← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 21

Sashe 9

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t

SHAFI NA BIYAR

A hargitse ya wurgar da ledar hannunsa jikinsa yana rawa ya ƙarasa ya riƙe hannun matar ya ce.
"Umman Sumayya wace ce ta mutu?"
Sototo ta yi tana kallonsa da mamaki, ganin haka ya sa shi girgiza hannunta yana ƙara tambayarta. Don haka ta ce.
"Fauwaz wai kana nufin ba ka san Abida ta rasu ba? Ina ka je ne?"
Bai jira ta dire kalamanta ba ya faÉ—a cikin gidan a guje, ita da ragowar matan da ke tsaye suka bi shi da kallon tausayi.
Kai tsaye É—akinsu ya shiga, sai dai yana shiga ya hango katifarsu da kayan da ya fita ya bar Abida da su a jikinta. Da wani irin sanyin jiki ya shiga, don har lokacin zuciyarsa wasu-wasin abin da kunnuwansa suka ji take yi.

'Abida ba ta mutu ba, É—azu fa na fita na bar ta a wurin nan.'

Zuciyarsa ta raya masa, amma sai É—aya tsagin zuciyar tasa ya ankarar da shi.
'Idan ba ta mutu ba tana ina? Shin Umman Sumayya za ta yi maka ƙarya ne?'
Cikin sauri ya fita daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Tani ya shiga. Daga can jikin bango ya hango Goggo Jamila ƙanwar mahaifinsu tana kuka, sai Tani da ke lungu tana sharɓar kuka waɗansu kitika-kitikan ƙawayenta suna rarrashinta, waɗanda sune suke sake ɗora Tani a duk turbar da take kai.

"Kaico mutuwa! Yanzu shi kenan Abida ta tafi, yanzu ko kallon Fauwaz na yi dole hankalina ya dinga tashi. Yaran nan kullum suna tare, ta ina zai fara jure rashinta."
Tani ta furta cikin kururuwa, ilahirin mutanen da ke ɗakin suka bi Fauwaz da kallon tausayi. Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi, sai kuma ya ji wani irin sanyi tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya fita daga ɗakin duk da ya ji Goggo Jamila tana ƙwala masa kira.

Yana fita ƙofar gida ya ga Sumayya ƙawar Abida tana kuka, tana ganinsa kukanta ya ƙaru ta ce.
"Yaya Fauwaz wai shi kenan ba zan sake ganin Abida ba? Shi kenan mun daina wasa da su 'yar gala-gala?"
Motsa bakinsa ya shiga yi sai dai ya gagara furta koda kalma ɗaya, da sauri ya wuce ta ya nufi maƙabartar cikin sauri da yake a cikin unguwarsu take, yana fatan ya ga koda gawar Abida ce. Sai dai yana shiga ciki ya hango mutane suna fitowa, bai fasa tafiya ba har suka haɗu a hanya. Mahaifin Sumayya ne ya ce, "Fauwaz ina ka shiga tun ɗazu ana ta nemanka?"

"Hmmm zai wuce ya tafi yawon banza, tun da shi ya saka a gaba. Me ka zo yi maƙabartar? Ai da ka yi zamanka a can ba sai ka zo ba."
Abba ya furta yana yin gaba, ba tare da ya jira cewar Fauwaz ba. Yawancin mutane wuce shi suka yi, sai tsiraru da suke yi masa ta'aziya.

Zannur abokinsa ne ya dafa shi ya ce, "Ka yi haƙuri Fauwaz, mu ƙarasa ka yi mata addu'a ba."

"Me ya sa ne Zannur? Me ya sa rayuwa ta juya mini? Me ya sa duniyar ta yi mini zafi? Na rasa Umma a daidai gaɓar da ban zata ba, ga shi yanzu mutuwar Abida ta shammace ni. Me ya sa Abba ba zai fahimci halin da nake ciki..." Kuka mai tsuma zuciya ya ƙwace masa.

