← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 21

Sashe 10

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu dai ba wannan ba, ga kayan da zan fara saidawa. Ki saka mini albarka da bakinki mai albarka."
Ya furta yana miƙa mata kwandon turaren da glass ɗin yari, fara'arta ce ta faɗaɗa. Cikin jin daɗi ta shiga kwarara masa addu'a, sai da ya gama amsawa sannan ya ce.
"Zuba mini abinci."
Hararar wasa ta yi masa ta ce, "Kai da amarya take jiranka, ko ka manta ne?"
Guntun tsaki ya saki, yana jin wani tsantsanin Zuwaira.

"Ni fa na gaji da kara tun da ba ku san zuru ba, na ga alamar idan na yi shiru sai ta gama da kai tukunna."
Suka ji an furta a tsakiyar kansu, a tare suka waiga suka ga Zuwaira riƙe da labule fuska a murtuke.

"Mene ne haka Zuwaira?"
Malam Hasan ya furta, kamar jira take yi ya dire ta ce. "Kwanana na biyo, tun da na ga ana ƙoƙarin cin amana ta. Don ma dai a banza abin yake wai an tsikari kakkausa, tun da ba iya ƙyanƙyashe ƙwan take ba..."

Tass! Malam Hasan ya ɗauke fuskarta da mari, sannan ya nuna ta da yatsa rai a ɓace ya ce.
"Idan ganganci ya sake biyo dake ta cikin É—akin nan sai na tattaka ki." Da sauri Rakiya ta sha gabansa ta ce.

"Haba Abban Fatihu, me kake yi haka?"

Yana shirin ba ta amsa Zuwaira ta fita da sauri tana sakin kuka tamkar wacca aka ba wa saƙon mutuwa.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Ka ga za ka janyo mini ko? Rakiya ta furta, Malam Hasan ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Kada ki damu don Allah, na sanki sarkin tsoro ce."

"Hasan! Hasan! Za ka fito ne ko kuwa sai an ba ka izinin fitowar?"
Inna ta furta cikin É—aga murya, kusan lokaci É—aya Rakiya da Malam Hasan suka dubi juna. Suna nan zaune suka ji an É—aga labulen É—akinsu.

"To sake shi baƙar munafika, tun da ba kwananki ba ne sai ki ba shi dama ya yi gaba." Inna ta faɗa tana wurga wa Rakiya harara.

"Ga ni zan fito yanzu."

Malam Hasan ya furta, tun bai gama rufe baki ba Inna ta nuna masa hanya ta ce.
"Fita mu je na ce maka, shashasha bawan mace."

Babu yadda ya iya, haka ya bi bayan Inna jiki a saluɓe, don ba ya son ya sake wata maganar ya ja wa Rakiya wani sabon zagin ko baƙar magana.
Tamkar raƙumi da akala haka ya bi bayan Inna har suka fita tsakar gida, ɗakin Rakiya ta nuna masa ta ce, "Maza ka shiga wurin amaryarka, idan ka ga dama kada ka taɓuka abin arziki. Sakarai kullum kana can wurin da babu ƙaruwa ballantana mamora."
Jiki a sanyaye ya nufi ɗakin Rakiya bakinsa ɗauke da sallama ciki-ciki, yana shiga Rakiya ta yi farat ya tare shi cike da kissa da kisisina. Tsaye Malam Hasan ya yi yana kallon ikon Allah, don rashin kunyarta ba ƙaramin mamaki take ba shi ba. Ya san dama ba za a taɓa haɗa kunyar budurwa da ta bazawara ba, amma kuma ko kaɗan bai fuskanci haka daga wurin mahaifiyar Fatihu ba, domin ita ma a bazawara ya aure ta.

"Barka da zuwa angona."

