← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 21

Sashe 4

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duka mutanen wurin shiru suka yi, saboda kowannensu zuciyarsa babu daɗi duba da irin mummunan yanayin da take ciki. Malam Hasan ya sunkuya ya fara rarrashinta, a daidai wannan lokacin 'yan jaridar gidan Radiyo suka ƙarasa domin rahoto ya je musu. Sai da ɗan jaridar ya gabatar musu da kansa ya kuma jajanta masa abin da ya faru sannan ya ɗora da cewa.
"Malam Hasan muna son mu ji matsayinka, da kuma yadda wannan al'amarin ya kasance."
Sai da Malam Hasan ya yi ta maza sannan ya faɗa masa abin da ya faru, da ya ji tambayoyin za su yi yawa ya dakatar da su. Haka kuma da suka buƙaci jin ta bakin Rakiya ya hana su, don ya lura tambayoyin ba ƙaramin tayar mata da hankali suke ba. Sai suka koma jin ta bakin mutanen unguwa, su ma suka sanar da su gwargwadon abin da suka sani. Jin dalilin da ya sa Malam Hasan ya fito daga gidansa, ya sa mutane suka kawi taro da sisi suka haɗa musu kuɗin mota. Domin sun buƙaci da a yi wa Fatihu sutura a nan ya ce zai ƙarasa garinsu a yi a can.

Taxi suka tara tun daga titin har cikin ƙauyensu da ke garin Ɗanbatta. Sai da ya sallami mai Taxi, sannan suka ja ƙafa jiki a sanyaye suka shiga, Inna ba ƙaramin mamakin ganinsu da farar safiya ta yi ba. Malam Hasan ne ya gaishe ta ta amsa, Rakiya da fuskarta ta kumbura suntum sabod kuka ta ce.
"Ina kwana Inna."
A wulƙance Inna ta amsa sai ta ce, "Ciwon baki kike yi da ba za ki buɗe baki ki mini magana ba? Ina Fatihun yake? Ai kya miƙo mini jikana mu gaisa."
Rakiya ta sunkuyar da kai ƙasa, lokaci ɗaya ta fashe da kuka.

ALHAJI LAWAN

Alhaji Lawan yana zuwa gida cike da murna HajiyaTani ta tare shi, sai da ta kawo masa ruwa ya sha sannan ta ce.
"Alhaji sai kuma na ji ka ce an gama komai."
Alhaji Lawan ya saki murmushi yana miƙa mata takardar ya ce.
"Ga takardu ma sun zo hannu, sai ki adana mini su don kin fi ni iya ajiya."
Hajiya Tani ta zaro takardun ta duba, bayanin fasalin gonakin ne da kusurwoyinsu ta fannin tsayi da faÉ—i. Sai bayanan masu saya da mai sayarwa, jinjina kai ta yi ta ce.

"Kai amma fa kamar suna da girma sosai."
Alhaji Lawan ya gyaɗa mata kai ya ce, "Girma ma ai ba a magana, so nake sai kayan da muka tura sun sauka mun ga abin alherin da muka samu na ga me ya dace na yi wa wurin. Zan dai gina mana ƙaton gida mu huta da yawon haya, sai ƙatuwar plaza da nake son yi wacce za a zuba shaguna."
Cikin jin daÉ—i Hajiya Tanj ta É—aga hannuwa sama ta ce, "Kai Allah mun gode maka, Alhaji Allah Ya kusa yanke mana haya."
Alhaji Lawan ya saki murmushi ya ce.
"In Shaa Allahu kuwa."
Hajiya Tani tana shirin tashi Alhaji Lawan ya ce, "Ni kuwa ina yaran nan? Tun da na shigo ban ji motsinsu ba."

Hajiya Tani ta É—an gwasale baki ta ce, "Shi dai wancan gantallan ka san ai ba zaman gida yake ba Alhaji. Ita kuma Abida tun da na saka ta wanke-wanke don ba su fita ba, na yi mata faÉ—a take fushi a É—aki." Sai kuma ta sake raunatar da murya cike alamun damuwa ta ce.

"Yanzu Alhaji yaran nan ban isa da su ba kenan? Ko don ba ni ce na haife su ba ne oho?"

Ransa Alhaji ya sake ɓaci, cike da damuwa ya ce.
"Don Allah ki daina faÉ—ar haka Tani, yaran nan tamkar 'ya'yanki suke kuma duk hukuncin da ya dace kina iya zartarwa a kansu."
Tani ta rangwaÉ—a kai gefe ba tare da ta yi magana ba, Alhaji ya sake cewa.
"Kira mini ita, idan ba ta yi aikin gida ba waye zai yi? Yara gabaÉ—aya so suke su sauya halayensu."
Da sauri Tani ta miƙe ta fita, bayan wani lokaci suka dawo tare da Abida. A rakuɓe can gefe ta zauna musamman da ta lura da mummunan kallon da mahaifinta yake jifanta da shi.

"Ba ki da mutumci ko Abida? Ina ganin kin fi É—an'uwanki hankali ashe ya fara zuga ki? Me ya sa ba kya son yin aiki yadda ya kamata?"
Alhaji ya furta yana tsare ta da idanu, muryarta tana rawa ta ce.
"Ka yi haƙuri."
Tana son ta ce masa ba ta da lafiya, tana jin tsoron bayan fitarsa kada Tani ta hukuntata. Don haka ta ja bakinta ta yi shiru, tana nan tsugunne ta ji ya ce.

"Kin ci abinci?"

Da sauri ta kalli Tani, sai kuma ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Eh" Sai ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa.
"Idan aka ƙara kawo mini ƙararki wallahi sai na ɓata miki rai..."
Maganarsa ta maƙale sakamakon sallamar da ya ji ta Fauwaz.

