Sashe 42
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
ganin Ni’ima ma azaune a compound din yasa sukace. “Ayiririri ga Babban kawan Amarya, yoo ba dole aganki yau ba ana daura auren kawarki labari yabaza gari anachan ana rabon kudi” daga Mama har Ni’ima confusion look suke musu ita Ni’ima ma bata magana Mama da gabanta yashiga fadi tace “wace kawar Ni’ima kuke magana akai Jamila?” Dasauri Jamilan tace “kaji Maman Ni’ima kuma, tsufa kika farayi ne? Ni’ima nada wata kawa data wuce Hawwa ne? Hawwa yar sanda mana yar wajen Baba gurgu muke magana gashichan an daura aure ana biki a unguwansu sai tafiya ake layin nasu” atare daga Mama har Ni’ima suka kalli juna Ni’ima tabuga wani ihu tana mikewa tana daura hannu aka. “Wayyooo na shiga uku na lalace, na bani, Mama na bani” dan duk atunaninta Baba ya aurama Baban Yaseer Hawwa tunda tamusu rashin mutunci dazu, ahaukace Mama taja hijabi daga igiya tace “sa hijabi Ni’ima muje zama bata ganmu ba, dena ihu kidau makullin mota sabida muyi sauri” su Jamila da mamaki da confusion suke kallonsu Hijabi Ni’ima tasaka ko silipas bata tsaya sawa ba suka wuce su Jamila suka fice daga gidan babu zancen kulle gidan ma ta shiga mota Mama ma na shiga suna tada aiko Samari sai gudu suke kaman ranan idi ana tafita layin koda sukakai tundaga bakin titi an cika tap parking motan tayi agaban wani pharmacy suka fito da karfin yaji da balam bala’i suka shiga kutsawa cikin mutane har zuwa cikin layin daga inda security suke tsaitsaye da bindigogi suma suka tsaya suna kallon Baba tare da wasu manyan mutane suna magana suna gaisawa, sosai Ni’ima ke kallon fuskan kowa one by one bataga wanda tasani ba chan idanunta ya yasauka kan Khaleel da she’s sure shine wanda tagani dazu daidai wasu gayu dake tsaye dasu sunahau gisting.“Kai Baaba shinefa yaron Senate President shi kadai mutumin ya haifa, just farkon shekaran nan Forbes sukace baban shine number 5 richest man in the whole world, wai bakasan Mangal BeWeeCee ba?” Daga Mama har Ni’ima dakejin hiran faduwa gabansu yashigayi cikin karaman murya Mama na whispering tace “ke Ni’ima ba Baban Yaseer ta aura ba kinaji ana maganan Alai Mangal” daidai lokacin gayun dame bada labari yace “sadakinta Miliyan Hamsim da Darhamin gwal dari fa kai Baba gurgu da yarsa sun gama da talauci har abada, talauci bye bye” sake faduwa sosai gaban Ni’ima yayi, daga motan Baban Yaseer har gidan nasu da dan albashinsa 350k networth dinshi gabaki daya baikai sadakin Hawwa bama Innalillahi wa Innailaihi raji’un.Gayun sukace. “Mangal din fa yabama masallaci miliyan dari a gyara, sannan yabama anguwan miliyan dari wai arabama kowa babba da yaro, tsoho da tsowuha sabida sun bama dansa yarsu, kai Baaba yauna kara yarda wani jinkirin alhairi ne, yaushe su Gwaggo suka gama Gulmanta agidanmu ranan da safe kan Hawwa ce kadai yarda batai aure a unguwan nan ba Kannin kannenta sunyi aure amman gashi yau dalilinta kalli anguwan mu yatashi da miliyan dubu dari biyu ba in total, Allah kaimana arziki!” Sake faduwa sosai gaban Niiima yayi yana wani jigijim! Jimdum! Dumjum! Dumdum! Lankwashewa kafafun Ni’ima yayi tai baya zata fadi Mama ta tareta tana salati sun shiga shock, dasauri Mama tace “kinga gobe zanje asibitin nabama su Baba hakuri da Hawwan Ni’ima, kokin hanani billahilazi sainaje, nine mahaifiyar babban aminiyan Amarya ko miliyan goma Alhaji Mangal yabani mena manta tuni zanja jari, jari, gobe da safiyan Allah zani ko asibiti ko nan gıda duk inda suke! Allah yasa banwani mata magana mara dadi ba kuma nasan ba lallai tafadi ma tazo wajena ba, gobe zanje na sasanta komi na shiryaku nasan da gudu zata karbeki da gudu ayanda Hawwa ke miki soyayya, gaba zuciya tuni anyi an wuce, kawancen shekaru ashirin da yan kai, Ni’ima ina chan zan kiraki kizo kibada hakuri! Goben nan zaku shirya!”.