← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 123

Sashe 76

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daga kunne Khaleel yana bude kofa yashigo dakin hada idanu sukayi dasauri ta dauke kai ya maida kofa yarufe yataho dinning din yana kallonta kaman yau ya fara ganinta dan kanta ba dankwali ga hannuwanta lalle hakama kafafunta dasauri Hawwa tamike tsaye zata wuce yasha gabanta yace “dawa kikai waya?” Dan kallonshi tayi suna hada ido tadauke kai tace “Ina ruwanka”? Hannunshi kawai yasa ya karbi wayanta tawani yi kanshi kaman yaro zata daka Khaleel yace “kin manta bani da lafiya ko” chak Hawwa ta tsaya tana kallonshi saikuma ta dauke kai call log nata yagani ganin Ammi ne sai kawai yakira Ammi back ta dauka tace “Hawwa” dasauri Khaleel yace “Mom nine shine nima baki kirani ba Matana kadai kika kira kinfi sonta ko”? Kunya Ammi taji yakamata Hawwa tasaki baki tana kallon Khaleel, Ammi tace “assha ai Ibrahim itama bawai nakira naji yataka bane kira nayi na sanar da ita na aiko su Ramla sukawo mata sako suna bata su juyo gida Aminu zai kawosu sabida tafada abarsu su shigo, ya kake ya Hawwa? Hope babu wani abu bata bata maka rai?” Hannun Hawwa kawai yaja yawuce kujera da ita ya zauna yana janta zuwa jikinshi zata fizge yahanata yasa wayan a speaker yace “Ammi me kikace banji ba”? Ammi tace “cewa nayi ya kuke Ya Hawwa dafatan bata batamaka rai babu wani abu”? Kallon Hawwa yayi da gangan yace “in fada”? Zaro idanu Hawwa tayi irin me haka Khaleel, itakuma Ammi dataji abinda yace dasauri tace “fada Khaleel metayi fadamin na cicimata”? Cikeda iskanci yadagama Hawwa gira daya yace “Ammi tace tadena karki damu takaramin zan kira na fada miki” Ammi tace “dan Allah Khaleel kome tamaka ka sanar dani zan gyaramata zama nine daidai da Hawwa, bari na barku to saida safen ku, Allah muku albarka, Allah baku zaman lpy, Allah ya dafa maka Khaleel yabaku yara masu albarka, ina Noor banji muryanta ba” Murmushi yayi yaji dadin addu’an Ammi sosai yace “yau sunday fun day nata ne taje outing” Ammi tace “tom shikenan sai anjiman ku” katse wayan yayi yadan kalli Hawwa datamai mugun kallo yamata murmushi kadan yaciro wayanshi yakai kunne yace “I will be having guest any moment Salman, a shigo dasu” ya katse wayan ya kalli Hawwa data dauke kai tace “ar…..e you not eating”? Shiru Khaleel yayi yana kallonta so ta damu tasan baici abinci ba, warmers na dinning ya kalla ahankali yace “I don’t want food from Mom! Kununa yarage?” Dan kallonshi Hawwa tayi saita dauke kai dasauri tace “Mesa za kasha kunu?” Murya chan kasa yace “I don’t want to make you work, our chef will start work gobe she’s coming from lagos” shifa Khaleel baisan wahala ba, yarone daya taso cikin hutu baisan cewa mata suppose cook ba not wasu chef, cus baiga Momy shi na girkiba, batare da Hawwa ta kalleshi ba tace “akwai abinda kakeso kaci?” Gyadamata kai yayi yace “uhm” ahankali still taki kallonshi tace “mene kakeson kaci?”Dagowa yayi yasa kanshi akan kafadanta dasauri ta kalleshi murmushi yamata yace “I want pasta da chicken” dan tureshi Hawwa tayi ta tashi dasauri tai kitchen tace “I don’t want any chef karma ka kawomin wata” yabita da kallo baitaba sanın she’s this caring ba wlh, jiyayi daga tashinta falon yadaina mai dadi sai kawai yatashi yabita kitchen din