"Fauwaz! Kai Fauwaz zo nan."
Ya furta a ɗan fusace, ɗaga labulen Fauwaz ya yi bakinsa ɗauke da sallama sannan ya zauna. Fuskarsa a haɗae take tamau, don a duniya babu matar da ya tsana sama da Tani. Ko kaɗan jininsu bai haɗu ba, musamman da ya fahimci gashin ƙumar da take yi musu.

"Daga ina kake? Kuma tun yaushe ka fita?"
Alhaji Ya furta yana tsare shi da ido.
"Ban daÉ—e da fita ba Abba..."

"Ƙarya kake Fauwaz! Rabon da na gan ka tun safe, ko ka ɗauka ba na lura da kai." Tani ta furta a ɗan kausashe.
Wani wulaƙantaccan kallo ya wurga mata, ya jima idonsa yana kanta har sai da ta ji ɗar a zuciyarta a kan irin kallon da yake yi mata.
"Fauwaz ka kiyaye ni fa? Kana son ka koyi yawon banza da yara ko? Kai wanne irin yaro ne da kullum sai an kawo mini laifinka?"
Fauwaz da takaici ya cika shi ya ce, "Wai Abba duk abin da aka faɗa maka sai ka dinga hawa kana zama, ka dinga bincike wallahi wani abin ƙarya..."

"Ungo naka, gidanku na ce."
Abba ya yi masa daƙuwa da hannu, Tani tana jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta ce.
"Ka ga irin abin da yaron nan yake yi mini ko Alhaji, yanzu tun yana yi mini a bayan idonka har ta kai yana ƙaryata ni a gabanka."
Alhaji ya sake fusata, rai a ɓace ya ce. "Idan na sake jin makamanciyar maganar nan wallahi sai ranka ya ɓaci Fauwaz, sakarai marara hankali ka ba ta haƙuri."

"Haƙuri?"

Fauwaz ya furta cikin sigar tambaya yana kallon Tani, saboda Fauwaz irin yaran nan ne masu taurin kai. Musamman idan ya kasance a kan gaskiyarsa yake.

"Ko ban isa in saka ka ba ne?"
Abba ya furta murya a sama, Tani ta share guntuwar ƙwallar munafurci da ba ta gama sauka ba ta ce.
"Alhaji yaron da yake ƙaryata ni shi zai ba ni haƙuri? Yanzu da Allah Ya ba ni haihu da ban haifi wanda ya fi shi ba."
Alhaji ya saki ƙwafa sannan ya dubi Fauwaz ya ce, "Idan na sake magana wallahi sai ranka ya ɓaci."

Kamar ba zai motsa bakinsa ba haka Fauwaz ya yi, sai bayan wasu sakanni sannan ya ce.
"Yi haƙuri."
Yadda ya yi maganar da ba su kasa kunne ba babu wanda zai ji, Tani ta haÉ—iyi yawu mai É—aci sannan ta amsa masa.
"Tashi ka ba ni wuri sakarai."
Alhaji ya furta masa, Fauwaz da Abida tare suka tashi suka fita. Suna fitowa Fauwaz ya riƙo hannun Abida ya ce. "Abida na gaji da zaman gidan nan." Muryarta tana rawa ta ce, "Ni ma na gaji yaya, tun da Umma ta mutu muke shan wahala."

ÆŠakinsu suka shiga, sai a lokacin ya ji jikinta da zafi zau. A É—an gigice ya ce, "Ba ki da lafiya ne Abida?" Kai kawai ta gyaÉ—a masa, ya sake ce mata.
"Kin faÉ—a wa Abba?"
Ta girgiza kai ta ce. "Idan na faÉ—a masa Aunty dukana za ta yi, É—azu ma ta dake ni saboda da safe na faÉ—a masa littafin makarantata ya cika."

Fauwaz ya furzar da iska mai zafi cike da takaici ya ce.
"Abida matar nan ba ta sonmu, ba ta son Abba kina ga ta saka shi ya sayar da filinmu."
Muryarsa ta yi rauni, idanunsa suka ciko da ƙwalla musamman da ya tuna fafutukar da mahaifiyarsu ta yi ta sayi filin kafin ta rasu.
Cike da yarinta Abida ta ce, "Allah zai saka mana, ai ita ma idan ta mutu sai mun sa Abba ya sayar da nata."
Ganin yadda jikinta ya ƙara ɗaukar zafi, ya sa Fauwaz jiƙa tsumma yana saka mata a jiki, saboda tun tasowarsa haka ya ga mahaifiyarsu tana yi idan suna zazzaɓi mai zafi.

Alhaji ya jima yana ba wa Tani haƙuri sannan ta sauka, daga haka ya tashi ya fice daga gidan. Tana ganin ya fita ta ciro waya ta latsa wata lamba, ba a jima ta ɗauka tana ƙasa da murya.
"Ina fatan komai ya tafi daidai?"
Daga can ɓangaren aka ba ta amsa da cewar. "Kada wani abu ya ɗaga miki hankali, kuɗi ga su a hannuna tun da ciniki ya riga da ya faɗa. Ragowar maganar idan mun haɗu ma tattauna."
Sallama suka yi, Tani ta saki murmushin farinciki mai cike da tarin manufa sannan ta ce.
"Alhaji Lawan kenan! Idan har ni Tani ina raye, daga yau ka fara irga asara ba riba ba."
Sai ta sake sakin murmushi ta koma tana ƙare wa takardun gidan da ya damƙa mata ajiya kallo mai cike da tarin manufa.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624

[11/05, 16:08] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA UKU
Chapter 4 · 0% Book details