Sashe 41
Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
that girl said you must find a way to show her who’s the boss, there’s nothing da zakaso da bazaka iya samun shi ba, and comfortably use it and dump it” murmushi kadan Khaleel yayi yace “starting tonight! She will belong to me!” Sam na annashuwa yace “use her kayi BDSM kamata lilis, 50shade of Lee zakai da ita” dan dariya kadan Khaleel yayi murya chan kasa da bata fita da kyau sabida bacci yace “she’s sick I don’t wanna hurt her now!” Da sauri Sam ya kalleshi jin maganan dayayi which sounds so unlike him yace “Lee mekace? Cousin? Kai Khaleel?” Yakai hannunshi yayi tapping nashi amman ina yayi bacci, dan murmushi Sam yayi yace “shegen yaro to ahaka zaka auren? Lemme call Balalau designer” kiran designer yayi aka turamai bespoke manyan kaya dayawa na gizna ya zabanma Khaleel milk shiya dauki ash yatura kudi around 4 aka kawo musu kayan wuraren 5:00PM wayan Khaleel yahau ringing ganin Pops ke kiranshi yasa Sam yashiga tadashi da kyar yatashi wayan Sam yabashi karba yayi yasa a kunne yana lumshe idanu yace “gamu a hanya already” gyadama Pops kai yayi yace “okay” Dasauri Excellency yace “bacci kake ne Khaleelu?” Ahankali yace “uhn” cikeda so yace “okay tashi kashirya sannu stop stressing yourself” katse wayan yayi yana kallon Sam dake shiryawa baiyi magana ba Sam yace “jekai wanka ga kayan ka nan my gift for ango” dan tsuki yayi kawai yatashi yafada bayi yayi wanka yafito jallabiya mai kyau yasa ya shimfida dadduma yayi la’asar yana idarwa Ga mamakin Sam saiyaga yawuce yana bude kayan without complain cus baison saka manyan kaya yafara sakawa Sam kawai ya tsaya yana kallonshi…….Tun around 4 Baba yabar asibiti yakoma gida, yana kwalama Ramla dabata dawo hospital ba sabida Ammi tacemata yazauna kawai an basu abinci kira, dasauri tafito tace “gani Baba” murmushi yayi yace “dauko hijabi kibini kofar gida tabarmai zamu shimfida kaman zanyi baki da yamman nan” biyo Baba tayi har dakin Umma data hadarai Baba ko kallon inda take baiyiba yashiga kwaso tabarmai daga dakinshi yana bata taba karba sannan suka wuce waje tare tashiga shimfidawa yace “bari na leka gidan Malam Sama’ila Allah yasa yana nan” yawuce yana kallonshi yashiga sallama a gidan dake just 2 houses daga nasu.EPISODE Fitowa Malam Sama’ila yayi Baba suka gaisa sosai Baba yace “Malam Sama’ila kai kadai nake sanarma da maganan nan sabida koda abun baiyuba kar kunyan duniya yakamani” yadan sauke ijiyan zuciya yace “inasa ran wani yaro dake neman Hawwa zai kawo mahaifinshi da mangariban nan suna zuwa nakeso na daura musu aure shine nace bari nazo nafada maka tunda kaine Babban amintacce na kuma limamun masallacin mu” cikeda farin ciki yace “Alhamdulillah, Alhamdulilah ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi, matar mutum kabarinsa inji hausawa, bakada matsala ina nan ai duk sanda suka zo sai nabada sanarwa a masallacin a tsaya” gyadamai kai Baba yayi jikinshi narawa yace “akwai wani abun da ake bukata ne a masallaci kowani abu, kaga duk su test din nan ba matsala bace Hawwa wajen aikinta duk bayan rabin shekara 6month sukeyi, nasan AA ce Hawwa zata iya auren kowa, sannan Hawwa na batada wani cuta, banson tambayoyin nan suhanani auran da ita dan Allah kadama kayi Malam Sama’ila” murmushi Malam Sama’ila yayi yace “kada kadamu bazan yiba” Baba yace “yauwa bari nabaka kudade adan fefesa turare a masallacin