Sashe 17
Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ba kuɗi za ki biya mu ba a zuwanki na farko, za ki kwanta tsirara akwai abin da baƙaƙen Aljanu za su ɗiba a jikinki. Amma kada ki ɗaga hankalinki, babu wanda zai cutar da ke." Ya furta mata yana ɗauko wani ja da baƙin ƙyalle, Zuwaira tana son musa masa tana jin tsoro. Don haka a ɗarare ta tuɓe kayan jikinta, cikin jikinta da ya fara fitowa bokon ya ƙura wa ido. Bayan ta kwanta ya rufa masa ƙyallayen hannunsa, sannan ya rufe idonsa yana kiran aljanu. Sun ɗan jima a haka sannan ya ce ta miƙe ta saka kayanta, daga wannan ranar kuma idan za ta zo kuɗi kawai za ta kawo masa su ma ba masu yawa ba.
Zuciyar Zuwaira cike da farinciki ta nufi gida, sai bayan da ta shiga ɗakinta ta sake ciro ledar magani ta ƙare mata kallo ta tuntsire da dariyar ƙeta. Sai da ta yi mai isarta sannan ta ajiye ta a gefe, ta shiga nazarin yadda za a yi ta kai maganin jikin Rakiya. Tun da na farko ita ba zama inuwa ɗaya suke yi ba, na biyu ba wata doguwar hira suke yi ba. Da ta yi tunanin ko ta takale ta da faɗa don ta shafa mata sai kuma ta tuna da boka ya ce maganin a jikin mutum ɗaya yake aiki. Kenan babu damar ta lakata ta shafa mata a jikinta.
"Ko na bari idan dare ya yi sai na shiga É—akinta na shammace ta?"
Ta tambayi kanta, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta. Tana nan zaune ta ji sallamar Malam Hasan, da yake ita ce da girki sai ba ta fita ba don ta san É—akinta zai shigo.
"Rakiya zo ki gyara wannan."
Malam Hasan ya furta daga waje.
Jin haka ya sa Zuwaira ta ce, "Bantan uba, ni da girkina amma a ba wa wata shegiya gyaran nama."
Da sauri Zuwaira ta tashi, don duk a tsammaninta nama ne Malam Hasan ya kawo, bisa rashin sani ta take ledar maganin ta fasa ta. Maganin ya wanke yatsun ƙafarta, da yake a yunwace ta miƙe da masifa sam ba ta lura ba har ta fita tsakar gida.
Littafin 500 ne ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan lambar 07062062624 idan littafin ya kammala zuwa doc 800 ne.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[19/05, 17:24] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA TARA
Zuwaira tana zuwa ba ta yi wata-wata ba, ta hankaɗa Rakiya da ke duƙe za ta ɗauki ledar da a Malam Hasan ya ajiye mata. Kasancewar Rakiya ba ta san da Zuwaira ba hakan ya sa da ta faɗi ta bugu a hannu sosai, daga ita har Malam Hasan sakin baki suka yi suna bin ta da kallon mamaki. Cike da masifa Zuwaira ta ce.
"Saboda rashin adalci, ranar girkin nawa ka kawo nama za ka ce ta fito ta gyara. Dama ai ka sha cewa ta fi ni iya girki, wato shi ne za a nuna mini rashin adalci. To wallahi uban kuturu ma ya yi kaɗan ballantana na makaho." A wannan karon ma mamakin kalaman Zuwaira ne ya mamaye su, tana sunkuyawa za ta ɗauki leda ta ci karo da waken ƙosa da geron wainar Rakiya. Sororo ta yi jiki a saɓule ta ajiye, tana ɗagowa za ta juya ta tafi da sauri Malam Hasan ya fisgo ta ya ce.
"Wai ke wacce irin jahilar mace ce? Me ya sa ko kaÉ—an ba ki san ciwon kanki ba? Yanzu me kika aikata haka? Ko kin É—auka yadda kike abu da jahilci haka kowa ma yake yi?"
Da farko shiru Zuwaira ta yi duk kunya ta kama ta, amma ganin Malam Hasan ya cigaba da yi mata faÉ—a ya sa ta fara borin kunya wai don kada Rakiya ta raina ta.
"Eh na ji ɗin, duk abin da za ka ce sai dai ka faɗa. Ai da ba a yi mini rashin adalci ba zan magana ba, wa ya sani ma waken ko da kuɗinka ka sayo mata." Zuwaira ta furta tana wurga musu harara, don Malam Hasan ya ƙara tunzura ta sai ya ce.
"To ai daɗin zama ne yake sa wa mace ta ce da miji baba, idan na sayo mata ai matata na ƙara wa jari ba wata ba."
