← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 123

Sashe 50

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

aiki dawani kudi zaki dinga ci ga Aliyu yaki kulamu?” Murmushi tama Mama tace “inada yan kudi kuma kudi bazai taba gagarana ba saidai in ba Hawwa aduniya, don’t worry Mama” ijiyan zuciya Mama tasauke but ranta babu dadi Ni’ima ta tashi tashiga daki ta chanza kaya zuwa abaya tafito Mama tace “ina zaki?” Murmushi tayi tace “gidansu Hawwa” dasauri Mama tace “suka koroki fa?” Dan murmushi tayi tace “Mama kibar mafarkin nan saina dawo kawai”. Hawwa da Ramla nafita, Baba da Aminu suma suka fice zuwa bank kai gold, Ni’ima na shigowa unguwan tai parking motanta taji dadin yanda bataga Baba ba, ijiyan zuciya tasauke takalli fuskanta ta side mirror ganin komi daidai yasa tabude kofan tafito tashiga gidan da sallamanta Ammi ce kadai a tsakar gidan tana wanke kayan Hawwa dana Ramla taga Ni’ima that’s the last person datai expecting taga agidan nan tsayar da wankin datakeyi tayi, Ni’ima ta shiga shigowa tana tahowa har inda Ammi take, babu wasa kan muryan Ammi tace “me kikazo yi agidan nan?” Dan murmushi kadan Ni’ima tama Ammi ta duka gabanta takai hannu zata karbi bahon wankin tace “kawo kayan na wanke miki Ammi” kul! Ammi tafadi azafafe dayasa Ni’ima ta tsaya chak, ahankali tace “Ammi kin shararamin mari haryau inajin zafin hannunki a kan kunci na baki hakura?” Ammi na kallonta tace “tashi kibar gidan nan I don’t want to talk” ahankali Ni’ima tace “wajen Hawwa nazo wannan dabanganta ba nasan batanan bari naje nazauna najirata” tawuce tadauki kujera tazauna a tsakar gidan Ammi tabita da kallo sai kawai ta dauke kanta yacigaba da wankin datake bata sake cemata uppan ba. ** Faduwa gaban Hawwa yayi jin abinda Khaleel yace wanda har saida yagani yanda ta tsorata hakan yamai dadi kawai yadauke kai Hawwa ta kadakai cikeda karfin hali tace “ka gwada kaini hotel kagani!” Tai kwafa kawai tadauke kanta ta jingina da kujera tana zancen zuci, ada kafin tasanshi kamshin turarenshi namata dadi yanzu ko dazaran taji kamshin yana reminding nata of yanda takejin haushin sa da tsanan sa da kinsa, sunyi kusan 30min tafiya sannan sukakai wani building dataga an rubuta The couples dream world aka bude musu gate suka shiga parking sukayi wani babban mutum yafito sanye da suit zuwa wajen motan driver yafito yabude ma Khaleel tunda ba Salman yafito Hawwa naji tsohon na cewa “welcome to The couple dream world Sir, we are so honored and pleased to have you” dan gyadamai kai Khaleel yayi yajuyo tareda leko motan yamika mata hannu yace “Police girl mun iso hotel din let’s go” hannunta tasa ta kabar danashi azuciye tafito daga side nata da aka bude mata tazagayo tsohon yakara bowing yace “welcome to the couple world Ma’am” dan gyadamai kai kadan Hawwa tayi ranta abace, Khaleel yace “after you” gaba mutumin yayi shikuma ya matso dab kusa da Hawwa bata ankaraba taji yakama hannunta hade hannuwansu gam yayi Hawwa takalli hannun tashiga kokarin kwace nata tace “cikamin hannun” make mata kafada yayi kawai yajata, duk yanda Hawwa taso ta kwace hannunta takasa Khaleel sai tafiya yake abunshi driver yabisu da kallo dasauran mopol nashi, yau shakara kusan ashirin ina aiki dasu bantaba ganin Oga yayi kyau dawata kaman yar sandan nan ba, they look so great, Allah kasa itace sanadiyan gyaruwansa” shiga ciki sukayi Hawwa taga kayayyakin amare ne da ango ajere kaman irin su veeke james dasu xtrabrides datake gani a IG irin wajen ne, yana jerawa da ita ahankali batare daya kalleta ba yace “banso ki dinka bridal dress dinki da kanki kinji yarinya!” Yadan kalleta dauke kai Hawwa tayi, Khaleel yace “I want them to do it for us” murya kasa kasa itama Hawwa tace “dazakaji nawa dabaka kashe kudin nan ba cus they will be no any wedding” office aka shiga dasu dasauri wata yoruba woman ta taso dasauri tace “welcome Sir” kawai ta rungume Hawwa tace “welcome Ma’am, you guys makes a very very lovely couples congratulations”. Mshakur
Chapter 50 · 0% Book details