Sashe 7
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wani irin sanyin jiki Rakiya ta matsa kusa da shi, ta zuba masa ido tana karantar mummunan yanayin tashin hankalin da yake ciki ta ce.
"Koda wasa kada ka yi ja-in-ja da mahaifiyarka. Tabbas ana sake mata, amma duk duniya babu mai maye maka gurbin mahaifiya. Ba tun yau Inna take gwada mini ƙiyayya ba, amma a wannan gaɓar ta zarce kowanne lokaci."
Rakiya ta ja gefen hijabinta ta share hawayenta sannan ta cigaba.
"Ban ga laifin Inna ba, domin kowacce uwa tana son ganin zuri'ar 'ya'yanta. Ni kuma kalar ƙaddara ta kenan ta rashin haihuwa, sai dai ba yin kaina ba ne..."
Kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata, Malam Hasan zai yi magana ta katse shi da cewar.
"Baban Fatihu ka bi mahaifiyarka, ni kuma zan tafi duk inda Allah Ya ƙaddara zamana zai ƙare a can."
"Ba za ki tafi ko ina ba Rakiya."
Malam Hasan ya furta cikin hargitsattsiyar murya mai cike da zallar ɓacin rai, sannan ya ɗora da cewar.
"Koda ace ba ki kasance matata ba, haƙƙina ne na kula da ke matuƙar ba kya ƙarƙashin wani."
Za ta sake magana ya riƙe hannunta da ƙarfi suka fita daga gidan, kai tsaye gidan Kawu Sani suka ƙarasa. A lokacin da suka shiga Kawu yana tsaye a bakin ƙofar ɗakinsa yana rufewa, kallo ɗaya za ka yi wa su Malam Hasan ka fahimci kwanciyar hankali ta bijirewa gangar jikinsu.
"A'a, yau Hasanu ne da farar safiya haka?"
Kawu Sani ya furta yana ɗan faɗaɗa fara'arsa. Murmushin yaƙe Malam Hasan ya saki ya ce, "Mune Kawu, barka da safiya."
Kawu Sani ya amsa sannan suka gaisa da Rakiya wacce fuskarta ta yi jajir saboda kuka. Iya matarsa ce ta ƙarasa suka gaisa, tana shirin kai su ɗaki Malam Hasan ya ce.
"Kawu dama ba zama muka zo yi ba, akwai maganar da take tafe da mu."
Kawu Sani ya girgiza kai ya ce, "Hmmm Kulu ce ko?"
Malam Hasan ya gyaɗa kai sannan ya kwashe duk abin da yake faruwa ya sanar da shi. Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin faɗa-faɗa ya ce.
"Indo wai yaushe Kulu za ta yi hankali ne? Wanne irin rashin hankali take son aikatawa haka? Yara sun rasa ɗansu ko gawarsa ba a binne ba take ƙoƙarin sake saka su a wani tashin hankalin."
Iya da ke gefe ta furzar da iska mai zafi ta ce.
"Wallahi a kullum lamarin Kulu yana sake ba ni mamaki, wai me ya sa wasu iyayen suka fi ƙuntatawa 'ya'yan da suke fi yi musu biyayya? Saboda Allah ina adalci a cikin hukuncin da ta yanke, rayuwa da mutuwa duk a wurin Allah suke, sai kace ba ta san ƙaddara ba."
Kawu Sani ya girgiza kai ya dubi su Malam Hasan ya ce.
"Ku wuce mu je gidan, wallahi idan Kulu ba ta yi wasa ba sai ranta ya yi mummunan ɓaci."
A É—an sanyaye Malam Hasan ya ce. "Amma Kawu don Allah kada ta..."
"Kada ka damu na san yadda zan ɓullo mata."
Kawu Sani ya katse shi, sannan suka wuce can wurin Inna.
Lokacin da suka ƙarasa gidan a soro suka ci karo da Zuwaira, tana ganin Kawu Sani ta haɗe fuska murya ciki-ciki ta ce.
"Sannu da zuwa Kawu..."
"Wuce ciki mu je baƙar munafuka."