asa yara su gyara” cikin kudaden daya dauka dazu dazaije asibiti yazare 20k yamikamai Malam Sama’ila ya karba Baba yawuce yatafi Malam Sama’ila yabishi da kallon tausayi yace “Ya Allah kadubi zuciyan tsohon nan ka aurar da yarshi kada ka kunyatashi” saikuma kawai yawuce masallacin nasu.Zama Baba yayi a kofar gida sai kada kafafu yake itama Ramla tafito tazauna kusadashi dan cikin gidan ya isheta ganin yanda yakeyi yasa Ramla tace “Baba su waye zasuzo wajenka ne haka”? Dan kalle kalle Baba yayi saikuma yamata alamu da hannu datazo kusada shi dasauri Ramla tazo tana zama agabanshi akasa akan tabarma, dan dukowa yayi cikin whispering yace “Hawwa ce tayi miji sunanshi Ibrahima, bakiga yaron ba badai shiga rai ba, gashi kyakkyawa dan gayu tsaftsaf dashi son kowa kin wanda yarasa ga tausayi, inhar abun ya yuwa Kulu na tayi goshi” zaro idanu Ramla tayi cikeda farinciki dan bakaramin addu’a sukema Hawwa tasamu mijiba ba, Baba kaman yaro yace “banso asani, banson kowa yaji, daga Mamanki sai Malam Sama’ila sai kece mutum ta uku danike fadamawa, hadiye murnan” hadiye murnan kuwa Ramla tayi tana kallonshi kaman TV, Baba yace “nace suzo karfe shidda da mangariba dai kinga ana salla sai adaura auren kawai” kai kasa daurewa Ramla tayi kawai saita tashi tahau tsalle sosai tana bude bakin ihun murna amman bata bari ihun ya fito, Baba ya tuntsure da dariya sosai yana kallonta yanajin dadin dabai tabajiba yace “wai bacewa nayi kidena murna ba, wannan yarinya bakiji” yacigaba da dariya shima kaman yatayata tsallen, shi kanshi baisan murnan yakeba, zama Ramla tayi awajen sai hira suke da Baba farin cikin auren yama kore damuwan rashin lafiyan Hawwan dake asibiti akwance, wajajen 6:30 Ramla tawani zabura tace “Baba ga motocin yan sanda tare da wasu jeep suna shigowa, Baba wlh sune, sune Baba” Da Ramla da Baba yar tsere tseren leke ake yakama hannunta yana hamdala yace “zauna zauna Ramla kada aga mun kosa kokuma imaza je kiramin Malam Sama’ila maza” dasauri Ramla tawuce tana kallon motansu dake shigowa ahankali yaran anguwa na binsu daidai ana parking motoci a kofar gidan Baba, shima Malam Sama’ila tareda wasu dattawan unguwa da Ramla na zuwa wajen duk sukazo suka tsaya tareda Baba dudda maza ne Ramla jitayi bazata iya komawa ciki ba wlh agabanta za’ayi komi abunka da yarinya.Gently aka bude motan Excellency yasauko yana sanye da Baban riga na gizna tareda Musbahu, aka bude second car din, Mahe ne Baban Sam kanin Excellency shima sanye da manyan kaya, sai third car, Nigerian chief of staff da attorney general wayanda shakikan Excellency ne sai fourth car wanda gently Khaleel ya sauko yana sanye da milk na Gizna dake sheki ya kafa hula ta kusan 8million akai tana sheki yana zuba kamshi fuskanshi yayi wani kwarjini da annurin haiba, Ramla ta taushe bakinta sabida ihu na neman fitowa ganin mijin Ya Hawwa tace “Ammi mijin Ya Hawwa na da kyau, wayyyoo wlh bantaba ganin mutum me kyanshi ba, Ammi yahadu, Ya Hamza, Asiya wayyooo” Sam shima yafito, anatse Malam Sama’ila yace “Bismillan ku” gaban Baba sai bugawa yake yaga Khaleel yasan dan masu kudi ne but bai dauka kudin yakai hakaba, duk zama sukai akasa Baba ne kadai zaune kan kujera dan zaman kasa namai wahala sabida kafanshi da guda daya ce.Yan anguwa aka taru kaman ana wani abu but babu wanda ya iya zuwa wajen sabida jami’an tsaro dasuka tare wajen da bindogoginsu a hannu.Malam Sama’ila cikeda natsuwa