← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 21

Sashe 21

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tsaye take a wani ƙungurmin dajin da babu gida gaba da baya, sai manyan bishiyoyin kuka masu siffar ban tsoro. Lokaci ɗaya hadari ya haɗu, walƙiya ta dinga gilmawa ta ko'ina. Tana nan tsaye cikin firgici da tsoro ta ji bishiyoyin kukar suna takowa gabanta, waɗansu daga cikinsu suna ƙyaƙyata dariya marar daɗi sauraro. Daga saitin tsakiyar ƙafafuwanta ji ta yi ƙasa tana darewa, tana sauke idonta ta ga wani murgujejen maciji ya faso kai ta cikin ƙasa. Duk yadda ta so motsa ƙafarta domin ta gudun don ceton rayuwarta ta ji ta gagara, bakinta take son motsawa amma ko kaɗan ta kasa. Tana ji tana gani macijin ya sulalo kansa ta ƙarƙashinta. A daidai ƙasanta ta ji ya tura kansa, ya fesa mata wani ruwa mai tsananin zafi. Ta saki ƙara cike da azaba, tana kururuwar neman ɗauki. Ya jima a haka sannan ya zaro kansa, sai da ya matsa can gabanta sannan ya miƙe tsaye. Daga cikin macijin ta ga ya rikiɗe zuwa surar mace, ba ta ga fuskarta ba saboda ta ba ta baya kuma tana tafe tana ƙyaƙyata dariya.

Firgigit! Rakiya ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, motsawar da za ta yi ta ji ta sharkaf cikin ruwa. Warin da ya daki hancinta ne ya sa ta yi saurin bankaɗa zanin jikinta, tana cikin wannan yanayin ta ga Malam Hasan ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da kaya yana sharce ruwan kansa wanda hakan ne ya tabbatar mata daga banɗaki yake.

"Rakiya me yake faruwa ne? Ina ta shi na ga gadon ya ɓaci da ruwa, na yi tsammanin ko mafarki kika yi ruwan fitsari ne. Amma kuma sai na ji yana wari yanzu haka wanka na yi zan je masallaci."

Wa Abban Fauwaz ya gani har ya gigice? Me ya aikatawa Tani a shekarun baya? Ya ya rayuwar Fauwaz za ta ƙarke bayan an rufe mahaifinsa a gidan yari? Shin zai dawo? Idan ya dawo wurin wa zai dosa? Kuma wacce irin savuwar rayuwa yake yi a can? Yaya makomar Gambo dillali? Ya ci bulus shi da Tani ko gaskiya za ta yi halinta? Tun a farkon labarin ba a ambaci dangin mahaifiyar su Fauwaz ba, shin tana da dangi ko ba ta da su? Idan tana da su a ina suke rayuwa?

Da alama Zuwaira ta yi galaba a kan Rakiya, shin ya Rakiya za ta kaya ga tsangwamar Inna ga kuma sabuwar lalurar da ta same ta. Shin Rakiya z ata haihu kuwa ko kuwa ƙaddararta ce a haka? Idan aka cigaba da tafiya Inna za ta sauko ta ƙaunaci Rakiya, ko kuwa ƙiyayya ce ta har abada. Ina dangin mahaifi da mahaifiyar Rakiya da ba ta da kowa sai Malam Hasan? Yau idan Malam Hasan ya kwanta dama ina makomar Rakiya?

Gabaɗaya waɗannan amsoshin suna cikin cigaban labarin nan.💃🏻🥳

AlhamduLillah mun kammala free pages É—inmu, ga mai son cigaba zai biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa document 800 ne.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
Chapter 21 · 0% Book details