← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 123

Sashe 39

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE Kusan 5min Khaleel da Baba sukai ahaka sannan yadaga kanshi daga kafadan Baba yakalli Baba yace “kahuta? Kadena damuwa”? Gyadamai kai Baba yayi yace “nahuta Ibrahima” sauka Khaleel yayi yadauki crutches din yabashi Baba ya karba suka fito tare, Ammi bata wajen hanyar dakin sukayi Khaleel yaci tura dagadan nesa Baba yajuyo yakalleshi yace “bazaka shiga ba” dan sosakai yayi saikuma ya dauke kai ahankali yace “uhmmm kunyan nakeji” dariya Baba yayi irin na manya dinnan jin maganan dayayi yace “kunya? Wai kunyan Ammi”? Dasauri Khaleel yajuya yana gyadamai kai yace “bye Baba sai munzo anjima” kafin Baba yayi magana har yayi kofa su Salman dake wajen suka budemai kofa yafice suka bishi Baba yace “jama’a wannan yaro akwai shiga rai, Ya Allah inama Hawwa na kwadayinsa sosai, Allah inhar alkhairi ne auren nan kasa ya tabbata yau” yayi maganan a yana shiga cikin dakin da murmushi kan fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”? Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren, zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab? Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki dan hukuncin nan tare zamu yankewa yarmu” murmushi Ammi tayi jin yanda Baba ya girmamata yabata matsayi yakuma karramata, anatse tace “na yarda Malam, nakuma aminta idan Alkhairi ne Allah yasa su dawo adaura idan ba alkhairi bane kuma Allah ya musanya mana yabata miji da gaggawa” Baba yace “Ameen Ameen” yana murmushi suka cigaba da hira, abinci aka kawo musu akace an riga an biya kudin abincin duk sukaci Ammi takira Ramla tace kartai girki, tabama Baba wayan Hawwa tace “Malam kira wajen aikinta ka sanar dasu tayi hatsari” Baba yace “nemomin number kaman DIG naji tana kiran Ogan nata duba kiciromin number” Ammi ta karba tana ciromai.WAIWAYE BAYA KADAN..!Ana fitar dasu waje har parking space aka kaisu aka tsaitsaya akansu kaman barayi, Salman yace “you have 10secs to leave this hospital else we hand you over to police and press charges against the both of you, we have cctv camera in every corner of this hospital starting from patient room” kallonta Baban Yaseer yayi yanda take kallonshi tana haki, ranshi ya baci iya baci da abinda tamai, baitaba sannin this is who Ni’ima is ba sai yau, cikin kakkausan murya yace “daganan kiwuce gidanku, namiki iyaka da gidana zankira mai gadi na shaidamai kada ki shiga gidan nan, kije na sakeki saki daya!” Faduwa gabanta yayi sosai zatai magana kawai yabude motan yashiga yawuce tabishi da kallo kirjinta na bugawa, Salman yadaka mata tsawa. “Madam leave our hospital!” Jikinta har rawa yake ta wuce ta shiga tata motar ta kunna tabar asibitin.School nasu Yaseer yawuce direct ranshi na suya ya daukosu yace zasu danyi tafiya na 2week, sukaje gida yahada kayansu tundaga kansu Ipad yasasu a mota kawai sukai Kano gidan iyayenshi sukaje yakaima mahaifiyarshi yaran sunata murna yace suyi kwana biyu yasayo musu komi washe gari yabar Kano da sassafe danso yake yaje yaga Baba he made up his mind zai auri Hawwa yanzu, he wants to make her his wife.****EPISODE Sundanyi nisa ahanya yasa hannu yadauki wayanshi yayi dialing number Babanshi, Musbahu PA Excellency ya dauka yace “Khaleely Babanka na kan chamber” cikeda isa yace “I don’t care kaimai waya” cikeda lallashi Musbahu yace “Allah huci zuciyan yallabai bari na kaimai” Khaleel na kan layin kusan 5min sannan yaji muryan Babanshi a speaker yana excuse me sai chan Excellency yayi magana cikin so da kewa yace “Khaleely na ya akayi? Ina tsaka da meeting? Meya faru bakada lafiya ne”? Dan kishingida yayi murya chan kasa yace “I will send you address na wani anguwa kasameni awajen by 6, kazo da trust friends naka” dasauri Excellency yace “angama yarona zanzo, but meke faruwa lemme know wat I’m coming there for” shiru Khaleel yayi kaman bazaice wani abuba chan yace “I want to marry someone Pops” dasauri Excellency yace “aure? Aure Son? Ba mamanka is the one handling all of that for you ba, an mata screening ne ita wacce kakeson auren? Why do I have