yabude taron da addu’a yace “ina muku maraba da zuwa” faram faram su Excellency suka amsasu, anatse Excelllncy yace “to Masha Allah da farko dai sunana Alhassan Mangal senate president na Nigeria” kaman ruwa ya cinye su Baba yana kallonsu yayi shiru, yanuna Mahe yace “ga kanina Uwa daya uba daya Mahe, ga yarona Ibrahim Khaleel, ga dan kanina Sameer, gakuma shakikai na” yanuna kowa yace “d’ana ya samemu da maganan yaga yarku mai suna Hauwa’u yanaso, sun hadu ta sanadiyan kwato mana yarmu datayi daga hannun yan kidnapping Noor, munzo neman aurenta dafatan za’a bamu” murmushi sosai Baba yayi he’s overwhelmed baisan cewa yaune rannan da zaiga auren Hawwa ba, today started so bad for him, ciwon Hawwa saikuma hatsarinta, saikuma Ni’ima da abubuwan datayi, baitaba tsammanin ending na yau will be this good ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace idan kasan mafitar rana bakasan mafadan ta ba. Gyaran murya yayi yanuna kirjinshi yace “harga Allah na yarda da Ibrahima! Na aminta da Ibrahima! Nakuma natsu da Ibrahima, danhaka ni mahaifin Hawwa nabawa Ibrahima auren y’ata Hauwa’u dayazo nema ayau!” Malam Sama’ila yace “Allahu Akbar” duk akai Kabbara awajen, Malam Sama’ila yace “idan ba damuwa ga masallacin mu nan, muyi sallan magriba tunda lokaci yayi sai adaura auren” kai tsaye Excellency yace “bismillan mu” duk aka tashi aka wuce out of respect Excellency ya jera da Baba dake dogara sanda suna zance freely kaman sunsan juna babu wani zancen nuna kaskanci, hakanan abin yama Khaleel dadi inda Pops yafi Mom kenan, yanada saurin accepting mutane unless baice yana sonsu ba, hakama yanuna bayason abu to wlh Pops shima zai nuna bayaso kodako menene abin.Alwala akayi yau masallaci ya cika makil har gaban layi akai salla aka bada Sanarwa za’a daura auren Hawwa, dumbannin jama’an unguwa suka sheda aure tsakanin IBRAHIM KHALEEL DA HAUWA’U AKAN SADAKI MILIYAN HAMSIN DA DARHAMIN GWAL DARI!Zokaga yanda mutanen anguwa suka haukace news na flying kaman kite Hawwa tayi aure, ashe wani jinkirin alkhairi ne, ta auri dan masu kudi, ai shi Khaleel din shine d’a daya tilo wajen mutumin the richest man a Nigeria menene menene, tashi Excellency yayi ya karbi speaker ya sanar yama masallacin nan donating miliyan dari! Saikuma yabama mutanen ungunwan matar dansa tundaga kan yaro da babba, tsoho da tsohuwa Miliyan dari arabama kowani household, haukacewa Umma tayi acikin gidan dan tanajin announcement daga speaker tace “ina matarsa zai aurar da diyarsa banda darajan dazai fadamin saidai naji a speaker? A inama tasami mijin? Kodai hada baki akayine? Ta ina Hawwa zatasan yaron Alhaji Mangal damuke gani a TV ta ina? Kai karyane da wata akasa auren nan bazai taba lasting ba” kaman mahaukaciya takasa rike bakin cikin tashiga kiran yaranta mata wanda all of them are happy for yayarsu suna cewa zamasu zo gobe kawai ta katse wayan tana zage zage har Ammi dake waya da Ramla dake bata labari saida tajuyo ta Ammi tace “kisa sakata a kofa kada ki bude sai Malam ya shigo” dasauri Ramla tace “ita ta isa ta tabani wlh saina mata tsinannen duka Ammi” Ammi tace “ke!” Dasauri tace “yakuri naji zansa sakatan Ammi”.Adai area nan nasu duk wanda yasan Hawwa yasan Ni’ima duk wanda yasan Ni’ima yasan Hawwa, Mama na zaune a tsakar gida da Ni’ima daketa bambami tunda tazo gidan Mama dazu akai sallama aka shigo gidan matan makotansu ne suka shigo yima Mama Allah sanya alheri