← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 21

Sashe 11

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tani ta furta tana matsawa gabansa, a hankali ya dube ta cikin sanyayyar murya ya ce.
"Tani ina cikin tashin hankali."

Lumshe idonta ta yi cikin nuna damuwa ta ce, "Bari na fara kiran likita ya duba jikinka Alhaji. Saboda jininka ya hau, don haka suka ce idan ka farka a sanar da su."

"Tani babu buƙatar kiran likitoci, don lalurar da ta afko mini babu likitan da ya isa magance mini ita."
Abba ya furta da muryar damuwa, riƙo hannunsa Tani ta yi ta ce.
"Komai ya yi tsanani maganinsa Allah."

Abba ya jinjina kai sannan ya ce, "Wannan haka yake, amma abin da nake so ki fahimta. Irin wannan guguwar da ta taso mini, irinta ce wacce ake cewa gobara daga teku maganinta sai Allah."
"Alhaji har yanzu riga kake É—inka mini babu wuya, ban fahimci inda maganganunka suka sa gaba ba." Tani ta furta masa tana tsare shi da ido. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

"KuÉ—in da na ara kwanaki, waÉ—anda na zuba a kayan da aka tafi da su kwatano da Ghana ne suka halaka."

"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"

Ta furta a hargitse cike da tashin hankali ta ce, "Ban fahimci sun halaka ba Alhaji?"
Abba ya furzar da iska mai zafi ya ce, "Kayanmu ne aka kama su, sakamakon an samu ƙwayoyin hodar iblis a cikin wasu daga cikinsu, Alhaji Ɗan gaske ya ce mu yi ta addu'a idan ba a nemi masu kayan ba domin hukunta su."

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel! Alhaji wannan wacce irin jarrabawa ce? Yanzu ya za ka yi da kuÉ—in wurin Alhaji Dikko?"
Tani ta furta masa, jim ya yi yana nazari sai ya ɗago ya ce. "Wallahi ban sani ba Tani, ban san yadda za mu kwashe da shi ba." Zumbur! Ta ga ya miƙe, cikin sauri ta riƙo shi ta ce.

"Yi a hankali Alhaji, ko a kira likitan ne?" Girgiza mata kai ya yi ya sauka a kan ƙafafuwansa sannan ya ce.
"Gida zan tafi."
Duk yadda Tani ta so hana shi fir ya ƙi amincewa, sai da ya fita harabar asibitin ya ci karo da abokansa waɗanda suka kawo shi asibitin. Bayan an gama biyan kuɗaɗen da aka kashe suka wuce gida.

A washegarin abin da ya faru, sai da ta tabbatar da Abba ya fita, saboda tun a ranar Alhaji Dikko ya fara doka masa waya don ya ji makamar wurin da kuɗinsa za su ɓullo. Saboda ya ji labarin abin da ya faru da Abba a wurin mutane da dama. Abba ya tafi wurinsa ne domin ya ba shi haƙuri, ya kuma nemi alfarmar ya ɗaga masa ƙafa zuwa wani lokacin kaɗan.

Uwar ɗaki Tani ta shiga ta ciro wata lamba a takarda, sai da ta kwafe lambar a wayar sannan ta latsa kiransa. Daga can ɓangaren ta ji an ce, "Kunama mugunyar ƙwaro, ga ki da harbi mai kai mutum ƙasa." Murmushin jin daɗi ta yi, kanta ta ji ya ƙara girma. Cike da isa ta ce, "Kuma ko a yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli ya ci gwagwgwaɓar riba." Shi da ita duka suka bushe da dariya. Yadda Tani ta shagala ne ta manta da Fauwaz yana cikin gidan, Fauwaz ya fito zai fita ya ji tana cewa.

"Amma ya aka yi wannan tarkon namu ya kama shi yanzu? Ni fa na ɗauka sai tura ta kai bango. Ka san fa duka kuɗin da ya ranto na saka shi ya zuba a waɗannan kayan da yake shi mahaukaci ne." Daga can ɓangaren ya ce, "Ki ce ya ɓallo wa kansa ruwa. Yanzu kusan nawa ya ranto?"
Shiru Tani ta yi tana nazari sannan ta ce, "A ƙalla za su kai miliyan uku, kuma daɗin da na ji maganin wurin malamin nan da ka karɓo mini bai karye a jikinsa ba."

"Ke fa bala'i ce Tani, amma ki ɗan ɗaga masa ƙafa mana." Mutumin ya furta yana sakin murmushi, ita ma murmushin ta saki ta ce. "Wallahi tallahi ko Alhaji zai yi yawo tsirara ba zan rangwanta masa ba, don tun kafin yarinyar nan ta mutu tuni na yi masa farraƙu da su. Tsakaninsa da su sai tswangama, kuma duk abin da na faɗa ta zauna."

"Sai da ke 'yar kunama."

Ya furta cikin kanbabawa, jin haka ya sa ita ma ta amsa suka kwashe da dariya sai ta ce.
"Lighter ka ƙara riƙe wuta fa, saboda daga wurin Alhaji Dikko kai tsaye tashar jirgin ruwa zai nufa." Amsa mata yi sannan ta ce za ta kira shi gada baya.
Fauwaz da ke jin duk tattaunawar da Tani ta yi, duk sai ya ji tausayin mahaifinsu ya kama shi. Duk wani haushi da ƙullatar da ya yi masa ya saɓe, sai ya sake jin tsoron Tani ya sake mamaye shi. Duk yadda yake fasalta rashin imanin Tani sai ya ga ashe ta doke harsashensa.

'Yanzu ta ina zan fara nusar da Abba wace ce Tani?'
Fauwaz ya raya a ransa, ganin ba shi da tsayayyar mafita ya sa shi barin wurin ya shiga ɗakinsa yana tunanin yadda zai ɓullo wa al'amarin.

