← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 21

Sashe 15

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t

SHAFI NA TAKWAS

Abba ya yi mamakin jin furucinsu, don haka ya ce.

"Amma don Allah ko zan san wanda ya turo ku wurina?"

Wani baƙi daga cikinsu wanda ya kasance mai ƙaton ciki ya girgiza kai ya ce, "Babu buƙatar haka, idan mun je ofis za ka ji bayanin gayyatarka." Abba ya yi jim sannan ya ce. "To shi kenan, amma don Allah ku yi mini afuwa zan shiga na sanar da iyalina." A nan ba su musa masa ba, jikinsa a sanyaye ya shiga ya samu Tani a kan gado tana bacci. Tashin ta ya shiga yi a gaggauce, cikin magagin bacci ta ce.

"Lafiya Alhaji."

A gefen gadon ya zauna ya ce, "Ina fa lafiya Tani, ina cikin tashin hankali. 'Yansanda ne a ƙofar gida suka zo tafiya da ni." Firgigit ta wartsake idonta, cikin sauri ta ce.

"Yan sanda kuma? Me ka yi musu? An ya ba ɓatan hanya suka yi ba?"
Abba ya rausayar da kai ya ce, "Babu wani ɓatan hanya, tun da complete sunana suka ambata har da lambar wayata. Yanzu dai bari na je duk yadda ake ciki za ki ji daga baya." Miƙewa Tani ta yi ta biyo bayansa tana sallallami kamar abin ya dame ta da gaske. Sai da ya fita tana shigowa cikin gida ta tuntsire da dariyar ƙeta, sai da ta yi mai isarta sannan ta nufi ɗakinta ta doka sakata.

Tun da su Abba suka ɗauki hanyar Bompai yake saƙa da warwara a cikin zuciyarsa, shi dai a iya saninsa lafiya ƙalau ya rabu da mutanen kasuwarsu ballantana ya ce wani abu ne ya haɗa shi da wani daga cikinsu har ya turo masa hukuma. Har Alhaji Dikko ne ya zo masa a rai, sai ya tuna kwana biyu kenan a tsakani da ya kai masa kuɗi kuma dama duk bayan kwana goma yake rage masa kuɗinsa koda babu yawa. Yana cikin wannan yanayin har suka ƙarasa Zone 1 hedikwata. Suna shiga bayan da Abba ya zauna aka shiga karanta masa ƙunshin tuhumar da ake ƙararsa a kai.

"Shin ka san Alhaji Isa Kura?"
ÆŠan jim Abba ya yi yana nazari, don ji yake kamar ya san sunan kamar bai san shi ba.

"Mutumin da kuka yi cinikayyar filaye da shi."
Ɗansandan ya taƙaita masa dogon tunani, da sauri Abba ya ce.
"Eh na san shi, wani abu ne ya faru?"
Rubuta jawaban Abba ɗansandan ya yi sannan ya ce, "Shi ne ya yi ƙararka a kan ka zambace shi, ka ci amanarsa ka sayar masa da fili a kan fili."

Dam! Ƙirjin Abba ya buga da ƙarfi, bakinsa yana rawa ya ce.
"Gaskiya ba haka abin yake ba, yadda aka sayar mini da wurin nan ni ma haka na sayar masa da shi."

Babu wanda ya tanka masa, É—ansandan da ke É—aukar statement É—insa ya ga ya latsa waya ya kara a kunne.
"Alhaji ka taho ne?"
Amsa aka ba shi daga can ɓangaren sannan ya ce, "To sai ka shigo." Katsewa ya yi ya dubi Abba ya ce.
"Wanda ya shigar da case É—in ya shigo gidan nan, yanzu haka parking motarsa yake yi. Idan ya zo sai ka yi mana jawabi." Abba ya gyaÉ—a kansa yana ta'ajibin abin da ya faru. Suna nan zaune Alhaji Isah ya shiga fuska a haÉ—e sai muzurai yake yi.

"Ofisa ya ake ciki?"

Alhaji Isa ya furta yana kallonsu, ɗansandan ya janye file ɗin gabansa sannan ya dubi Abba ya sanar da Alhaji Isah. Rai aɓace Alhajin ya ce.

"Malam kada ka raina mini hankali, a jiya na É—ebi ma'aikata da kayan aiki kawai na je na tarar da wani mutum ya yi gini har ginin ya kusa linta."

"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Wallahi ban san yadda abin ya kasance ba..."

"Ai kuwa za ka sani, don wallahi naira biyar tawa ba za ta yi ciwon kai ba." Alhajin Ya katse Abba, nan take suka shiga musayar kalamai. Shi Abba yana ƙoƙarin kare kansa, shi ma Alhaji yana nuna dagiya a kan haƙƙinsa. Har wayarsa Abba ya ciro yana neman layin Gambo dillali amma ta ƙi tafiya. Ganin hayaniya ta yi yawa ya sa ɗansandan cewa.

"Yanzu ba abin tashin hankali ba ne, za mu yi duk cike-ciken da ya dace mu miƙa ku kotu. Idan ya so sai a yi bincike a tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyarsa, wanda ba shi da gaskiya sai a hukunta shi."
Da wannan suka tashi, a kan Abba ya saurari sammaci daga kotu. Koda Abba ya fita daga zonal kai tsaye wurin filin da ya sayarwa Alhajin ya nufa, sai dai yana zuwa ya yi turus ganin leburawa rututu suna ta aiki. Wasu suna kwaɓa ƙasa, wasu suna ɗiban bulo suna jerawa, yayin da wasu suke hawa tsani suna miƙa suminti. Ruwan mamaki ne ya wanke shi, don ya gasgata abin da ya gani ba gizo idonsa ke yi ba sai da ya tambayi ɗaya daga cikin leburorin.

