Sashe 13
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna ta yamutsa fuska tana taɓe baki ta ce, "Amin, idan ma bai kai zuci ba kanki. To ina son ki sani yanzu aikin gidan nan gabaɗaya ke za ki dinga yi, har zuwa lokacin da cikinta zai yi ƙwari."
Zuwaira da ke gefen Inna tana cin É—ata tana yatsina ta yi zaraf ta ce, "Inna hatta girkin ma ta dinga haÉ—awa ranar kwanana." Rakiya ta É—ago suka haÉ—a ido, Zuwaira ta murguÉ—a baki ta cigaba da cin É—atarta. Inna ta dubi Rakiya ta ce.
"Kin ji dai abin da ta ce? Za ki dinga komai na gidan nan, idan cikin ya girma sai mu san abin yi."
Muryar Rakiya a raunane ta amsa wa Inna, bayan Inna ta sallame ta ta wuce É—akinta. Tana shiga ta zauna ta fara zubar da hawayen tausayin kanta.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[16/05, 18:10] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
https://chat.whatsapp.com/LyQRbgQCzbL9iUHgPoeyO2?mode=gi_t
SHAFI NA BAKWAI
Sai da Rakiya ta ci kukanta mai isarta sannan ta ɗebi ruwan randarta ta ɗaura alwala a ɗakinta. Don tana gudun kada ta fita, su Inna su ga fuskarta su ɗauka maganar cikin ce ta saka ta kuka su yi mata mummunar fassara. Uwar ɗakinta ta shiga ta gabatar da sallah raka'a biyu. Ta roƙi Ubangiji da ya yaye mata damuwar da ke ƙunshe a zuciyarta, bayan ta gama addu'ar ta ji sanyi a ranta don ta ji kaso mafi yawa daga cikin damuwarta ta yaye.
Rakiya ita ta cigaba da duk ayyukan cikin gidan, tun daga kan shara, wanke-wanke, wankin banɗaki da sharar turken awaki zuwa girki duk babu mai tallafa mata. Hatta abinci wani lokacin Inna cewa take ta zubo wa Zuwaira, ita dai Zuwaira sai dai idan girki ya zagayo kanta ta karɓi miji. Don ta lura a yanzu yana ba ta kulawa, kuma duk abin da ta ce tana so bakin gwargwado yana yi mata. Sai dai abu ɗaya ne ba ta jin daɗi yadda ta ga har lokacin bai fifita darajarta a kan ta Rakiya ba. Amma abin da yake damunsa bai wuce yadda ake yake cakuɗewa Rakiya ba, tun da ya lura a ɗan tsakanin nan har duhu ta yi duk da hasken fatar da take da shi. Da ya yi yunƙurin yi wa Inna magana sai Rakiya ta hana shi, saboda ta san ko ya yi maganar ba za ta sauya zane ba sai ma wani ƙalubalen da za ta sake fuskanta.
Watarana Rakiya ta gama aikin gidan tas, har ta É—ora abincin rana da yake rana ta yi. Inna ta É—ebo mata kayan wankinta, ta ce ta wanke mata nan take. Ta gaji sosai, domin bayanta har ciwo yake mata.
"Na ce Inna idan babu damuwa ko na bari zuwa gobe da sassafe sai na tashi da wankin?"
Rakiya ta furta a É—arare, Inna da har ta nufi É—aki ta waigo ta ce. "Ai da uwarki ce ta ba ki wankin ba za ki faÉ—a mata haka ba ko?" Shiru Rakiya ta yi, Inna ta gama zazzage mata rashin mutumci ta yi gaba. Babu yadda ta iya, haka ta ja kujera ta zauna, ta haÉ—a ruwan wankin don ba za ta iya wankin a sunkuye ba. Tana cikin wankin Zuwaira ta fito da nata kayan, tana zuwa kan Rakiya ta watsa mata cike da izgilanci ta ce.
"Ga nawa wankin nan, ciki ne ya hana ni iya taɓa ko rigar mama na wanke ballantawa kayan sawa."
Da ido Rakiya ta bi kayan, saboda tsabar wulaƙanci har da wandunan pant da rigar mama waɗanda suka yi duƙun-duƙun saboda datti. Rakiya ta dube ta ta ce, "Ba zan yi miki wanki ba."
Zuwaira baki ta buÉ—e cike da mamaki ta ce, "Au ni kike faÉ—a wa haka?"
"Na faÉ—a miki Zuwaira, ko kin É—auka tsoronki nake ji? Ko kuma kin yi zaton ni baiwarki ce?"
Rakiya ta furta a hassale, Zuwaira ta saki dariyar izgilanci ta ce.
"Mene ne marabarki da baiwar to? Ko kin É—auka kina da sauran amfani wanda ya wuce ki ci ki yi kashi da aikin gida?" Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da wanke kayan Inna, Zuwaira ta koma ta gabanta ta sake cewa.
"Ki yi ki mayar da hankali ki wanke mini su tas, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci. Banza juya marar mamora ballantana amfani."
Furucin Zuwaira na ƙarshe ne suka daki zuciyar Rakiya, kamar ba za ta kula ta ba sai ta ɗago ta ce. "Da Ubangiji kike, domin Shi ne ya ba ki cikin, kuma na tabbata ni ma bai manta da ni ba."
Cikin shewa irin ta izgilanci Zuwaira ta ce, "Ahayyee! Lallai fa sumumu-kasau an samu bakin magana, ai ke da haihuwa sai dai ki ga ana yi. Ko mugun halin bokan ubanki ya isa ya hana ki haihuwa...'
