← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 21

Sashe 2

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi sisi ba ni da ita a yanzu Malam Hasan."
Malam Ado ya furta yana zura hannuwa a aljihu yana kaÉ—awa, wani abu ne ya soki zuciyar Malam Hasan. A ransa ya raya wato shi duk wanda ya gan shi ya san neman rancan kuÉ—i ya zo kenan.
"Ka san fa sha'anin damina dama sai godiyar Allah. Komai maleji ake yi da shi, ga kuma hidimar iyali."
Kalaman Malam Ado suka dawo da shi hayyacinsa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"Dama ba rancan kuÉ—i ba ne, kayana ne zan ajiye su idan babu damuwa zuwa nan da gobe ko jibi In Shaa Allah."
Zuro kai Malam Ado ya yi yana bin kayan da kallo, sai ya ce.
"To idan dai ba za su wuce jibin ba ai babu damuwa, ka san ni ma jibin nake son zubin kajin sallah."
Malam Hasan ya saki murmushin yaƙe, don ba shi da mafita da ta wuce hakan ya ce. "In Shaa Allahu zuwa jibin ma zan kwashe su, na gode sosai." Amsa masa ya yi sannan ya wuce ya fara kwaso kayan kaɗan-kaɗan, har ya kwashe su gabaɗaya ya shiga da su wani ƙaramin ɗakin gidan Malam Ado. A gaggauce ya fito bayan ya gama kwashe kayan, ya ƙarasa wurin Rakiya ya ce.
"Mu je."
Murya na rawa ta ce, "Ina za mu je Malam?"
Malam Hasan ya ce, "Gidan abokina Sale."
Rakiya ba ta amsa ba, saboda a duk lokacin da ta buɗe ba ki hawaye ne yake shatata daga idanunta. Da ƙafa suke tafiya kasancewar suna da nisa sosai tsakaninsu da titi, sai da suka yi kusan rabin tafiyar ruwa kamar da baƙin ƙwarya ya tsuge, hakan ya sa Rakiya ta zare ɗankwalin kanta ta sake rufawa a saman hijabinta don Fatihu ya samu sauƙin dukan ruwan.

02/04/2000
Unguwar Na'ibawa, Kano.

Alhaji Lawan mai goro zaune yake a ɗaya daga cikin kujerun da ke zagaye a falon, ƙatuwar television da DVD da ke kange a saman dubaidar ƙarfen ke fitar da amon hoton india mai motso na Mother India. Zaman saman kujerar ne ya gundure shi, don haka ya sauka ƙasa musamman da ya kasance lissafin kuɗi yake yi masu yawan gaske. Wayar gidan ce ta fara ƙara da ke kange a jikin bango, sai da ya ajiye kuɗin hannunsa sannan ya ɗauka.
"Salamu Alaikum, Gambo dillali."
Daga can ɓangaren aka amsa masa, "Wa alaikassalam, Alhaji Lawan na ji ka shiru fa, wai ko ka fasa ne mu sallama wa wani?"
Cikin sauri Alhaji Lawan ya ce, "Haba Alhaji Gambo, ka san ba za a yi haka ba, yanzu haka jimillar kuɗi sun kammala. Irgasu nake yi sai na ƙaraso na kawo maka, amma ina fatan za a ba ni takardu da komai a yau?"
Gambo dillali ya ce, "Takardu tun yaushe suke hannuna Alhaji, yanzu nan da yaushe za mu jira ka? Don mai gidan É—azu ma sai da ya kira ni."

"Nan da awa É—aya In Shaa Allahu."
Alhaji Lawan ya ba shi amsa sannan suka yi sallama, yana ajiye wayar Hajiya Tani ta shiga falon, zama ta yi a gefe ta zuba wa kuÉ—in idanu sai ta ce.
"Alhaji kuɗi sun kammala kenan, ai muna nan da kai watarana sai ka ce na faɗa maka waɗannan da za ka saya sai ya fi wanda ka sayar daraja? Ka ga idan ka samu yadda kake so, har shaguna nan gaba sai ka fitar. Sayen ƙasa ai babu faɗuwa sai riba."
Alhaji Lawan da yake cigaba da irga kuɗin gabansa ya ce, "Tani ta inda kike birge ni wallahi kina da dogon nazari da tunani, duk matar da za ta ba ka shawarar cigabanka ai ita ce matar zama. Wannan gonakin fa sai a yi gida da manyan shaguna biyar a ƙofar gida, kuma unguwar ba ƙaramar daraja gare ta ba. Karkarasa kuwa ai ba za ki haɗa ta da sashenmu ba, kuma duka gonakin duk girman filotai ukun miliyan ɗaya fa, don haka na sayar da gonata na haɗa don na saya watarana sai ki ji wani zancan ake ba wannan ba." Hajiya Tani ta jinjina kai ta ce, "Haka ne kam, Allah Ya sa albarka.
Alhaji Lawan ya amsa da Amin, sannan ya cigaba da irga ragowar kuɗaɗen gabansa. Sai da ya kammala irga kuɗin tas, sannan ya zuba a wata ƙatuwar baƙar jakarsa. Ya dubi Hajiya Tani ya ce, "Ni zan ƙarasa 'yan dillalan, tun ɗazu na yi waya da Alhaji Nasiru shi ne wakilina. Na san ba shi da ɓata lokaci ƙila yana can." Hajiya Tani ta numfasa ta ce, "To shi kenan Alhaji, Allah Ya taimaka. Sai ka dawo." Jakar ya ɗauka ya fita gareji, ya saka a cikin mota. Sannan Fauwaz ɗansa mai shekara goma ya buɗe masa ƙofar ya fita da mota.