"Saboda kowanne bawa akwai launin ƙaddarar da ke bibiyarsa, taka a haka ta zo maka. Ina fatan za ka yi addu'ar Allah sa haka ne mafi alheri. Yanzu mu je ka yi mata addu'a."

Zannur ya furta yana jan hannunsa, cikin kuka Fauwaz ya ce.
"Ina jin kamar ba zan iya zuwa na ga kabarin Abida ba."

"Za ka iya, domin addu'arka tana da muhimmanci a gare ta."
Da tausasawar Zannur Fauwaz ya ƙarasa gaban kabarin Abida, sai da ya ci kuka mai isarsa sannan ya kwarara mata addu'a. Tsakanin kabarin mahaifiyarsu da na Abida babu tazara sosai don haka ya ƙarasa ya yi wa mahaifiyarsu addu'a suka fito daga maƙabartar. Koda suka ƙarasa gida zaune ya yi a ƙofar gida, komai da kowa ya fita daga rayuwarsa. Domin ji ya yi rayuwar ta ishe shi, har fata yake yi ina ma ajalinsa ya riske shi domin ko kaɗan gani yake ba zai iya jure rashin Abida ba. Yana daga nesa yana hango mahaifinsa yana ta karɓar gaisuwar mutane. Yadda yake haba-haba wurin karɓar ta'aziyya ya sa shi tuna mahaifinsu na baya da ke bakin ƙoƙari wurin ganin ya kula da damuwarsu. Don a yanzu gani yake kamar an canza musu shi, haka aka cigaba da zaman makoki dangin mahaifinsa suna lallashinsa da ba shi baki.

A cikin waɗannan kwanakin rayuwar ta yi masa sauƙi a fanin kyara, hantara da ƙalubalen da yake fuskanta a ɓangaren Tani da mahaifinsa. Sai dai ji yake da za a dawo masa da Abida da ya gwammaci ya cigaba da zama a cikin ƙuncin rayuwar da yake ciki. Wani babban abin da ya ɗaure masa kai da Tani yadda take haba-haba da shi, har idan aka gama girki take aikawa a kira shi, ta sa a ba shi nasa daban wai ya ci ya ƙoshi kada ya zauna da yunwa. Sai dai hakan ba ƙaramin sake hura wutar ƙiyayyarta ya yi a zuciyarsa ba, don haka a kodayaushe ta yi masa maganar abinci kalma ɗaya yake furta mata ya ƙoshi. Su kuwa dangin Abba ban da farinciki babu abin da suke yi, don Goggo Jamila cewa ta yi tabbas Fauwaz ba zai yi maraici ba.

Ranar sadakar bakwai da safe, Abba yana zaune bayan da aka gama addu'ar bakwai kira ya shigo wayarsa. Saboda haniyar mutane sai da ya fita daga cikinsu ya koma bakin masallacin da ke kallo su, sannan ya É—auka cikin sallama. Ba a iya amsa masa ba, sai jawaban tashin hankalin da aka rattabo masa. Tun bai gama wayar ba, ya zame hular kansa yana faÉ—in.

"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"

Shiru ya yi ya cigaba da sauraro har aka gama jawabin aka yanke kiran, daɓar ya zauna a kan dandamalin da ke gaban masallacin cikin firgici da tashin hankali ya ce.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Allahumma ajir ni fi musibati, wa aklifni khairan minha."

Yana gama faÉ—ar haka ya yanke jiki ya faÉ—i.

KAWU SANI

Murmushin takaici Kawu Sani ya saki, Inna ta sake tsuke fuska don a wannan karon ta ci alwashin dole Malam Hasan ya bi umarninta.

"Ina ce wannan tsohuwar magana ce Kulu? Ba tun kafin Zuwaira ta yi auren farko aka yi maganar ba yaron nan ya ce ba ya yi mata son aure sai na 'yan'uwantaka?"
Kawu Sani ya wurga mata tambaya, Inna ta cure baki wuri É—aya ta ce.
"Haka ne."
Kawu ya ce, "To a yanzu ma babu ita..."