Hawwa na tara ruwa a pot yashigo yace “I want to help” wani shegen kallo Hawwa tamai irin see this one saita dauke kai tace “wat can you do?” Dasauri yace “everything” yana zama kan stool na gaban island na kitchen din, wajen maggi taje tadauko tasa a plate tazo tace “peel them” daukan maggi yayi yana kallo yana juyawa yace “wat is this?” Murmushi kadan Hawwa tamai bata amsashi ba tai banza dashi, tashiga wanke nama tana yankawa shikuma yana chan yana karance karancen all rubutun jikin maggi batare dayama fara budewa ba cus yanaso yasan menene abun tukunna, chan Hawwa tace “Khaleel” dasauri yadago kanshi yace “yes my baby” hade fuska tayi tajuyo dasauri yace “sorry i mean yes my Yar Sanda” ahankali ta juya, calmly tace “you were so rude to your Mom” dasauri yace “she was so rude to my wife” tsayar da abinda takeyi Hawwa tayi tace “iyaye can get angry with yara” dasauri yace “I’m the only one that is allowed to get angry with you!” This time juyowa tayi ya kalleshi if Khaleel is this protective over matayensa mesa ya sassakesu toh? Maisa yayi use and dump dasu? Maisa baya dadewa dasu?.EPISODE Juyar da kanta Hawwa tayi gently and calmly cikeda hikima ta hanyar da bazata nunamai kaman shi bai saniba baida ilimi ko wani kalan kaskantarwa da nuna ta fishi sannin yakamata ba tace “kasan Annabi Muhammad SAW yace fushin Allah yana daga cikin fushin iyaye yardan Allah na daga cikin yardan iyaye, zagin iyaye is a sin!” Daidai ya bare maggi daya yace “mesa ta tabamin matana? Idan bata zageki b ai bazan mata abinda nayi ba”? Murya chan kasa tace “how would you feel idan Noor tazageka ko tamaka abinda kama Mom”? Tunda tafara maganan sai yanzu yadago kanshi ya kalli Hawwa kaman yanzu ne takama attention nashi, itama Hawwa juyowa tayi takalleshi eyes to eyes gently Khaleel yace “I will never insult mijin Noor, kome takeso I will love it as Babanta” juyawa Hawwa tayi tadauki season tana zubama naman tace “apologize to Mom sabida she loves you dearly! Stop insulting iyaye or shouting at them is very bad, in islam idan kanayi kaima naka yaran zasu maka, yima iyaye biyayya is obligation akan kowani d’a islamically, the only place da aka yarda karmu musu biyayya is awajen sabama mahallici, idan da kanayi sabida yarone kai yanzu the habit should stop you have a daughter, kaji”? Tafadi lovingly tawuce wajen pot batare data kalli fuskanshi ba yabita da kallo, there’s something about Hawwa idan tanama magana like he felt something just now kodan bata tabamai magana for this long bane calmly and sweetly koda yaushe fada suke ne oho, but the way tamai maganan captures his attention and it makes him relates it to wat if Noor tamai haka, Hawwa na cikin stairfrying chicken awuta kawai Khaleel ya rungumeta zata juyo yahanata yadaura kanshi a gefen wuyanta murya chan kasa yace “what if Mom insult you again”? Gabanta na faduwa tace “mothers can insult yaran su” cikeda kiriniya Khaleel yace “ni wlh babu wanda ya isa ya insulting naki nahakura kowaye” danjimm Hawwa tayi murya chan kasa tace “promise me bazaka sake treating Mom poorly ba or even Babanka, especially attempting dukansu or zaginsu, I get they pamper you too much but that was very very bad kaji, idan wani yamusu haka a waje zaka ji dadi? Will you be happy kaga wani awaje yana kokarin dukan