← Book details Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 123

Sashe 45

Gargadan So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tayi dasauri tace “dan Allah Malam ayakuri, Malam kabar yaran nan sudawo tare sunason junansu Malam” dakin Umma Baba yafada Umma ta watsama Mama harara dan basa shiri sabida uwar kawar Hawwa ce rai ba dadi Mama tawuce tabar gidan.Kari Baba yayi tareda Ramla sannan ta shirya suka fito tare wajajen 11 daidai motar Baban Yaseer na parking Baba ya tsaya turus yace “je gida Ramla natashi tafiya saina kiraki” komawa ciki tayi, Baban Yaseer yafito yazo wajen Baba cikeda mutunci suka gaisa Baba ya zauna kan kujera shikuma ya zauna a tabarma yadan sosa kai yace “Baba zan fara da baka hakuri bisa ga abinda yafaru jiya, Baba kayakuri yawancin maganganun da Ni’ima tayi na tabbatar cewa karya tama Hawwa, kowa yasan hakan ba halin Hawwa bane, Baba dan Allah kayakuri” murmushi Baba yayi yace “bakomi nahakura komi yawuce” ijiyan zuciya yasauke yace “saikuma ahhhhhmmm” yadanyi shiru yana sosa kai Baba yace “ina jinka” kanshi ya sauke kasa yace “Baba inaso kabani daman auren Hawwa! Baba ina matukar son Hawwa, namaka alkawari Baba zan kula da ita nakuma riketa amana Baba, Baba dan Allah dabi’un Niima kada su sa ka ki bani wlh Baba zan kula da Hawwa namaka alkawari babu abinda Ni’ima zata iya mata”Ijiyan zuciya Babayasauke anatse yace “Aliyu” dagokai Aliyu yayi yakalli Baba yace “Na’am Baba” Baba yayi murmushi yace “Aliyu kai d’a nagari ne da babu iyayen dabazasuyi alfaharin samunka amatsayin d’a ba, Kanada hankali natsuwa da kirki babu wanda bazaiso yahada zumunci dakaiba” yayi shiru chan yace “Allah yana jarabtanmu da abubuwa da dama, wani zubin yana nunamana duk yanda mukakai ga son abu bamu samuba sabida banamu bane” faduwa kawai gaban Aliyu keyi Baba yace “ina sonka Aliyu sosai amman y’ata Hawwa bataka bace, jiya nadaurama Hawwa aure da Ibrahima, Hawwa tariga tazama matar wani!” Faduwa gaban Aliyu yayi dasauri yakalli Bab idanunshi har twitching suke sabida bugawan kirji yama kasa magana Baba ya lumshe idanu yabude, Baba yace “kayakuri Hawwa tayi aure, inaso kaima kaje ka gyara rayuwanku da Ni’ima, ku daidaita kanku, ku shirya ku kula da yaranku, yanzu Hawwa tafita daga tsakiya, babu wani abu dazai kara jawo muku fada, inaso naga ka koma yanda kake d’a da Ni’ima gwanin ban sha’awa, ku manta da komi acigaba da rayuwa anama juna fatan alkhairi kaji Aliyu”baki Aliyu yabude zaiyi magana saiga hawaye mai zafi sun sauko daga idanunshi dasauri yakai hannu ya share yajuyar da kai yana huci zuciyanshi na kuna yanason Hawwa sama da tunanin kanshi, waye Ibrahima? Yaushe Hawwa ta sansa? Ko sanarwan da Baba yayi sanarwa a masallaci ne yasa aka samo Ibrahima? Zafi yaji ranshi namai hawaye suka kara zubowa ya share da sauri still yakasa magana, ba karamin tausayi yabama Baba ba, kana gani kasan Aliyu na son Hawwa sosai, ahankali yace “kayakuri Aliyu, nasan yanda so yake, baya neman shawara idan zai kamaka, amman kayakuri, ka rungumi kaddara, ka gyara aurenku da Ni’ima ka rungumi iyalinka kaji” gyadama Baba kai yayi yakasa motsi Baba yayi shiru yana kallonshi yakai kusan 20min ahaka sannan yatashi muryanahi narawa sosai kaman zai fashe da kuka yace “natafi Baba” Baba ya gyadamai kai duk jikinshi yayi sanyi but this is the right thing, yawuce yatafi Baba shima yayi shiru, saida yaga barinshi