← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 123

Sashe 111

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE Mom tai murmushin jin dadi ganin yanda yaronta yatafi, Baba da Ammi ma sunji dadin abinda Khaleel yayi Excellency ne cikeda so yace “it’s okay Hawwa na, he will come around, je flat naku kihuta I want to talk to your parents” gyadama Excellency kai tayi tamike tsaye ahankali tana tafiya da kyar tasa hannu tabude kofa tafito, da hankali da hankali take tafiya har zuwa side nata tabude kofa tana shiga tawuce carpet na tsakiyan falon kawai ta kwanta tana kuka mai radadi da soya zuciya.Kallonsu Baba Excellency yayi yace “daga Khaleel har Hawwa duka yarane, duk mu bisu a sannu muna correcting nasu, shima Khaleel din bawai he’s innocent bane, duk matsalan shi ta haddasa wannan fadan, d’ana na shaye shaye” Excellency yafadi ahankali there no point aboye an zama daya yanzu, daga Baba har Ammi suka kalleshi dan basu dauka zai iya fadin kalan maganan ba, ahankali Excellency yace “duk laifi nane inason Khaleel da yawa da nakasa gyara kuskuren shi but namuku alkawari komi zai chanza daga yanzu zamu tsaya tsayin daka akanshi ya gyaru”Excellency yace “kuma dan Allah Malam da Hajiya kada ku kara tabamin yarinya kuka kara dokanmin diya shari’a zanyi daku sosai” dan murmushi both Ammi da Baba sukayi Ammi tace “diyar taka akwai taurin kai ne amman za’a kiyaye harda fushi” Excellency yace “ga abin doka Khaleel ba’a dakaba sai iya” Mom ta tashi kaman ba itaba anatse tace “ko ruwa ba’a baku ba” shi kanshi saida Excellency ya kalli Mom but harta wuce Excellency yakalli su Baba yace “kar maganganun da Zainab tayi yasa ku dauka Hawwa zata wahala ko zata takura mata bar Zainab da masifa amman batada mugunta, abu kadan Hawwa zata iyayi ta sace zuciyanta” Baba da Ammi sukai murmushi saiga Mommy tareda ma’aikata dasuka dauko hadaddun ubansun trays dake dauke da drinks da ruwa da kulolin abinci da su fruits duk aka ijiye a tsakar falon Excellency ya sauko yace “bismaillah Malam” Mom ta kalli Ammi ahankali tace “ni banson bakunta fa” Ammi cikeda raha tace “kikazo gidana Allah sa kada kiyi” Mom ta sauko Ammi ma ta sauko suka shiga hira da Mom har tana tambayan Ammi garinta suna hira sosai kaman ba fada yaransu suka gamayi ba sai wajajen shabiyu sukace zasu tafi har waje su Excellencu suka rakosu Ammi tace “bari taga Hawwa” tawuceHawwa na kwance akasan Ammi tabude kofan dakin ta shigo tana kirne fuska Hawwa na ganinta ta tashi zaune da sauri tana goge fuskanta Ammi tayi kaman bataga tana kuka ba, tace “abu daya nazo gayamiki kije tiktok ko IG kiyi searching M Shakur ki shiga class dinta na Kissa training da Intimacy ki koyi yanda ake abubuwa, idan zaki zage damtse kiyi zaman aure kiyi Hawwa, ga mijinki nan yayi fushi dake, tun wuri kafin dare yamiki kisan yanda zakiyi ki lallaba ki shawo kansa ku shirya, ni natafi zaria bazan kara dawowa Abuja sabida kin tapka hauka ba kome kika shirya yi kiyi, duk abinda zakiyi ki tabbatar kinyi kin shawo kan Khaleel kafin ya tsaneki da gaske” Ammi tayi kofa daidai zata fita taji Hawwa ta kama mata hannu dasauri Ammi tajuyo sai kawai Hawwa ta rungumeta tama kasa magana kuka kawai take jikin Ammi, ga jikinta yayi zafi, Ammi na so ta karaya but ta tuna this is the same thing she did