iyayenka ko zaginsu will you be happy”? Girgiza mata kai Khaleel yayi yace “no” da zuciya daya dan yasan bazaiji dadi ba aka musu haka, yabi Hawwa da kallo tana kamshi sosai sai kawai ya manna mata kiss a kumatu dasauri tajuyo cikeda masifa sakinta yayi yawuce yafita yace “I’m coming zanje wajen Mom” fitowa yayi a garden nasu ya tsaya wani white flower yacire yawuce flat nasu Mom bata falo direct bedroom nata yawuce yaboye flower abayansa.Kai tsaye ba knocking kawai yabude kofa yafada dakin Mom na kwance agado tabuga tagumi bawai bacci takeyi ba ganin Khaleel yashigo yasa tawani zabura ta diro daga gado tana dafa kirjinta kaman zatai having heart attack tace “Khaleely jikin ne? Meke damunka eh?” Murmushi yamata kadan yace “calm down Mom common you look so frightened come” yasa hannunshi daya yakamata suka koma wajen gadon ta ya zaunar da ita shima ya zauna sai kawai ya ciro flower dayake boye wa abayanshi ya mika mata yace “sorry Momaaaa” yafadi ashagwabe daman duk sanda zai mata shagwaba yake cemata Moma, Mom ta tsaya shiru tana kallonshi cus batamasan meyake cema sorry ba idan fadan jiyane tama manta bayau Khaleel yafara zaginsu ba har ubanshi duka yana musu is a normal thing.Ganin tana kallonshi yasa ahankali yace “I’m sorry Mommy for shouting at you, for being aggressive and for insulting you Moma bazan karaba pinky promise” sosai Mom ke kallonshi she was shocked to bone marrow dahar tama kasa reacting, Khaleel ke bata hakuri sai taji hawaye yafara tsatsowa a idanunta sai kawai tafashe da kuka dasauri Khaleel ya ijiye flower yayi hugging nata a chest nashi ashagwabe yace “Moomaa sorry okay bazan kara ba trust me stop crying” Mom na kuka tace “no I’m not crying sabida abinda kamin jiya I’m crying sabida tunda na haifeka this is the first sorry daya taba hadani dakai Khaleel” dasauri yasaketa yace “really?” Gyadamai kai tayi tana murmushi tana share hawayen tadauki flower ta rungume a kirji tace “Wlh banyi fushi ba ina zan iya fushi dakai babu abinda ke damuna banda rashin lafiyanka Khaleely what if? Wat if your cancer is back?” Murmushi yamata yace “bakiso na mutu”? Fashewa da kuka Mom tayi tana kaimai duka ahankali akirji jin maganan dayayi, yayi dariya ashagwabe yace “idan bakiso na mutu treat Hawwa kaman yanda kike treating dina, she doesn’t have a Mom be her Mom kinji Mooma, idan kika mata haka I promise I will not die I will fight this cancer this time also!” Sosai Mom ke kallon Khaleel bata taba ganin Khaleel na son abu kaman yanda taga yanason this police girl ba, kai infact tun yana karami bai taba son abu har kaba, how did this police gurl bewitch Khaleel haka? Khaleel hardly loves fa, bai cika son abuba but akan Hawwa daban ne ahankali ganin Mom tayi shiru yatashi yace “okay na mutu saiki huta” hannunshi takama da sauri kaman zata dake shi tace “ka kara kiran ma kanka mutuwa saina bata maka rai, I will give my life to save you kajini” murmushi yamata yace “naji, naji, naji, tom will you love Hawwa toh like me eh Mooma plzzzzzz?” Gyadamai kai Mom tayi ahankali sai kawai ya rungume Mom yanajin dadi sosai, ahankali Mom tace “Khaleel kanason Hawwa sama dani ko?” Da zuciya daya Khaleel yanawani kankame Mom yana murmushi yace “yes yes yes wlh Mom! I love Hawwa with all my life,
Chapter 76 · 0% Book details