Sashe 53
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
love you too kaman yanda sukeyi da saita kasa furtawa murmushi tamata ahankali mai taushi tace “thank you agaida Mama” juyawa Ni’ima tayi tayi zaure tana tafiya ahankali hoping Hawwa zata kirata ko agogon nan ne tabata amman taji shiru tace shikenan Hawwa ta chanza ba haka Hawwa takeba da ba, ko waya Hawa tasaya zata iya sadaukar mata amman yau ko kudin ma datace batada su Hawwa bata bataba, ga gifts tagani but Hawwa couldn’t give her a thing.Komi Hawwa ta kwasa ta shiga daki da sallama Ammi ta kalli Ramla tace “fita zanyi magana da Yayarki” fita Ramla tayi ganin yanda ran Ammi yabaci tana fita Hawwa tayi wajen Ammi dasauri tace “Ammi dan Allah kiyakuri yazanyi I have to talk to her amman naji maganan ki bazan maida ita kawata kaman d’a ba!” Kabar da hannunta Ammi tayi daga jikinta cikin tsananin fushi tace “you are very very very stupid Hawwa!”Dasauri Hawwa ta kalli Ammi dan bata taba zaginta ba, rai abace Ammi tanuna kanta tace “is something wrong with your brain? I expected you kice kinji kin yafe let’s end things kaman yanda ita tai initiating at first ki sallameta but kin tsaya kina hugging Ni’ima are you mad?” Baki Hawwa tabude tace “Ammi wlh bah……” “yimin shiru!” Ammi tafadi tana mata ihu, Hawwa tayi shiru tasauke kanta kasa Ammi tace “imagine kun fita keda mijinki yabaki gifts wannan kawar kike nunamawa har tana tayaki karanta note din da mijinki yarubata miki, you are telling her zaki ma Oganki magana kan licence dinta, zaki tayata kiran Baban Yaseer what is your business with Ni’ima and her affairs sai Ni’ima ta kasheki zakisan ta tsaneki ba kawar arziki bace?”Ammi tai ihu she don’t care at this point uban kowa yaji Baba yashigo dakin yace “da kyau Zainabu wanke miki ita tunda kunnen kashi gareta” Ammi tace “Uwarki ce Ni’ima ko ubanki da bazaki iya hakura da ita ba can’t you leave with out her? Wlh kika kira Baban Yaseer kokikai magana kan licence dinta sainayi mummunan saba miki, Hawwa kika kara jawo Ni’ima jikinki wlh saina zame hannuna a lamarunku tunda ke kinsaka differentiating good people from bad, you’re a criminologist but kin kasa karantan Ni’ima kisan criminal ce ita all she’s doing dake is friends with benefit bata taba sonki ba, yau tazo wajenki sabida tasan u might be able to get her licence back for her, tasan mijinta na sonki kina karansa kika cemai yadawo da Ita zai dawo da ita, this gurl has been benefiting from you right from day one, Ni’ima tafi kowa cin albashinki saitaci tarage sauran mu yan uwanki kike rabamana” Ammi bambami takema Hawwa bana wasaba, tace “yanda kike kashema yaranta kudi kanninki da yaran kanninki basu samu haka daga jikinki suci, duka abinda kika mata arayuwa bai hana rana daya ta kwance miki zani a kasuwa ba ta zagi ubanki ta zagi uwarki ta goranta miki yanzu shine still kike neman goyata abaya kiyi Allah baki sa’a nina tafi zaria nafasa kwana gidan nan, Ramla zoki hada kayanmu mutafi”Dasauri Hawwa tarike kafanta tana girgiza kai tace “Ammi dan Allah kiyakuri” Baba shima yace “Zainab yakuri yamma tayi bani barinki kishiga hanya yanzu” kaman Ammi zatai kuka tace “Malam Hawwa na batamin rai, tana bakantamin rai, haba haba dan Allah gamai sonta ta tsaya tana gayamana mashayi ne menene menene, ga mara sonta takasa ganewa binta take ido rufe kaman makauniya,ana nuna mata gaskiya tana kulle idanu ina dalili kasheni takeso tayi da bacin rai da takaici nagayamaka bazan kwana ba Malam” Baba shima cikin masifa yace “shikenan kin batama mahaifiyar ki wacce ita kadaice bata fushi dake aduniya rai, matarnan ni da ita bama hammata iska muke akanki sabida yanda bataso ina fada akanki ina damunki, jibi yanda kika bakanta mata rai yau Hawwa kinji dadi ko”? Tashi Hawwa tayi sai kawai ta rungume Ammi tafashe da kuka tace “Ammi dan Allah kiyakuri trust me I don’t consider Ni’ima my friend anymore and namiki alkawari bazan kara bari tasan sirri na ba kawai tabani tausayi ne somehow I feel responsible for her situation and condition da Baban Yaseer baiyi all abubuwan nan ba da yanzu suna tare abinsu but bazan karaba kiyakuri Ammi na forgive me dan Allah” shiru Ammi tayi saikuma ahankali tace “naji nahakura ya isa, kawai abin namin zafi arai ne yanda kike yunkurin dawo da makashinki rayuwanka” Baba yace “Allah ya kyauta ai ta kuskura tai haka saitaga bacin raina” ahankali Hawwa tace “bazanyiba Baba” wucewa Baba yayi yafita Hawwa takai Ammi gado ta zauna sai kawai ta kara rungume Ammi, ahankali Ammi tanuna mata wasu shopping bags tace “kinga abinda Ramla tayi taga opportunity” dan murmushi tayi kadan tace “yarinya ce Ammi” ahankali Ammi tace “ina kukaje?” “Wani shagon dinki aka aunani hmm” ta tabe baki Ammi tai murmushi tace “muga abubuwan”.