Sum sum sum Zuwaira ta juya ta shige ciki, tun daga tsakar gida Kawu Sani ya fara ƙwala wa Inna kira.
"Kulu! Ke Kulu ko sai na shigo É—akin?"
Inna ta fito fuskarta a cunkushe ta ce, "Ga ni Yaya."
Kawu Sani ya janyo hannun Malam Hasan ya ce, "Maza zo ki tsine masa, na ce ki zo ki tsine masa sakarai wacce ba ta da hankali. Wato so kike ki sabauta yaron nan ko ki saka masa hawan jini ki tsugunnar da shi ko Kulu?"
Inna ta sake haÉ—e fuska ta ce, "Yaya kai ne ba ka san abin da ya faru..."
"Idan ba ki yi mini shiru ba sai na ci mutumcinki, wai Kulu yaushe za ki gane Allahn da ya busa miki numfashi, Shi ya dasa miki ƙwan da kika haihu ba tare da sisin kwabo ko wayo da dabararki ba? An ya Kulu kina son ki wanye lafiya kuwa?"
GabaÉ—aya shiru suka yi wurin ya yi tsit, Kawu Sani ya nuna Zuwaira da yatsa sannan ya ce.
"Ke kuma daga yau, idan na sake jin kin faÉ—a wa Rakiya wata magana ke ko kallon banza kika yi mata wallahi tallahi sai na tattaka ki." Ya waiga wurin Inna ya ce.
"Yanzu zan samu mai gari da Malam Liman a suturta yaron nan, zuwa nan da dare za mu zauna mu tattauna."
Kawu Sani ya juya zai fita, har ya je bakin ƙofa ya waigo ya ce. "Idan kun ga dama bayan na fita ku cigaba da rashin mutumcin da kuka saba. Kai Hasan zo mu je." Ajiyar zuciya a fili Malam Hasan ya saki, jiki a sanyaye ya rufa wa Kawu baya suka fita.
Bayan fitar Kawu daga Inna har Zuwaira babu wacce ta yi mata magana, ganin haka ya sa Rakiya ta ɗan samu ƙwarin gwiwar shiga ɗakin da gawar Fatihu take. Tana tsoma ƙafa cikin tsawa Inna ta ce.
"Kada ki sake ko da wasa ki taɓa mini gawar jikana. Idan kin so kuma kin ga dama kina iya haihuwar naki, tun da ke dai kin zama ƙaddara wacce ba ta da zuciya."
Shiru Rakiya ta yi sannan ta fito bakin bishiyar darbejiyar da ke tsakar gidan ta zauna. Tana nan zaune Zuwaira ta fita ta fara sanarwa da maƙota, cikin ƙanƙanin lokaci maƙota da abokan arzikin Inna da suka cika gidan. Sai dai a yadda Rakiya ta lura kowacce mace ta shigo da irin wulaƙantacan kallon da take jifanta da shi. Wanda hakan ne ya alamta mata ruwa ba ya tsami banza, don ta tabbata akwai maganar da Zuwaira ta sanar da su a kanta.
"Don Allah ki dubi yarinyar nan kamar mutuniyar arziki, yanzu wa zai ce za ta iya aikata rashin imanin nan haka."
Rakiya ta ji wata tsohuwa ta furta ƙasa-ƙasa, tana cikin nazarin kalaman tsohuwar ta sake jin wata ta ce.
"Ke kuma Tatu kamar ba ki san karuwancin matan birni ba? Yoo shi ma Hasan É—in ai an ce ba banza ta bar shi ba."
Wata tsohuwa da ke kusa da Inna, wacce kana ganin yanayinsu za ka fahimci ita ce babbar aminiyar Inna ta karɓe zancen da cewar.
"To Allah na tuba kya ce ita, ai ki ce ubanta tuni ya gama da Hasan. Abin da tun bai san kansa ba ake ba shi a ruwa da abinci yake ci me ya rage kuma? Ai wallahi matuƙar kika cigaba da zama Kulu za ki zaunau ganin idonki."
Inna ta sake yin tsumu abin duniya yana sake damunta, cike da sanyin jiki ta ce.
