kikazo yi a sharia court?” Yake Hawwa tamai tace “ahhhhh, abu……Abu nazo amsa” gyadamata kai Baban Yaseer
Chapter 98 · 0% Book details