to come our lawyers da Malamai can take care of the aure for you, is my presence necessary”? Kai tsaye Khaleel yace “ai nasan dasu nace kazo Pops” dan tausasa murya Excellency yayi yace “I know, I know, karka bata rai I didn’t mean to hurt you, zanzo kawai nayi mamaki ne this is the first person dakake neman aure da kanka batare da Mom naka ta zaba maka ba ta auro maka ba, wacece yarinyar?” Kai tsaye yace “that police girl” dan zaro idanu Excellency yayi yace “you mean officer Hawwa wacce ta ceto Noor? That criminologist”? Murya chan kasa Khaleel yace “uhmm” dan shiru Excellency yayi sai chan yace “Khaleely are you sure about this decision? Cus naga yarinyar is hot tempered, bakaga yanda kuketa fada rannan ba, and you guys are almost age mate fa dan ba karaman yarinya bace, banson wacce zatazo tana baka ciwon kai ba tana wahalar da d’ana fa, I dislike stubborn girls” ahankali Khaleel yace “I can handle her Pops, I just wanna have fun with her Pops don’t worry” dan murmushi Excellency yayi cikeda kaunar yaron nashi yace “you know I will always give you kome kakeso ko? You have my support, see you by 6, I love you yarona Khaleelyn Babanshi” dan smiling kadan Khaleel yayi ya katse wayan ya yar agefe yadago kanshi yakalli Salman yace “I want every info akan mahaukaciyan nan and that photo boy of hers” gyadamai kai Salman yayi yace “yes sir” kallon driver yayi yace “Sam’s house”.Wani tamkeken estate suka wuce suna zuwa gaban gidansu gate yayi scanning motansu kawai yabude musu suka shiga, budemai kofa Salman yayi Khaleel ya sauko yawuce ya shiga flat din Sam dayake bangare daban aka budemai kofa, tundaga falo yake jiyo ihun Sam din tareda na mace, tsaki yayi yawuce wajen dinning inda yaga wine, wine cup yadauka yaje fridge yazuba ice sannan yazo ya tsiyaya wine din ya zauna yafara sipping yana jiyo ihunsu wlh sun isheshi, bacci yakeji, dan gajeren tsaki yayi ya ijiye wine glass din kawai yawuce sama kai tsaye yabude kofan dakin yashiga Sam yadago kanshi yana nishi kaman kwado yace “Hi cousin” mugun kallo Khaleel yama yarinyar dayake abun da ita yace “get out!” Dasauri yarinyar ta fixge jikinta ta duka tana kwasan kayanta ta wuce tafita Sam rai abace yace “wai kai mehaka ne eh? I’m not done fa Dan iska kawai mai bakin hali” tsaki Khaleel yayi yawuce abinshi ya shiga next dakin yafada gado yana lumshe idanu bacci yakeji sosai.Kusan 20min Sam yadauka dan saida yayi wanka sannan yafito yashiga dayan dakin yana kallon Khaleel dake lumshe idanu yace “ya akayi Lee”? Da muryan bacci yace “wake me before 6 zamuje daurin aure” Sam yace “wani daurin aure wazaiyi aure?” Yana kulle idanunshi yace “me”? Dasauri Sam yazauna bakin gadon yana kallonshi yace “yaushe aka fara daura maka auren gayyatan jama’a? I thought a seminar room na gidanku ake komi”? Hamma Khaleel yayi yace “this time is different” “wazaka aura”? Sam ya tambaya da kosawa, Idanun Khaleel a kulle yace “that Police gurl” fashewa da dariya sosai Sam yayi yace “Leee bakada mutunci shegen gari! Ai nasan after all that girl said you must find a way to show her who’s the boss, there’s nothing da zakaso da bazaka iya samun shi ba, and comfortably use it and dump it” murmushi kadan Khaleel yayi yace “starting tonight! She will belong to me!” Sam na annashuwa yace “use her kayi BDSM kamata lilis, 50shade of Lee zakai da ita” dan dariya kadan Khaleel yayi murya chan kasa da bata fita da kyau sabida bacci yace “she’s sick I don’t wanna hurt her now!” Da sauri Sam ya kalleshi jin maganan dayayi which sounds so unlike him yace “Lee mekace? Cousin? Kai Khaleel?” Yakai hannunshi yayi tapping nashi amman ina yayi bacci, dan murmushi Sam yayi yace “shegen yaro to ahaka zaka auren? Lemme call Balalau designer” kiran designer yayi aka turamai bespoke manyan kaya dayawa na gizna ya zabanma Khaleel milk shiya dauki ash yatura kudi around 4 aka kawo musu kayan wuraren 5:00PM wayan Khaleel yahau ringing ganin Pops ke kiranshi yasa Sam yashiga tadashi da kyar yatashi wayan Sam yabashi karba yayi yasa a kunne yana lumshe idanu yace “gamu a hanya already” gyadama Pops kai
Chapter 39 · 0% Book details