Zuwaira ta furta tana dafa ƙirjinsa, mamaki ne ya sake mamaye shi da ya ga ta ware kamar ba ita ce ta fita tana zabga ihu daga ɗakin Rakiya ba. Bai amsa mata ba, sai gefen gado da ya zauna yana haɗe fuska. Ganinsa hannuwa suna dukan cinya ya sa ta wurga masa tambaya, kwata-kwata ya manta da sayen wani naman kazar amarci. Don wannan auren ya yi ne kawai da zummar ko Rakiya za ta samu salama a wurin Inna. Abincin da Inna ta girka Zuwaira ta miƙa masa, kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya ci loma biyu ya ce ya ƙoshi. Zuwaira da kanta ta dinga jan Malam Hasan cikin kissa da kisisina har mai afkuwa ta afku a tsakaninsu. Don haka koda gari ya waye ko ƙofar ɗaki Zuwaira ƙin fitowa ta yi, wai ba ta jin daɗin jikinta don a dole ta nuna wa Rakiya wani abu ya gifta a tsakaninsu. Da safe koda Malam Hasan ya fito zai shiga ɗakin Rakiya fir Inna ta hana shi, a cewarta ba kwananta ba ne don haka ba ta da haƙƙi a kansa ranar. Yana ji yana gani ya tafi tallan turaren, don kwandon turarensa ma sai Inna ce ta ɗauko masa.

Sannu a hankali zaman Rakiya da Zuwaira ya fara sauya salo duk da dama ba zaman daɗi suke yi ba. Sai Zuwaira ta ɓullo da duk ranar girkin Rakiya tun rana za ta fara kwanciya ta ce ba ta da lafiya, idan yamma ta yi sai ta haye gado ta rufa da bargo. A kan dole idan Malam Hasan ya dawo Inna take tilasta masa kwana a wurin Zuwaira. Saboda wani lokacin cewa take ana tsorata ta, ko ta ce motsi da giftawar mutum take gani. Tun yana ɗaukar abin kamar gaske har ya fara fahimtar makirci ne, damuwarsa ta ninku musamman da yake buƙace da matarsa Rakiya. Don a ƙalla ya kai sati uku ƙwarara bai kwana a ɗakin Rakiya ba, ko da rana bai isa ya shiga ɗakinta ba sai Inna ta fara yi musu masifa. Watarana Inna ta fita unguwa, yana zaune a bakin kasuwa ya ga wucewarta. Farinciki ne ya lulluɓe shi, don haka cikin sauri ya ɗauki kwandon turarensa ya wuce gida. Ya ci sa'a Zuwaira ba ta tsakar gida, don haka ya faɗa ɗakin Rakiya. A kwance ya same ta idanunta suna kan silin, da yake ta yi zurfi a duniyar tunani ko motsinsa ba ta ji ba. Sai da ya kira sunanta sannan ta kalle shi, da sauri ta miƙe tsaye kamar ta ga sabuwar hallita. Malam Hasan ya zuba mata idanu ganin lokaci ɗaya ta zabge duk ta rame, a hankali ya fara takawa wurinta Rakiya ta matsa da sauri ta faɗa jikinsa sai ta ji kuka ya ƙwace mata. Kukan da ta ɗauki kwanaki tana son zubar da hawayensa ba ta samu sukuni ba, tausayinta ya ji har cikin ransa. Ya saka hannu yana bubbuga bayanta, cikin so, ƙauna da tausaya ya ce.

"Ki yi haƙuri farincikina."

Sai da ta share hawayenta ta ce, "Ka fita kada Inna ta dawo."
Bai iya amsa mata ba, sai janyo ta da ya yi ya sake riƙe ta tsam. Tana son ƙwace kanta amma ta kasa, ya sunkuya saitin fuskarta ya furta.
"Na yi kewarki, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi. Ban san ya zan ɓullo wa Inna ba."

"Mu cigaba da haƙuri, watarana sai labari."
Rakiya ta furta a sanyaye, don shi kansa ba ƙaramin tausayinsa take ba. Girgiza mata kai ya yi ya ɗago da fuskarta ya ce.