jiya ta tausaya mata tahakura amman da safiyan Allah tayi shirmen dayafi na jiya so taji ajikinta, cireta kawai tayi daga jikinta tajuya abinta tafice tarufo mata kofa Hawwa ta tafi wajen window taga su Ammi sun shiga wata mota daban da yaron daya kawosu sun tafi.EPISODE Komawa Hawwa tayi tasake zama sai kallon kofa take jira kawai take Khaleel yashigo ahaka wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, tana cikin bacci taji motsi dayake batai nisa a baccin ba da gudu tabude idanunta Khaleel tagani awajen kofa yana fita dawasu manyan akwatinan shi na LV guda biyu, mugun faduwa gabanta yayi da gudu ta tashi kirjinta nawani irin bugawa tayi wajen kofan tace “Khal…..” mugun kallon daya mata yasa takasa karasa kiran sunansa kawai yaja kofan ya kulle yawuce abinshi, Hawwa tayi wajen window dagudu tadaga labule taga flat dinsu yashiga da akwatinan sai kawai taji kuka yazo mata saida taji ana salla ta iya barin wajen tawuce dakinta bayi ta shiga tayi alwala, tafito tazauna kan dadduma tayi salla ta kwanta akan dadduma tana wani kalan sauke ijiyan zuciya her heart is so heavy kaman an daura mata manya manyan duwatsu, takasa cin abinci takasa bacci sai kuka har bayan sallan isha da kyar ta tashi tajawo wani first aid box taga PCM tadauka tasha ta mike ta tsaya tsaye wajen window ta tana kallo babu Khaleel a compound din, ina yaje? She’s missing him, wayanta ta dauka ta zauna bakin gado tai dialing number shi saitaji ana cemata number shi bayama kan network gabaki daya ijiye wayan tayi ta tashi tafada bayi da kyar tai wanka tafito tasaka wani sexy rigan bacci ta feffesa turare sai kawai tawuce ta tafi dakinshi tabude ahankali everything smells like him, zama tayi abakin gadon ahankali tana kallon gadon tana tuna how happy Khaleel use to be, his full smile yana kallonta, his loving eyes, his erotic talks, his sleep, yanda yake kankameta, yanda yake bacci ajikinta, yanda yake tashi da kyar, the way yake amsawa ummm idan ta tadashi, the way he acts like a baby, the way he dances for her, the way yake tsokanan ta, the way he calls her Kulu, Yar Sanda, muguwa menene menene, bata taba sanin she loves all the moments ba sai yanzu, like she will give anything just to experience those moments one more time yanzu, hawaye masu dumi taji yana bin hancinta yana diddiga ta tip na nose nata yana sauka a hannunta dasauri ta share da bayan hannu kaman mai mura cikin wani irin murya na ban tausayi da nadama da dana sani tace “I am sorry Khaleel!” Sake goge hawayen tayi tace “I really am, I’m badly sorry Khaleel, I miss you, I missed everything about you, please come back to me kayakuri” tayi maganan tana kwanciya ta kifa kanta jikin pillow dinshi Hawaye na gangarowa daga idanunta tana kallon kofan tamika hannu tadauki pillow daya ta rungume a kirjinta tana kallon kofa har 2 nadare takasa bacci ta tashi taje ta dauro alwala tadauko hijabinta tadawo dakin tai salla har four sannan bacci ya iya kwasheta akan dadduman.Ahankali take iya bude idanunta ganin gari yayi haske yasa ta kalli wayanta da sauri taga 7:45, Subhanallahi tafadi da sauri ta tashi tashiga bayinshi tadauro alawala tazo tai salla ta idar tai azkar ta karatu ta gyara dakin tass ta kunna turare tawuce bayinta tai wanka har yanzu idanunta a kumbure closet nata ta shiga