← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 123

Sashe 16

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

anjima zanje kasuwa nadan sayo kayan abinci bye” Ni’ima zatai magana Hawwa ta katse wayan da sauri chan saiga messege tace “thank u Best, I love you, yaranki suma sunce Allah amfana”.Murmushi Hawwa tayi batare datayi replying message dinba ta tashi tawuce wajen basket din tabude tana ciro wasu materials datariga ta yanka ta warwaresu akasa sannan tadauki wani ta hau kan keken tana saita zare tahau dinki, yawanci dinki yanasa tana mantawa da damuwanta, tana cikin dinkin akai sallama wani yaro yakawo mata makullin mota inji Baba ta leko ta amsa.Sai bayan tayi la’asar sannan ta shirya cikin wani black abaya mai kyau sosai ta daura gyalen asaman kanta batare datai rolling ba, tadauki handbag da wayanta da car key tafito kaganta zaka dauka yar mai kudi ce tanada expensive body, fitowa waje tayi Baba yace “ina zaki”? Ahankali tace “zandan karo kayan abincin gidan ne Baba an biyani bonus, zan kuma siyo landing da zaren dinki ina dinka wasu kaya ne banda abubuwan dinki” jinjina mata kai yayi yace “to saikin dawo Baban Yaseer ya aiko da motan ki dazu” gyadamai kai tayi tawuce wajen motan nata dataga an wanke har ciki yayi tsaf tsaf yana kyalli tabude ta shiga tanabin motan da kallo dataga an samata turarukan mota masu bala’in kamshi harda wani expensive car diffuser, murmushi tasakeyi ta shiga tada motan yan anguwa sai kallonta suke inda sabo ta saba tai reverse ta juyo sannan tafice daga anguwan kasuwa tafara shiga tasayo buhun abinci dasu jarkan mai akasa mata a boot sannan taja motan zuwa wani super market dake wuse 2 mai shegen kyau yawanci anan take samin wani botura masu kyau foreign datake sawa gaban shirts dinta na zuwa office.Parking tayi tabude motan tafito tana rike jakanta a hannu tanajan gyalen gaba sabida yanda gashinta ke fitowa gashi kitson yadanyi tsufa, maida kofan tayi tarufe tama motan key sannan tai ciki tana tafiya ahankali one step at a time harta shiga tafara duba wajen supplies din kayan dinki duk abinda take bukata saida ta dauka sannan tabar wajen tana tafiya ahankali rikeda basket din datasa abinda tasayo ciki, wajen shelves na books ta tsaya tana daukan novels tana duba authors din cus tana karanta English novels sosai kamshi mai bala’in dadi ne ya daki hancinta daidai ta dauki wani novel abin har saida yasa takai novel din hancinta cus she was curious an fara scented novels ne? Jin ba novel din ke kamshi ba yasa ta janyeshi daga hancinta, she don’t want to look stupid but wlh kaman tajuya ta nemi mai kamshin and ask sunan turaren cus she loves the scent, tana tsaye awajen kaman daga sama taji an rungumeta ta baya. “FAA yayyyy!” Adan tsorace Hawwa ta juyo dan har saida gabanta yafadi jin yanda muryan little girl an kuma riketa atare, da sauri ta juyo daidai Noor ta saketa tana dagowa tana wani irin murmushi tana kallonta, kyakkyawan yarinya ce tana sanye dawani half gown, kallon yarinya Hawwa tayi sosai from facial expression dinta kasan bata ganeta ba saikuma tabi gabanta da kallon ko zataga iyayen yarinyar, ganin maza tayi su hudu wanda tana ganinsu tasan bodyguards ne, hannunta taji an kama dasauri Hawwa tadauke kanta daga kallon bodyguards din takalli yarinyar dake murmushi sosai tana washe baki tace “I can never ever and ever forget your face Anty, Anty you don’t remember my face”? Ahankali Hawwa ta duka tana kallon yarinyar that is so beautiful and the way she talks is so adorable tace “Hi cutie” still trying tagane yarinyar dasauri Noor takai hannunta goshi tace “oh noo, I’m Noor Ibrahim Khaleel Mangal, and you saved me, your are my fairy angel Anty FAA” zaro daradaran idanunta Hawwa tayi tace “Ohhh Noor I’m sorr……” bata karasa magana ba Noor ta matso tareda manna mata peck a goshi tace “Noor loves Fairy Angel Anty, come and see my Dady” yarinyar tayi maganan tana kama hannun Hawwa data tashi da sauri awkwardly tace “uhm Noor, no….” jan hannunta da karfi Noor tayi tace “please, please please FAA, yanzun nan Dady na yafita yayi waya” yanda bodyguards din suka wani bude musu hanya yasa ba yanda ta iya tabar basket na abubuwan dazata saya awajen tabiyota suka fito waje Noor tarike hannunta gam gam kaman za’a kwace zuwa wajen wata arniyan customize Maybach dake pake a tsakiyan motocin mopol guda biyu gawani lafiyayyen bodyguard tsaye gaban motan dayana ganin Noor yabude bayan motan, tana zuwa wajen motan batai wata wata ba tasaki hannun Hawwa data tsaya awkwardly tana kallon yanda yarinyar tashiga motan ko 1min batayiba tafito tana jawo black hand waje da karfinta kaman yanda taja Hawwa dazu tace “Dadyyyy” rasa yanda zatayi Hawwa tayi Noor tajuyo tana kallon Hawwa tana dariya sosai kaman mara lafiya nan ko tsabagen murna ne tace “Dady see my Fairy Angel Anty she saved me that day from those bad people, Dady comeeeee” tai maganan ashagwabe kaman zata fashe da kuka dayasa gently ya sauko da kafafunshi kasa hakanan