Hausawa sabon titin 'yan dillalai da ke titin masallacin Murtala, unguwa ce da ke ɗaya daga cikin fitattun unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kano. 'Yan dillalai, wani keɓantacce wuri ne da ke kan sabon titin. Wanda mafi yawa dillalai ne da ke hada-hada a wurin, wasunsu suna da wata sana'ar bayan ta dillanci. Yayin da wasu kuma suke zaune ba sa cas ko as, sai wannan dillancin kawai suka dogara da shi. Da yawansu ba samari ba ne, masu iyali ne wasu ma dattijai ne waɗanda suka ga jiya da yau a harkar dillanci.
Gambo dillali ɗaya ne daga cikin manyan dillalan da ke rayuwa a wannan wurin, kusan su biyar suka yi haɗakar kama shagon da suke zama. Sai dai mafi yawa sun fi zama a bakin shagon, saboda bishiyoyin darbejiya da ke rufe da wurin don haka ƙofar shagon ta fi cikin shagon sanyi. Harabar 'yan dillalai tana da girma babu laifi, domin a kan gudanar da kasuwamci kala-kala. Akwai masu sayar da abinci, masu fura, kanikawa, shagon teloli, masu gashin balangu, masu gyaran inji da mashina da dai sauransu. Amma rinjayar da dillalai suka yi ya sa ake kiran wurin da 'yan dillalai.
Daga masu zama a kan tabarmin harabar, wasu daga ciki ba su da aiki sai caca da bushe-bushen sigari, yayin da wasu daga ciki ko ƙamshinta ba sa son ji. Iya abin da ya kawo su shi suka saka a gaba, daga cikin dillalan da ke hada-hada akwai na gari masu yi domin Allah. Akwai kuma waɗanda suke cuta, ko su yi kaka-gida a kan fili, gona, kamfani, ko gida idan har ba a ba su abin da suka yanka na la'adarsu ba.

Lokacin da Alhaji Lawan ya ƙarasa 'yan dillalai a can ya tarar da amininsa Alhaji Nasiru, ba su ɗauki lokaci mai tsayi ba suka shiga motar Alhaji Lawan suka ɗunguma zuwa unguwar Karkasara. Kasancewar a lokacin unguwar ba ta cika ba, ya sa take shiru sai ɗaiɗaikun manyan gidajen masu hannu da ƙunbar susa. Wasu katafaren gonaki ne, wanda yake farkon layin. Daga gabansa da bayansa fili ne fetal, an yi masa alama da an riga an saya ba na sayarwa ba ne. Gambo dillali shi ya sake dinga nuna masa gonakin, yana sake kwaɗaita masa darajar unguwar. Har yake fasalta masa zai iya gidan bene sama da ƙasa, mai ɗauke da kusan ɗakuna goma, har a samu babban garejin da zai iya ɗaukar mota biyu, Alhaji Lawan sai murmushi yake yi cike da annushuwa da farincikin a wannan ranar zai mallaki manyan gonaki kamar waɗannan. Suna tsaka da duddubawa, Alhaji Wali shi da wasu mutane biyu suka ƙaraso, sai da suka gaggaisa sannan Gambo dillali ya gabatar da shi.

"Alhaji Lawan wannan shi ne Alhaji Wali, mamallakin waɗannan gonakin, a tare da shi akwai shaidun masu sayarwa." A karo na biyu Alhaji Lawan suka sake gaisawa, sannan ya fito da jakar kuɗi ya miƙa musu. Suka zauna suka fara lissafi tiryan-tiryan har suka kammala kuɗi ya cika cif, miliyan ɗaya. Takardun gonakin aka miƙa wa Alhaji Lawan ya saka hannu, Alhaji Nasiru shi ma ya yi sa hannu a wurin shaidar mai saya. Sai Alhaji Wali ya saka hannu da shaidunsa, suka yi addu'a da fatan alheri sannan Gambo dillali ya kawo gabaɗaya takardun ya miƙa masa suka tafi.
Wayarsa ce ta fara ƙara, yana dubawa ya ga Hajiya Tani ce take kira. Da sallama ya ɗauka, bayan ta amsa masa ta ce.
"Alhaji na ji ku shiru, na ce bari na ji ya ake ciki?"

"AlhamduLillahi Tani, komai ya kammala. Mun gama ciniki har ya damƙa mini takardun ga su, sauran bayanin dai idan na dawo gida ma tattauna."
Alhaji Lawan ya furta cike da farinciki. Amsa masa ta yi, sannan ta katse wayar. Shi da abokinsa Alhaji Nasir ne suka cigaba da duba unguwar suna tattaunawa, don shi ma Alhaji Nasir ya ci alwashin nemo kuÉ—i ya mallaki gona a Karkasaran koda ba ta yi girman da Alhaji Lawan ba. Sun kai kusan minti talatin suna dubawa, sannan suka nufi gida. Alhaji Lawan yana jaddada idan ya samu kuÉ—i zai ba wa leburori su zagaye masa shi.

Su Gambo dillali sai da suka yi nisa da su Alhaji Lawan, sannan Alhaji Wali ya dubi Gambo ya ce.
"Yautai mugun tsuntsu, ma sha miyarka sai ya yi dare. Kar dai ka ce mini hawan ƙawara ka yi wa mutumin nan?"
Gambo dillali ya bushe da dariya, yana sake ƙanƙame jakar kuɗin a kafaɗarsa ya ce.
"Idan fa ana cin baure, ba a tona cikinsa. Kai tun da na gara maka aiki ai kasan tatsuniyar gizo, ba za ta wuce ƙoƙi ba."

"To wallahi dole ka ba ni kaso mai tsoka, don ka san an wuce lokacin aiki banza yanzu."
Alhaji Wali ya furta haka suna bushewa da dariya.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[10/05, 08:08] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA BIYU

RAKIYA
Chapter 2 · 0% Book details