tasaka wani atampa riga da skirt dakeda red ajiki batasa komi a fuska ba tafito tasauko kasa kitchen ta shiga tayi tea a cup tafito tazauna tana kallon tea din wlh takasa sha sai kawai ta tashi taje kitchen ta ijiye tasa marfi tarufe tafito takoma sama ta shiga closet red mayafi ta dauka babba tayafa tafito tasauko kasa, crocks dake nan kasan falon na Khaleel tasaka tabude kofa tafito tana tafiya ahankali tawuce side nasu Mom.Gently tabude kofan da sallama a bakinta ta shiga ciki Momy ne kadai afalon ga plate na fruits tanaci cus yanaci fruits take faraci dasafe idan Excellency na gari tana breakfast da wuri but jiya da night yatafi France saisa take breakfast ita kadai ga ma’aikata a dinning na jera warmers, kallo daya Mom tama Hawwa ta dauke kai tacigaba da cin fruits abinta, dudda gaban Hawwa na fadi but har gaban Mom tazo ta duka ahankali tace “ina kwana Mom” dauke kai Mom tayi kaman bada ita take magana ba chan tace “lafiya” shiru Hawwa tayi still tana gabanta chan tace “Mommy dan Allah kiyakuri kiyafemin kinji Mom” kallonta Mom tayi tamata wani banzan kallo tace “tashi agabana” ahankali Hawwa ta tashi, gently tawuce wajen dinning saikuma tawuce kitchen, 3workers ne ke aiki an riga an gama breakfast na Mom dasauri suka gaida Hawwa. “Good morning Ma” gyadamusu kai tayi ahankali Hawwa tace “me kuke dafawa” babban ma’aikaciyan tace “an gama breakfast na Madam, tace ama Mr Khaleel kunu da akara shine zan fara yanzu” Dasauri Hawwa tace “ki barshi zanyi” batama jira amsan su ba tace “ina wajen wake? Da gero”?EPISODE Dukansu suka nuna mata store sai kawai tawuce store ta debo wake da geron kunu tafara aiki sukace mezamuyi tace “no karki damu, kawai zan dinga tambayanki unda abubuwa suke” tafara aiki she will do everything in her power to win Khaleel’s love back.Kunu tashiga yima Khaleel, Mom na zaune a falo kusan 30min saikuma ta juyo badai yarinyar nan taje tana taya yan aiki yin aikinsu ba, juyowa tayi but bata ma iya ganin kitchen daga wajen, tashi tayi ahankali rike da empty plate na fruits nata tazo wajen kitchen din duk basu ganta ba turus ta tsaya tana kallon Hawwa dake buga kosai yan aikin sun zazzauna suna kallonta, yaune rana na farko da Momy ke ganin Hawwa babu mayafi dan ta rataya gyalen a kofa tana aiki gaskiya yarinyar is very very beautiful she cannot even lie and she’s tall and very pretty dan kitson datayi dan ya zubo a bayan wuyanta kuma gashinta da tsayi, tai shiru kawai tana kallon Hawwa somehow she’s seeing why yaronta ke sonta, Hawwa kaman taji ajikinta ana kallonta juyowa tayi ganin Mom yasa gabanta yafadi da sauri ta ijiye bowl din ta taho wajen kitchen din bayan taja gyalenta daga kofa ta yafa cus is her own way of showing iyayen mijinta tana girmama su, yan aikin na tashi suma dasauri, ahankali cikeda respect Hawwa tasa hannu takarbi empty plate dake hannun Mom, cikeda girmamawa tace “Momy kina bukatan wani abune namiki?” Tsayawa Mom tayi tana kallon Hawwa shekeke sabida mijinta yayi yaji itama tazo tawani biyoshi nan, saikuma cikeda masifa tace “me kikemin a kitchen nina aikeki”? Kanta na kasa tace “Momy kiyakuri kosai zanmai” dariyan takaici yakusa kufcema Mom tace “eh kin iya kosai amman baki iya kulamin da yaro ba mara mutunci kawai, kinaso ki kashemin
Chapter 111 · 0% Book details