Hawwa taji gabanta yafadi dayasa dasauri tace “Noor Dear, Dady don’t have to see……” Kasa karasa maganan Hawwa tayi sabida yanda Khaleel yafito daga motan yana sanye da 3quater wando daya tsayamai a knee, yasaka wani black sneakers na givency mai tsinannen kyau, yana sanye da shirt lilac color shirt da butura ukun sama duka a bude kana hango black huge chest dinsa cus babu singlet aciki, waya na kunnensa yana yatsine fuska a wulakance amman yayi wani irin mahaukacin kyau, gashin kansa na sheki kaman yayi barin hair butter akai, ko kallon inda Hawwa take baiyiba, kallo daya Hawwa tamai tadauke kai da sauri, from his dressing kasan irin yaran nan ne marasa ji, Noor tana rike da hannun Baban nata, dayan hannun nata that is free takama hannun Hawwa dashi da sauri tarike tana washe mata baki dan bala’in son Hawwa taji tanayi tace “My Dady is on call FAA he will finish now kinji, saiki gaisa da Dady na ko” azuciyan Hawwa tace “wannan wace irin yarinya mai naci ne haka”? Azahiri tadanyi yake tana mamakin yanda yanzu daga fitowanshi tafarajin kamshin data jiyo dazu, Noor dake kallonta har lokacin tace “FAA you look very very beautiful, and you are tall like my Dady” kallonta Hawwa tayi, Noor tamata wani sweet smile tace “kusan tsawonki daya da Dadyna” dan murmushi kadan Hawwa tama yarinyar tanajin yanda yake magana comfortably one one kaman ba jiran sa akeba, ita kanta small Noor kallonshi tayi kaman zatai kuka tace “Dadyyyyyy” dan juyodakai yayi yakalleta ganin zatamai kuka yasa ahankali yace “hold on Sam” sannan ya zare wayan daga kunnenshi dasauri Noor tai murmushi tace “Dady see Fairy Angel Anty she saved me that day katuna? Dady she’s so nice and she’s so beautiful, Dady kalli she’s tall like you, Dady I love her abaya banda irinshi zaka saimin? Dady look at her she’s so beautiful ko Dady”? Tai wani tsallen farin ciki, ahankali Khaleel yadago wild eyes nashi ya daura kan Hawwa da daidai itama tadago nata idanun ta daura akanshi, wani kallon kallo sukama junansu yana tuna abinda tamai ranan, tundaga head zuwa flat sandals na kafanta Khaleel ya kalla irin kallon rainin nan dayasa Hawwa taji wani iri, cikin muryan nan nashi kaman wanda tun safe yake aiki yace “Princess I’ve seen her can I go back inside now?” Wani iri Hawwa taji kaman ya taka mata zuciya hakan yasa softly itama tace “Noor I have to go now” gamgam Noor tarike mata hannu tace “wait wait FAA” sannan tajuya takalli Babanta da idanu shima yana kallonta batare dayayi magana ba yadan bata fuska yakalli Babban bodyguard nashi yace “settle the girl please, bunch of government beggars!” Kaman an watsa mata kasa a kirji haka Hawwa taji sai kawai ta duka gaban Noor tana murmushi tana zare hannunta kaman tana magana da Noor tace “I wish you have enough to settle me with! Seems to me you guys were the beggars 2days ago haha” tadanyi yar dariya dayasa daga bodyguards din har Khaleel saida yajuyo yamata wani irin kallo dayasa tace “Noor see you another time okay and take care and be a good girl”Kaman Noor zatai kuka tai kwabekwabe da fuska dan bataso ta tafi Hawwa ta mata a very calming smile ta girgiza mata kai alamun kartai kuka sannan ta mike ta juya zata wuce taga bodyguard sun tareta gabaki dayansu, hakan yasa chak ta tsaya saikuma ta juyo tareda folding hands dinta a kirji ta zubama Khaleel kallo, daukan Noor Khaleel yayi yasa a mota yace “stay in the car princess” maida kofan yayi yarufe batare daya jira takara magana ba sannan yajuyo ya jingina da motan ya tsaya yana kallon Hawwa kaman yanda take kallonshi batare data cemai uppan ba, dan murmushi Hawwa tayi ta kadakai yaron nan baisan ita gogaggiyar yar iska bace ta hadu da yara ire irensu ajebon garin abujan nan and he’s no different from them, hakan yasa gently ta tako tafara tafiya tana tahowa gabanshi Khaleel na kallonta mata tsoranshi sukeji but ita bata tsoranshi, har tazo wajen dayake dan distance na tsakaninsu baiyi 4-5 feets ba takalleshi right in the eyes sannan tace “lemme give you a small analysis” tadan lumshe idanu tace “da mutumin da kullum yake tashi yafita nema and collect his salary da mutumin da live up under wealth na parents nashi waye beggar?” Wani irin kallo Khaleel yamata dayasa tadan tabe baki saitadan kalli kafansa tadago har zuwa kanshi kaman dai kallon daya mata dazu tace “tundaga samana to kasa na is my work and effort I can for a fact say tundaga kan this designers sneakers of yours zuwa duka kayan dake jikin ka da motan nan da this security are your Dad’s wealth who is the beggar”? Idanun Khaleel yayi ja dake nuna maganganun sun tabashi, Hawwa tace “the only thing dake naka mamallakin ka is that little princess in the car!” Yunkurowa Khaleel yayi kaman zai kai mata bugu dudda gabanta yayi mahaukacin fadi dan kaman zaki haka yazo amman chak Hawwa ta tsaya batare data ja bayaba dudda taji kafafunta na rawa, dab da ita ya tsaya kaman zai shiga jikinta tanajin saukan numfashinsa akan fuskanta dake kamshin
Chapter 16 · 0% Book details