Zuwaira ta sake hassala, suna jin ta fara hargagi Malam Hasan ya miƙa wa Rakiya hannu ta riƙe ya ɗago ta. Don ya sake dagula wa Zuwaira lissafi ya rungume ta yana kaɗe mata ƙasar jikinta haɗe da yi mata sannu. Waken ya ɗauka da kansa ya kai mata har ƙofar ɗaki, sannan ya shimfiɗa tabarma a tsakar gidan ya ɗauko ƙaton kwandon turarensa don Allah Ya saka masa albarka jarinsa ya ninku. Dogon tsaki Zuwaira ta saki ta koma ɗakinta cike da takaici, sai da ta zauna idonta ya sauka a kan ƙafarta da take jin maiƙo. Ƙirjinta ne ya yi mummunan bugawa, har sai da ta dafe shi da hannunta tana jin tamkar zuciyarta za ta finciko ta fito sarari. Laluben ledar maganin ta fara yi ta hango ta a bakin ƙofa ledarsa ta fashe wanda ya tabbatar mata da take shi ta yi da ƙafarta.
"Wayyo Allahna, na shiga ukuna."
Zuwaira ta ƙwalla ihu tana ɗora hannu a ka, saboda zallar tashin hankali. A hargitse Malam Hasan ya shiga ɗakin da gudu, cikin damuwa ya shiga jera mata tambaya.
"Lafiya me ya faru?"
Rasa bakin magana ta yi, don ba ta san me za ta ce masa ba, cikin inda-inda ta ce. "Dama zame wa na yi na faɗi, sai nake jin ƙafata kamar ta gurɗe."
Kallon tsaf ya yi mata, don duk wanda ya ƙare mata kallo zai ga ba ta yi irin zaman da za a ce mutum ya faɗi ba. Guntun tsaki Malam Hasan ya saki ya ce.
"Amma kamar ba musulma ba Zuwaira, ai sunan Allah ya kamata ki kira ba ihu ba."
Ita dai Zuwaira shiru ta yi tana kukan zuci, don hatta jikibta rawa yake saboda tashin hankali.
"Ina ne wurin na yi miki addu'a."
Malam Hasan ya tambaye ta yana zama a gefenta, ƙafar da ta taka maganin bokan ta nuna masa ta ce.
"Duk ƙafar take yi mini ciwo, ka tofe mini ita."
GyaÉ—a kai Malam Hasan ya yi, sannan ya shiga karanta mata addu'o'in yana tofa mata.
"Allah Ya sawaƙe, ki dinga kula."
Ya furta mata cikin tattausan lafazi ganin duk ta yi laushi ta fita hayyacinta, wani tunani Zuwaira ta yi. Har ya je bakin ƙofa ta ce, "Ko na zo na je gidan Malam Bala mai kamu."
Malam Hasan ya juyo ya ce, "Ke da kike fama ina za ki iya fita, ba gara na kira miki shi ba ya zo har gida. Amma ƙafar taki ta yi tsamari haka ne?"
Zuwaira dama ta tambaye shi ne don ta samu ta fita daga gidan, ko ta je gidan bokan da ke can gaba da ƙauyensu ta sanar da shi ɗanyan aikin da ta aikata. Amma jin amsar Malam Hasan ya sa ta ce.
"Ƙyale dai mu gani zuwa gobe, idan ban ji daɗin jikina ba ka kira shi."
Malam Hasan bai kawo komai a ransa ba, ya sake yi mata sannu sannan ya fita. Bayan fitarsa wani sabon kukan ta dasa marar sauti, abin duniya ya haɗe mata don har ji take kamar rayuwarta ta zo ƙarshe.
Tun da ta ga an yi sallar magriba zuciyarta ta cika da tsoro, da yake Malam Hasan bai sake fita ba har sai da ya lura da firgicin da take ciki.
"Zuwaira wai akwai abin da yake damunki ne?"
A firgice ta ɗago ta girgiza masa kai, ana kiran sallar isha'i Malam Hasan ya miƙe zai tafi masallaci da sauri ta riƙo shi ta ce.
"Don Allah ka yi a gida."
Da mamaki ya dube ta ya ce, "Sallar zan yi a gida Zuwaira? Wai ko wani abu ne yake faruwa ban sani ba na ga duk kin firgice."
A wannan karon gyaÉ—a masa kai ta yi ta ce, "Eh wallahi tsoro nake ji, don Allah kada ka fita."
Komawa ya yi ya zauna a gefen gado ya ce, "Ikon Allah, to shi kenan bari na ɗauro alwala sai mu yi jam'in tare." Da wannan maganar Zuwaira ta gamsu, Malam Hasan ya ajiye hularsa a kan gadon ya fita ɗauro alwala. Malam Hasan yana fita kamar wacce aka dasa wa allurar da ke saka bacci, lokaci ɗaya Zuwaira ta ji idanunta suna lumshewa. Duk yadda ta so dakatar da baccin ya gagare ta, nan take ta ɓingire nannuyan bacci ya yi awon gaba da ita. Koda Malam Hasan ya shigo murmushi ya yi ya matsa gabanta, ganin bacci take hankali kwance har da munshari sai ya ƙi tashinta. Ya ce zuwa jimawa kaɗan ya tashe ta, don tun da ta samu ciki idan ta fara bacci da an tashe ta da ciwon kai take tashi. Da yake shi ma ya gaji, kwanciya ya yi da niyyar kishingiɗa sai baccin ya yi awon gaba da shi, ba shi ya farka ba sai da asuba da ya ji motsin Zuwaira ta tashi.