unguwan ya kwalama Ramla kira suka tafi abinsu.Da kyar cikin ikon Allah Baban Yaseer yakai gida gateman dinsu na gaidashi ko iya amsawa baiyiba yawuce yabude flat nasu yashiga yashiga bedroom nasu yazauna yafara fuzar da iska da baki sosai, hawaye masu dumi suka shiga zubomai yasan da Ni’ima duk batai haukan nan ba wlh Baba zai iya bashi Hawwa, yanzu ga shi Baba yaki, yasan rigiman Ni’ima yasa Baba yaji gwara ya aurar da Hawwa ga kowama ko wutan da Ni’ima ta kunna tamutu, iska yakara fuzarwa hawaye masu zafi suka zubomai baitaba sani rana zaizo dazaiji yanajin tsanan Ni’ima ba sai yau jiyayi ya tsaneta completely, bazaima so yaganta ba ko ya kalleta sai iya shaketa, yana ahaka wayanshi yahau ringing share fuskanshi yayi ya daga wayan Ni’ima yagani na kiranshi harta katse wayan bai daukaba tanamai kira na biyar ya daga yakai kunne baiyi magana ba, murya chan kasa tace “Baban Yaseer dama nakira nacemaka kayakuri ne da duk abubuwan dana maka natuba dan Allah let’s forget the past and move on for the sake of yaranmu” Wani kaluluwan abu Baban Yaseer yaji yana tasomai yana zuwa wuya Ni’ima tace “Babyna kaji nasan bazaka iya fushi dani for long ba please kayakuri” kasa rike abun dake wuyan nashi yayi cikin tsantsan tsana yace “bazan taba dawo dake ba, and for yarana ko da ke ko bake zasu rayu, na tsaneki Ni’ima na tsaneki da ko muryanki banso na sake ji, I hate you with everything in me, na tsaneki” yazare wayan ya katse ya jefar yazauna akasa yana dafe kanshi yashiga kurma ihu sosai kaman mahaukaci he’s so heartbroken, gateman yazo yana buga kofansu yana “Alhaji lafiya, Alhaji Alhaji”.EPISODE Ammi na zaune wuraren 11 tana duba wani littafin azkar while Hawwa na bacci sosai mai nauyin gaske taji kamshi ya daki hancinta mai dadi har saida tadago kanta ta kallo kofa Khaleel ta hango jikin kofan dago kan datayi yasa ya matsa da sauri gefe, shiru Ammi tayi saikuma ta kalli Hawwa dake bacci mai nauyi massage din yamata dadi ga drip ana samata ta lullube mata tundaga ciki har kafafu da bargo daga cikinta zuwa kai abude kanta babu dankwali tayi kyau sosai, she’s sure shine yaron jiya shine mijin Hawwa kunya yakeji ne kome? Lallai yaron kam akwai kunya yana abu saikace barawo, Ammi tayi murmushi tana tashi ta taho wajen kofan tabude tafito, Khaleel na tsaye jikin kofan yana sanye da riga da wando masu kyau milk adan hankali yace “good good morning Mom” saikuma yajuya zai tafi dasauri batare daya jira amsan Ammi ba, ahankali Ammi tace “Ibrahim” chak ya tsaya yadan juyo kanshi akasa, dan murmushi kadan tayi tace “bazaka duba matar taka ba? Dan zauna da ita nima kafafuna sunyi tsami bari nadanyi tafiya cikin asibitin kadan” kafin yayi magana ta wuce yabi Ammi da kallo saida yaga tafice sannan yajuyo ya kalli dakin kafin ahankali yabude kofan ya shiga maida kofan yayi yarufe ya tsaya jikin kofan yana kallon Hawwa dake bacci mai nauyi hakanan kawai yaji kirjinshi na bugawa sosai dum dum dum! Gently yadaga kafanshi yataka zuwa gaban gadon ya tsaya tareda folding hannu a kirji yana kallonta, she looks very sick and beautiful a hospital gown din, har lokacin akwai bandage a goshinta but an cire na hannuwanta ga ciwuka a hannu, ahankali yadaga hannunshi yakai gently yadaura kan left hand dinta wani kalan shock yaji baisan sanda yarike hannun gam ba tareda sauke ijiyan zuciya sannan ahankali yakai yatsanshi yana shafa ciwon