← Book details Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 21

Sashe 20

Gammon Rama Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba ya katse shi a fusace sannan ya ɗora da cewa, "Wai me ya sa wasu mazan sun cika kishin masifa ne? Idan na faɗa maka sunan me za ka yi da shi bayan wannan zancan da nake yi maka ya doshi shekara goma sha biyar zuwa sama." Da sauri Abba ya zura takalminsa ya yi wa Baba sallama, don ya lura tun da ya faɗi ƙaryar da Tani ta yi masa ya hassala.

Kai tsaye gidan Alhaji Harisu ya nufa, a lokacin har an fara kiran sallar Magriba. Sai da ya yi sallah sannan ya same shi ya sanar da shi abin da yake tafe da shi, sai dai shi kansa a nan ya tabbatar masa da Tani ba ta gidansa. Kuma ya ɗauki lokaci mai tsayi bai saka ta a idonsa ba. A saluɓe Abba ya baro gidan, ya shiga tunanin inda zai ga Tani saboda akwai muhimmiyar tattaunawar da yake son su yi.
Lokacin da ya ƙarasa gida gani ya yi gidan ya zame masa kamar kango, saboda yadda damuwa ta cunkushe shi ko abincin da ya sayo ya kasa ci. Daga kan gado ya hango wata farar takardar, nan take gabansa ya faɗi. Domin a yanzu farar takarda ta fi komai ɗaga masa hankali, kamar wanda za a kama haka Abba ya miƙa hannu a hankali ya ɗauko takardar. Sai ya ga wani rubutun Tani ta ajiye masa.

_Daga lokacin da ka karanta waccan wasiƙar, na tabbata zuciyarka a ɗokance take da san sanin wurin da nake rayuwa. Sai dai ka sani, za ka yi ta bulayi bara a kufai ne har zuwa lokacin da zan bayyana maka kaina. Kada ka ɗauka wannan takardar a tare da waccan na ajiye maka, a'a, na ajiye maka ita ne ɗazu bayan ka tafi gidan Baba nemana. Na barka lafiya._

Abba ya karanta wasiƙar babu adadi tamkar yana son gano wurin da Tani take a cikin takardar, a nan ya cigaba da zama har bacci ya yi awon gaba da shi.

Daga wannan ranar sai rayuwa ta sake juye masa, al'amuransa suka cigaba da dagulewa. Duk shagunan da yake karɓar bashin kaya sun daina ba shi. Abokan kasuwansa kuwa tuni suka janye jikinsu daga gare shi, idan ya ce su ba shi aron kaya ya kasa ko zai ɗora na shi fir suke hanawa. A haka suka cigaba da zaman shari'a wani lokacin ma sai dai ya tafi kotun a ƙafa, wani zubin kuma ya nemi alfarmar a rage masa hanya a wurin masu ababen hawa.
Sannu a hankali kwanaki suka cigaba da shuɗewa har aka kammala shari'ar su Abba, daga ƙarshe da ba a samu komai daga gare shi ba alƙali ya aika shi zaman gidan yari na shekara takwas babu zaɓin tara. Sakamakon an bi duk wasu ƙa'idojin da suka dace amma bai cika su ba, na farko an ce ya dinga biyan wani kaso lokaci-lokaci ya ce ba shi da hali. Alƙali ya ce ya sayar da wata kadararsa, ko a yi ƙiyasun kuɗinta ya mallaka wa mai fili ita. Amma gabaɗaya Abba ya nuna gazawarsa, Alhaji Dikko da Alhajin da ya sayi fili a wurin Abba suka lamunce da a tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari don ya yi musu zaman kuɗinsu. Don haka aka ingiza ƙeyar Abba da wasu tsirarun matasa, waɗanda su kuma aka same su da laifin fashi da makami.
Babban abin da ya fi tsaye wa a zuciyar Abba shi ne Fauwaz, saboda a cikin kwanakin ya sha yin mafarkinsa cikin mummunan yanayi. Don haka yake ta neman yadda za a yi ya samu kuɗin motar da zai je ya ɗauko shi, sai dai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba har aka kai shi gidan yari. Don haka ya sa a zuciyarsa duk ranar da Goggo ta kawo masa ziyara, zai ba ta adireshin garin da Fauwaz yake da sunan makarantar allon da ya kai shi.

Ranar wata Alhamis ita ce ranar da aka kai Abba gidan yari, a ranar Asabar É—in da ta zo yana zaune jigum cike da damuwa. Domin har da ya kwana biyu a gidan ya gagara sakin jikinsa yadda ya kamata, musamman da yake jin sa a takure da zaman wuri É—aya. Mamaki abin yake ba shi da ya ga wasu sun sake kamar a gidajensu suke, ganin ana ta zuwa ziyarar mutane sai ya ji ina ma zai samu wannan gatan.