"Ba zan iya ba Rakiya, saboda ina shiga haƙƙinki. Ya zama dole na nemar mana mafita."Ba ta amsa masa ba, ya cigaba da aika mata kalaman soyayya masu kassara jiki, a hankali yake aika mata da saƙon soyayya mai cike da kewarta. Rakiya mace ce da ta san kanta, don haka ta shiga mayar masa da martani. Kowannensu sai da ya nuna wa ɗan'uwansa ya yi matuƙar kewarsa, don yadda ta ga Malam Hasan ya birkice mata sai ka yi tsammanin babu mace a kusa da shi duk tsawon kwanakin da suka ɗauka.

"Ka tashi ka gyara jikinka ka fita lokaci yana tafiya."
Rakiya ta furta masa, ga mamakinta sai ji ta yi hawaye ya gangaro daga idonsa.
"Me ya faru kuma?"
Ta tambaye shi muryarta tana rawa, don ta fahimci dalilin hawayensa.

"Ina sonki matata, ina ƙaunarki farincikina. Idan na fita yanzu ban san lokacin da zan sake jin ɗuminki ba, a cike nake da kewarki zuciyata ina jin kamar kada na matsa daga kusa da ke."
Yadda yake magana ne ya kashe mata jiki, amma gudun kada a samu matsala ya sa ta shiga tausarsa. Suna nan maƙale da juna suka ji sallamar Inna, tamkar waɗanda suka ga mala'ikan ɗaukan rai haka suka firgice lokaci ɗaya kowannensu gabansa ya shiga faɗuwa.

Tun shigowar Inna gidan ta hango takalmin Malam Hasan a ƙofar ɗakin Rakiya, don haka rai a ɓace ta ƙarasa ɗakin cikin masifa ta bankaɗa labulen ɗakin. Ta windon uwar ɗakin ta hango su da yake a gadon Rakiya a saitin windon yake. A kunyace su Rakiya suka ja zanen gado suka rufe jikinsu. Inna ta ja dogon tsaki cikin masifa ta ce.
."Ke dai wannan an yi jarabaiyar yarinya, yanzu don masifa da rana tsaka ma sai da kika yaudaro mini É—a? Ki bar shi ya tafi nema amma kin kanainaye shi a É—aki, wato kin samu dama na fita ko? To ka tashi ka fito ka je ka yi wanka ka fita nema, shashasha sai kace ba shi da wata matar don jarabar tsiya."
Inna ta yi furucin da ƙarfi, jin Hasan ya amsa ciki-ciki ya sa ta ce.
"Za ka fito ko sai na fito da kai da kaina?"

A kunyace Malam Hasan ya zura wata doguwar rigarsa ya fito, ya nufi banɗaki yana jin ɗacin ɓacin rai a zuciyatsa.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[15/05, 18:55] Ameerah Adam: *GAMMON RAMA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izina ba.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA SHIDA

ABBAN FAUWAZ
Da sauri mutanen da ke ƙofar gidan suka ƙarasa wurinsa suka shiga kiran sunansa, sai dai ganin ba ya numfashi ya sa aka yi gaggawar ɗaukarsa zuwa asibiti. Tun da Tani ta ji abin da ya faru ta saki sabon kuka da kururuwa, da farko abokan Abba cewa suka yi ta bari su je asibiti su ga yadda yanayin jikinsa zai kasance tukunna. Amma ganin yadda Tani ta ɗaga wa mutane hankali ya sa a kan tilas aka bar ta ta tafi asibiti. A lokacin da ta ƙarasa bacci yake yi ana ƙara masa ruwa, tana nan zaune bayan wani lokaci ya buɗe idonsa ya zuba wa fankar da ke wulwulawa ido kamar yana ƙidaya adadin gudun da take yi.

"Sannu Abban Fauwaz!"
Chapter 10 · 0% Book details