"Assalamu alaikum! Don Allah tambaya nake yi."

Abba Ya furta yana mintsinin hannunsa don ya tabbatar da ba mafarki yake yi ba.
"Wa alaikassakam, Allah Ya sa mun sani."
Suka amsa masa suna zuba masa ido, sai da ya sake leƙen yadda ginin ya yi tsawo ya ce.
"Don Allah waye mai wurin nan ina nufin wanda ya ba ku aikin ginin nan."

"Amma bawan Allah ina ruwanka da mai ginin nan? Ko kai ma aikin kake son ka samu? To idan ma haka ne ya gama É—iban ma'aikata"
Abba ya girgiza masa kai, sai É—aya daga ciki ya ce.
"Mai wannan wurin ai ba bahaushe ba ne, kai ba ma ɗan ƙasar nan ba ne. Na wani ɗan china ne, idan kana jin kamfanin shinkafa na Girma rice to nasa ne." Abba yana jin haka jikinsa ya sake yin sanyi, don haka ya yi musu sallama ya wuce gida kansa yana masifar ciwo.

Yana zuwa gida Tani ta shiga É—akin ta ga lokaci É—aya duk ya firgice ya fita hayyacinsa, zama ya yi ya zuba tagumi da hannuwa biyu. Ba ta yi tsammani ba ta ga hawaye bibbiyu suna fita daga idonsa.

'Hmmm wallahi tallahi hawaye ma yanzu ka fara shi.'
Tani ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce. "Alhaji wai me yaka faruwa ne, tun fa da ka fita na kasa zaune da tsaye."

"Mene ne ma bai faru ba Tani? Komai ya rikice mini, masifa ta kowacce hanya sai faÉ—o mini take yi. Ya zan yi Tani? Mene ne mafita?"
Nan take ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar da ita, sai da ya goge hawayen idonsa sannan ya É—ora da cewa.
"Na nemi layin Gambo dillali sama da ƙasa ba ya shiga, har wurin dillancinsu na je ko za a ba ni layin da zan same shi amma sun ce mini babu, yanzu haka sun ce matuƙar ban kawo Gambo dillali ba ni ne zan ɗauki asara tun da shi ya sayar mini. Kuma har abokinsa da suka zo tare na neme shi ban samu ba, ina cikin tashin hankali Tani."

"Har yanzu ba ka shiga ba."
Tani ta yi suɓutar baki ba tare da ta san zancan zai fita ba, da wani irin kallo ya dube ta. Cikin wayancewa ta ce.
"Ƙwarai kuwa Alhaji, tun da ai za a iya samun abokinsa. Da ace babu abokin Gambon shi ne ka shiga tashin hankali." Tsaki ya saki bai tanka mata ba, suka yi shiru gabaɗaya kowannensu da abin da yake saƙa wa a cikin ransa.

Daga wannan ranar Abba ya firgice ya lalace ya fita hayyacinsa don ko abincin kirki da bacci mai daɗi ba ya yi, duk inda zai buga neman Gambo dillali ya yi amma sama da ƙasa bai same shi ba. Yana cikin wannan gaɓar Alhaji Isah ya aika masa sammaci a kotu, kuma a wannan gaɓar ce Alhaji Dikko ya taso shi a gaba da zancan kuɗinsa don ya kwashe sama da sati biyu bai waiwayo shi ba. Saboda haka abin duniya goma da ashirin ya haɗe masa, ta ko ina fuskantar matsin lamba yake don ko kuɗin da zai ɗauki lauya ba shi da su. Sun fara zaman shari'arsa da Alhaji Isa ko wata guda ba a rufa ba, Alhaji Dikko ya aiko masa da na shi sammacin daga kotu. Cikin abin da bai wuce wata ɗaya ba Abba duk ya tsururuce, ƙanwarsa Goggo da ke ba ƙarfi gare ta ba kullum cikin yi masa addu'ar samun mafita take. Abu ɗaya ne ma ya ɓata mata rai da farko har ta ɗauki fushi da shi, maganar kai Fauwaz almajiranci da ba ta ji labari ba sai bayan da ya riga ya kai shi. Saboda da ta ji da wuri ita za ta ɗauke shi ya koma wurinta da zama, duk da har lokacin ba ta gane ainahin kalar Tani ba. Sai da ta ji jarrabawar da Abba ya shiga sannan ta sauke fushinta, har take zuwa wurinsa tana sake kwantar masa da hankali.

A ranar da za su fara zaman shari'arsa da Alhaji Dikko, har ya shirya zai fita Tani ta biyo shi ta ce.
"Ji mama Alhaji ina magana."

"Tani sauri nake kada na makara."
Abba ya ba ta amsa a gaggauce, da sauri ita ma ta sha gabansa tana cewa.
"Ba daÉ—ewa zan yi ba, da ka aiwatar ne za ka yi gaba malam."
Jin yadda take yi masa magana cike da isa-isa ya sa shi kallonta, Tani ta turo É—ankwalinta gaba ta ce, "Takardar sakina za ka ba ni, don ni ba matar shan wahala ba ce."

MALAM HASAN

Ganin ta cigaba da tafiya sai ya sha gabanta da sauri ya ce.
"Ba magana nake yi miki ba Rakiya, ki tsaya ki saurare ni."
Chapter 15 · 0% Book details