hannun wanda yasan Ni’ima ne tamata cus yana mota data tattake mata hannu haka murya chan kasa yace “why will you love a girl this much?” Yabi hannun da kallo that felts super soft kaman hannun little Noor ga nails nata so long and white and clean looks so sexy, mirginowa Hawwa tayi kanta zai fadi daga filo dasauri yakai hannunshi yatare fuskanta yafado cikin palm dinshi tana sauke ijiyan zuciya daya huro a hand nashi cikin muryan bacci tace “Ammiiii” wani irin lankwasa kai Khaleel yayi yana kallon fuskanta dake cikin hannunshiHer face is so damn soft, baitabajin wani excitement dan mace ta shiga jikinshi ba but right now he’s feeling so good, tsareta da idanu yayi yana kallonta ya duko a tsaye fuskanta na cikin hannunshi, kaman mai whispering yace “Hawwah!” Kar Hawwa tabude idanunta saida gabanshi yayi wani mummunan faduwa yanda take kallonshi da very very bright eyes saikuma tamaida idanun tashiga kullewa suna juyawa, muryan Baba yaji awaje dawani kalan sauri yazare hannunshi fuskan Hawwa ya kife anan kasan filo daidai Baba na bugo sallama yana shigowa tareda Ammi da Ramla dakuma wasu mata guda uku, biyu daga cikinsu goye da yara abaya daya babu yaro abayanta somehow somehow they look like Baba, Ammi ta wuce tana gyara fuskanta, Baba yace “Ibrahima kana nan? Ka kannin matarka Hawwa ku gaisa Khadija” Babban wacce ita kebin Aminu Khadija tace “ina yini Yaya Ibrahim” akunyace Khaleel ya gyadamata kai, Hafsa tace “ina yini Ya Ibrahim yamai jiki” Maryam tace “ina yini ya Ibrahim” Ramla itama tace “Ya Ibrahim ya jikin Ya Hawwa” kaman bai iya magana baisaba da mutane haka ba ana kiranshi Yaya Yaya yace “da…da sauki” yakalli Baba akunyace yace “Baba zan tafi zan dawo anjima” Baba yace “muje na takamaka” shida Baba suka wuce suka fita suna fita Khadija da Hafsat da Maryam da Ramla suka shiga tafi saikuma sukahau rawa, Hafsa tace “wlh mijin Ya Hawwa yahadu Wayyoo Allah na I’m so happy for Yaya Hawwa” Ammi tace “kunga karku tadamin yarinya da surutu” duk dariya sukayi sukahau hira.Around 4 DIG yazo hospital din tareda Abraham da Hayatu Baba yamusu iso suka gaisa sosai, suka ijiye kudi da basket na so many goodies sannan sukama Baba sallama suka tafi.Shima Aminu around 4 yashigo asibitin Baba yadingamai fada akanme zaibar school yazo….Wuraren 7 Khaleel yashigo asibitin Salman na binshi da shopping na kayan kwadayi daban daban yarike hannun Noor data isheshi da maganan Hawwa ga teddy a hannunta looking so pretty sukai ciki, tundaga glass na kofan ya hango Hawwa zaune kan gado an ijiyemata table da abinci daban daban kekai Ammi na kaimata abinci abaki tana kaudakai tana yatsine fuska idanunta sun kumbura na kuka da bacci, ga Baba shima tsaye kansu suna fama dataci abinci murya chan kasa Khaleel yace “she’s such a child” dasauri Noor tace “Daddy mekace?” Kallon Noor yayi baiyi magana ba tace “Daddy let’s go inside I want to see FAA” dan ijiyan zuciya ya sauke yasa hannu yayi knocking tareda bude kofan Noor tasaki hannunshi tai ciki da gudu tace “My Fairy Angel Anty” Hawwa tadan bude idanu tana kallonta kawai Noor tahau gadon ta gefen Ammi ta tattaka tafada jikin Hawwa ta rungumeta tsamtsam da karfi Hawwa itama ta rungumeta yarinyar is freaking cute and adorable.Baba yace “Ibrahima shigo ga wuri” yabashi plastic chair shi Baba yakoma kan dogon kujera ya sauna su Salman suna shigo suna
Chapter 45 · 0% Book details