"Kada ki sake zagin mahaifina!"
Rakiya ta furta mata da wata irin murya gargaÉ—i, cikin raini Zuwaira ta ce.
"Uban naki wata tsiyar ce da kike kumfar baki a kansa..."
Tas! Rakiya ta sauke wa Zuwaira mari a fuska, zaro ido waje Zuwaira ta yi tana mamakin wacce ta mare ta. Don haka ta wage murya cikin kururuwa ta ce, "Ni kika mara?"
"Na mare ki, ko yanzu kika yi gangancin sake zagin mahaifina sai na ninka miki wanda ya fi shi."Rakiya ta furta tana tsare ta da ido, Zuwaira ta tsorota da yadda ta ga ran Rakiya ya ɓaci. Amma don kada ta nuna mata ta ji tsoro ya sa ta dake ta sake cewa, "An zage ki, uban naki ba boka ba ne mashiriki? Ko ba shi ya mallake Yaya..."
A wannan karon ma Rakiya ta sake sauke mata mari a fuska, ihu ta saki ta yi zaman 'yanbori a ƙasa ta ɓarke da kuka. Da sauri Inna ta fito tana tambayar abin da ya faru, Zuwaira ta dafe cikinta cikin kukan makirci ta ce.
"Ina wai don na ce ta taimaka ta haÉ—a da kayana shi ne ta hau zagina, don na rama shi ne da hau cikina da duka."
"Duka a ciki?"
Inna ta tambaya a razane, Zuwaira ta gyaɗa kai tana sake murƙususu kamar wacce aka doka da gaske.
"Amma ke dai an yi baƙar muguwa, yanzu saboda rashin imani yarinyar tana da ciki kika dake ta don ki kashe ta? Wallahi bari Hasan ya zo a yi wacce za a yi."
"Gara ya zo ɗin, domin ni ma na gaji haka. Hasan ko ɗan autan zinare a cikin mazan aure ne na gaji da shi." Rakiya ta furta a zuciye, don a wannan gaɓar ta gama zuwa bango. Da mamaki Inna ta ce, "Ni kike faɗa wa haka?"
"Duk abin da kika ɗauka Inna, na faɗa na gaji wallahi. Ai ba baiwa aka ajiye muku ba, wallahi duk abin da zai faru sai dai ya faru amma zaman gidan nan daga yau na gama shi." Rakiya tana gama maganar ta miƙe tsaye ta yarfe ruwan hannunta ta juya za ta shiga ɗaki. Da sauri Inna ta bi ta ta ce, "Au Allah rashin kunya za ki yi mini? Wankin ba za ki zo ki yi mini ba?"
Rakiya ta juyo a hassale ta ce.
"Ba zan wanke ba, ita 'yar gwal É—in gabanki ta wanke miki. Ai da ni da ita duka 'ya'ya ne."
Tana gama faɗa ta shige ɗaki tana jin zuciyarta tana tafasa. Sai da ta yi da gaske sannan ta taushi zuciyarta, don ji take kamar ta fita ta wanke Inna tas sannan ta koma ɗaki. Daga Zuwaira har Inna kasa magana suka yi, sai zuwa bayan wani lokaci Inna ta fara kumfar baki. Har aka yi sallar Isha'i kowannensu da abin da yake saƙa wa a zuciyarsa, Malam Hasan yana shigowa Inna ta fashe da kuka. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, sai da ya lallashe ta sannan ya fara tambayarta abin da ya faru.
"Wallahi yau yarinyar nan Rakiya babu irin zagin da ba ta yi mini ba, daga kawai na ba ta wanki don Zuwaira ta kawo mata 'yan ƙwayayyaki ta ce ta matse mata ta hau ta da duka. Don na yi magana ta zage ni ta ce wankin ma ba za ta yi ba." Bayan Inna ta gama faɗa masa ƙarya da gaskiya ta haska masa tulun kayan wankinta, sai bokiti da ke gefe wanda ta fara wankewa. Ransa ne ya ɓaci, don haka bai tanka wa Inna ba ya nufi ɗakin Rakiya. Koda ya shiga a madadin ya ji ta bakinta sai kawai ya rufe ta da faɗa.
"Rakiya me ya sa kika zagi Inna? Ko don kin ga ina bin bayanki ne? Kada ki manta fa mahaifiyata ce, zan iya sauya kowa da komai a duniyar nan ban da ita. Don kawai ta ce ki mata wanki, yanzu idan mahaifiyarki ce za ki ce ba za ki wanke mata ba?"
Tun da ya fara faɗa ido ta kawo ta zuba masa, ranta ya sake ɓaci a kan wanda ya mamaye ta. Sai da ya gama faɗan har ya juya zai fita ta ce.
"Hasan ba ni takarda ta na gaji."
Da mamaki ya ce, "Hasan! Sunana kike kira kai tsaye?"
"Na faɗa ka ba ni takardata na ce maka, don ina mai tabbatar maka da ko kai ne autan maza na gama zaman aure da kai. Na gaji, na gaji da cin kashin da ake yi mini duk don saoda laifin da ake ganin ni na ɗora wa kaina." Rakiya ta furta a hasaale, saboda idonta ya gama rufewa da zallar ɓacin rai. Malam Hasan ya saki dariyar yaƙe ya ce, "Ni da ke ai aurenmu mutu ka raba ne Rakiya."