Tun daga wannan ranar kwanciyar hankali ta yi ƙaura a wurin Abba, ban da Tani da a zahiri take nuna masa tana cikin damuwa amma a baɗini ta fi kowa farinciki da al'amarin da ya same shi. Sai dai kuma ba ta so al'amarin ya faɗo a daidai wannan gaɓar ba, don tana gudun kada kwaɓarta ta yi ruwa tsululu asirinsu ya tonu.
A ɓangaren Fauwaz ya samu sauƙin tsauwalawarta da ta Abba sosai, saboda kusan kullum mahaifin nasa ba ya zama a gida. Yau yana tashar jirgin ruwa yana fafutukar a saki kayansa, gobe yana ƙofar gidan Alhaji Dikko. Ita kuma Tani ya rasa abin da take ƙullawa kusan kullum da mahaifinsa ya fita take shurar takalminta ta fita.

Ana cikin haka ne wani a cikin tashar jirgin ya ce zai yi masa hanyar da kayansa za su fito, amma sai ya biya kuɗi kusan dubu ɗari biyar. Jin haka ya sa Abba ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya dinga buga-buga tsakanin abokan kasuwacinsa na goro ya ranto kuɗi dubu ɗari biyar. Tun da Abba ya byar da kuɗin, mutumin yake yi masa yawo da hankali. Yau yace ba ya nan gobe ya ce an tura shi wani gari, daga ƙarshe ma har ya daina ɗaukar wayarsa. Ana cikin haka Alhaji Dikko ya tayar masa da ɓalli, don har hukuma ce ta shiga tsakaninsu. Don haka Tani ta shawarce shi da ya sayar da gonakin da ya saya idan ya so sai ya biya kuɗaɗen da suke kansa.

Kai tsaye lambar Gambo dillali ya nema, amma sai ya ji ta a kashe ba ta shiga. Da yake a buƙace yake da kuɗi kai tsaye 'yan dillalai ya nufa yana nemansa. A nan mutanen wurin suka jaddada masa cewar ya bar garin, sakamakon dama can asali ba ɗan jihar Kano ba ne. Buƙatar da ke tafe da shi ya sanar da su, a nan Shamsu dillali ya shige masa gaba wurin tallata ƙaton gonakin nasa. Ko sati guda ba a rufa ba cikin hukuncin Ubangiji aka yi dace da samun mai saya, bayan da suka je aka duba gonakin suka yi ciniki ya ɗebo takardu ya miƙa masa. Da yake sun ga a buƙace yake da kuɗi bai wani ci riba da gonar ba, don kusan yadda ya saye su haka ya sayar da su. Yana karɓar kuɗin kai tsaye ya kai wa Alhaji Dikko ko gida bai koma ba, ya kuma nemi alfarmar ya ɗaga masa ƙafar sauran zuwa wani lokacin. Sai da suka yi rubutu a gaban wani ɗansanda kowa ya saka hannu sannan Abba ya wuce gida.

Tun bayan fitarsa Tani ta cika fam da farinciki, a lokacin Fauwaz yana ɗebo ruwa yana zubawa a drump. A wani zuwa da ya yi zai juye ruwan ya ji muryarta can ƙasa tana cewa.
"To yanzu me ya rage? Ai ƙarshen tuka-tuka tik, mun yi waya da shi ya sayar da gonar. A tsammaninsa sayar da wannan gonar shi ne rufin asirinsa, bai san ɗaya daga cikin manyan ƙofofin tashin hankalinsa ne suka buɗe ba." Amsa mata aka yi daga can ɓangaren sai ta cigaba, "Wai ka san waye Alhaji Dikko a kan kuɗi kuwa? Kai dai ka zuba ido ka sha kallo."

Fauwaz ji ya yi zuciyarsa ba za ta iya ɗauka ba, don haka ya sauke bokitin kansa ya ƙarasa cikin ɗakin ya ce.
"Ke wacce irin mace ce da ba ta tsoron Allah?"

"Irin wacce mahaifinka yake muradin rayuwa da ita."
Tani ta ba shi amsa tana tsare shi da ido, wata irin tsanarta ta sake mamaye shi. Ya dube ta ido cikin ido ya ce. "In Shaa Allahu yau zan sanar da Abba wace ce ke, da irin cutarwar da kike yi masa." Wata irin dariyar izgilanci ta saki ta ce.
"Ai babban kuskuren da ka tafka a rayuwarka shi ne gangancin sauraron kalaman da nake yi yanzu. Waɗanda suka ingiza ƙeyarka har ka tsoma mini baki, kana tsammanin furucinka zai yi tasiri a wurin mahaifinka?"
Ta wurga masa tambaya tana tsare shi da ido, shi ma ita yake kallo babu ƙiftawa. Yana jin kamar ya yi tsalle ya maƙure wuyanta, yana nan tsaye ya ji ta cigaba.
"Da ace kalamanka suna da tasiri, da a daren da ƙanwarka za ta yi mushe sun ratsa jikin mahaifinka."

Dum! Ya ji a tsakiyar kansa tamkar an buga masa guduma, ya runtse idonsa da sauri yana hasko fuskar Abida cikin mawuyacin hali. Tani ta nuna shi da yatsa cikin wata irin murya mai cike da zallar rashin imani ta ce.
"Ka jira mummunan saƙon da zai iso gare ka..."
Ba ta kai ga dire kalamanta ba, ta ji sallamar Abba ya shigo gidan. Haka ya sa ta saki murmushin ƙeta sannan ta rushe da kuka.

ÆŠANBATTA
Chapter 11 · 0% Book details