"Don Allah ka yi.haƙuro Kawu, Baban Fatihu zai aure ta a wannan karon."
Rakiya ta yi ƙarfin halin furta haka, wani irin kallo Malam Hasan ya wurga mata cikin wata irin murya ya ce, "Ni na furta miki haka Rakiya?"
Rakiya ta girgiza kai sannan ta ce, "A wannan karon matuƙar ba ka auri Zuwaira ba ni ma na gama zaman aure da kai."
A wannan karon shiru É—akin ya yi, Kawu Sani ya numfasa ya ce.
"Ka ji abin da matarka ta ce?"

GyaÉ—a kai Malam Hasan ya yi sannan ya ce, "Na amince zan aure ta."
Rakiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci tana jin kishin mijinta, domin idan ta ce ba ta ji kishin kalamansa ba ta yaudari kanta. Amma ta san hakan shi ne kwanciyar hankalinsu gabaɗaya, don ba za ta taɓa manta tarzomar da suka sha a shekarun baya ba.

"AlhamduLillah! Ma Shaa Allah, Allah Ya yi maka albarka Hasan. Ubangiji Ya haÉ—a kan iyalinka."
Kawu Sani ya furta sannan ya mayar fa kallonsa wurin Inna ya ce. "Kada na ji ko na ga wata fitina ta ɓullo daga wurin Zuwaira, domin ke da ita duka bakinku ɗaya." Inna ta amsa masa zuciyarta fes don ta san ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli ya ci riba.

Zuwaira tun da ta ji maganar aurenta da Malam Hasan ta shiga firirta da feleƙe, sai dai duk abin da take yi ko kaɗan Rakiya ba ta nuna mata alamar ta fahimce ta na. A cikin kwana biyun da suka yi tsangwamar da Inna take yi mata ta yi sauƙi, sai dai duk wanda ya zo gaisuwa sai ta ji wata mummunar magana daga gare shi wacce za ta sosa mata rai. Ana cikin haka har Malam Hasan ya koma ya kwaso musu kayansu, wanda ya tabbatar mata da Kawu Sani ne ya ba shi kuɗin ɗawainiyarsu.

ÆŠakunan da ke cikin gidan ciki da falo-falo ne guda biyu, sai falle-falle guda biyu. Ciki da falon É—aya su Rakiya suka É—auka, sai Inna ta haÉ—e kayanta a ciki da falo É—aya ta ce idan an É—aura aure Zuwaira ta É—auki falle-falle guda biyu. Satinsu É—aya da komawa Malam Hasan ya kama awakinsa da Inna take yi masa kiwo guda biyu ya sayar, sai suka rage saura tinkiya É—aya da rago É—aya. Da wani kaso daga cikin kuÉ—in ya biya sadakin Zuwaira, ragowar kuÉ—in kuma ya kafa jarin turare irin wanda ake yawo da shi a kwando ana sayarwa da kayan yari na cikin glass.

Yadda Zuwaira take rawar kai abin ba ƙaramin ba wa Rakiya mamaki ya yi ba, saboda wasu kalaman da abin da take yi sam ba su dace a gaban Inna ba. Amma sai ta ga ita Inna ko a jikinta, a daren ranar Malam Hasan bai shiga gidan ba sai bayan sallar isha'i. Hannunsa ɗauke da kwandon turarensa, ɗakin Rakiya ya shiga ya same ta zukuɗum tana tunani.

"Rakiya ba za ki daina tunanin nan ba? Ko kina son ki dinga É—aga mini hankali idan na fita."
Malam Hasan ya furta cikin damuwa, ganin haka ya sa ta saki murmushin yaƙe ta ce.
"Tunaninka nake yi fa ba na Fatihu ba."
Ya É—an haÉ—e fuska cikin wasa ya ce, "Kina tunanin É—anki dai."
Ta saki murmushin yaƙe ta ce, "Har abada ba zan daina tunanin Fatihu ba."
Chapter 9 · 0% Book details