"Abuwa ya zama dole na É—auki matakin da ya dace."
"Atoh ke da É—anki amma wata juyar banza ta fi ki iko da shi ina dalili."
Abuwa ta amsa cike da taƙama tana jifan Rakiya da mugun kallo, don yadda take ɗaga murya da gayya take faɗa don Rakiya ta ji. Suna cikin tattaunawa Malam Hasan da wasu maza biyu suka yi sallama domin ɗaukar gawar Fatihu. Kai tsaye ƙaramin ɗakin da aka suturta shi suka shiga, lokacin da Malam Hasan ya rungumo Fatihu suka haɗa ido da Rakiya. Wani sabon kukan ta fashe da shi, duk yadda ta so tausar zuciyarta sai hakan ya gagara.
"Yaya haka kawai nake jin kamar ba zan rayu da Fatihu ba, don Allah ga amanarsa nan, ki yi masa duk abin da mahaifiya za ta yi wa É—anta. Domin na yarda da ke, kuma Fatihu É—anki ne. Zan so ki tuna da wasiyar nan tawa a ranar da Fatihu ya zama magidanci, a ranar da za ki aurar da shi domin wannan ranar ita ce mafi mafarinciki ga kowacce mahaifiya."
Kalaman bankwanan da mahaifiyar Fatihu ta yi mata a baya suka faÉ—o mata a rai, cikin wata irin murya da ba ta yi zaton kalaman za su fito ba ta ce.
"Shi kenan ba zan ga auren Fatihu ba? Shi kenan yadda na rasa Hafsatu mahaifiyarsa shi ma na rasa shi? Na rasa Fatihu mai É—ebe mini kewa kenan Baban Fatihu?"
"Ban yi zaton Ruƙayyar da na sani mai sanin hukunci da dokokin Ubangiji za ta cigaba da furta waɗannan kalaman ba. Na yi tsammanin ke ce mutum ta farko da za ta lallashe ni a kan babban rashin da muka yi." Malam Hasan ya furta mata haka a lokacin da ya ƙarasa gabanta da gawar a hannunsa.
"Ruƙayya!"
Ya kira sunanta da wata irin muryar mai taushi, wacce take bayyanar da zallar soyayya, kulawa da tausasawa. Ba ta iya amsa masa ba sai ido da ta zuba masa waÉ—anda suka kaÉ—a jajir tana hawaye, ya sake kwantar da murya ya cigaba.
"Yana da kyau ki tuna, Ubangijin da Ya ba mu Fatihu yana iya ba mu ninkinsa a lokaci guda..."
"Amma ba da wannan juyar ba."
Furucin Inna ya katse shi, waigowa suka yi lokaci ɗaya suna kallon Inna. Matan gidan da suka shigo gaisuwa duk suka yi carko-carko, don tun lokacin da ya ƙarasa wurin Rakiya suka saki baki da hanci suna bin su da kallo. Wasu su ce ta mallake shi, wasu kuma su ce mahaifinta ne ya mallake mata zuciyarsa, shi ya sa yake mutuwar sonta ya gagara rabuwa da ita.
"Hasan kai muke jira fa."
Kawu Sani ya furta, ganin Inna ta yi tsaye a gabansu ya sa shi cewa.
"Lafiya dai Hasan ko da wani abu?"
Cikin sauri Hasan ya ce, "A'a babu komai mu je Kawu." Daga haka ya wuce suka fita da shi, sai dai har ya kai soro yana jin gunjin kukan da Rakiya take yi mai tsuma zuciya. Inna kuma ta koma ta zauna ƙawayenta suka cigaba da ƙus-ƙus suna zuga ta. Cikin lokaci ƙanƙani aka sallaci Fatihu aka kai shi makwancinsa, da yake rasuwar ƙaramin yaro ce daga mutanan ƙofar gida har matan cikin gidan ba su wani daɗe ba kowa ya watse sai tsirarun ƙawayen Inna da suke shirin ganin ƙwal uwar daka.
BAYAN SALLAR ISHA'I