'Yanzu a duk duniya wa kake tsammanin zai kawo maka ziyara? Ko don wannan ai ka ga ranar Fauwaz.'
Zuciyar Abba ta raya masa, bai yi tsammani ba ya ji hawaye ya ziraro masa. Sai kuma ya tuna da Goggo, ya san duk duniya Goggo yake da ita shaƙiƙiyar 'yar'uwa, kuma a yadda take ji da shi ya san za ta samu lokaci ta shigo masa.
Yana cikin wannan yanayin wani ma'aikaci ya leƙo ɗakinsu ya ce, "Lawan Shu'aibu 2442."
Da sauri Abba ya É—ago ya ce, "Ga ni."

"Ka zo kana da baƙuwa."
Ganduriban ya furta, wani irin sanyin farinciki ne ya lulluɓe shi. Jikinsa yana rawa ya bi bayansa, suna zuwa Abba ya yi turus sakamakon ganin wacca ya yi tozali da ita. Saboda tsananin mamaki har sai da ya murza idanunsa don ya tabbatar ba mafarki yake yi ba.

GIDAN MALAM HASAN

Suna haɗa ido Zuwaira ta yi tafi cike da izgilanci ta fara waƙoƙin habaici, Rakiya ba ta kula ta ba ta cigaba da tsintar wakenta. Saboda yadda Zuwaira take jin ɗokin ganin abin da zai faru har alla-alla take dare ya yi, ita kuwa Rakiya da ba ta san wainar da ake toyawa ba ta cigaba da sabgoginta zuciyarta fes cikin kwanciyar hankali.

A daren ranar dama Malam Hasan a ɗakinta yake, tun bayan magriba ta yi kwalliyarta cikin riga da zani. Sai da aka yi sallar Isha'i sannan Malam Hasan ya shiga, da yake yawancin sai ya yi sallah yake shiga gida gabaɗaya. Sai da ya fara shiga ɗakin Zuwaira ya duba lafiyarta, da yake haka ƙa'idarsa take. Idan ba ya ɗakin mace to kafin ya shiga ɗakin mai kwana sai ya fara shiga ya duba lafiyarta sun ɗan taɓa hira ko ta minti biyar ce. Haka idan gari ya waye kafin ya fita sai ya leƙa ya ga yadda kika tashi.
Tun da ya shiga ya lura da annurin da ke saman fuskar Zuwaira, har sai da ya gagara haƙuri ya ce.

"Hala akwai wani albishir da kika ƙunshe mini a bakinki?"

Kamar Zuwaira tana jira ta yi zaraf ta ce, "Ni kuwa nake da albishir Yaya."
Murmushi ya saki ya ce, "Ina jin ki."

"A'a gaskiya, sai Allah Ya kaimu zan sanar da kai tun da na tabbata shi ne babban albishir É—in da za ka fara cin karo da shi."
Zuwaira ta furta tana yin far da ido cike da kissa da jin daɗin ganin Malam Hasan ya sake mata yadda take so. Miƙewa ya yi ya ce, "To bari na wuce tun da ba za ki sanar da ni ba."
Wani abu Zuwaira ta tuna ta yi saurin cewa, "Mafarki na yi fa wai na haifi tagwaye duka maza."
Da sauri ta ga ya faÉ—aÉ—a fara'arsa ya ce.
"Allah Ya tabbatar mana da alheri, ko É—aya Ubangiji Ya ba mu masu albarka muna so." Nan take ta haÉ—e fuska ta ce, "Sai ka ce Allah Ya tabbatar mana ai, ko tagwayen ne ba ka so? Ko kuma don ba matar so ce da cikin ba?"

"Zuwaira kina da matsala wallahi! Mene ne laifi a addu'ata? Ko kuwa kawai za mu ce Allah Ya tabbatar ko da ba mai albarka ba ne?"
Shiru ta yi ta zumɓuri baki gaba, sai ta ga ya miƙe zai fita. Tunowa da al'amarin da zai faru da Rakiya ya sa dariya ta suɓuce mata sannan ta ce. "To sai da safe mu kwana lafiya."
Mamaki ne ya kama Malam Hasan, don kusan tun da ya auro Zuwaira zai iya lissafa sau nawa ta yi masa sai da safe cikin tattausan lafazi, idan ba a É—akinta yake da kwana ba. Amsa mata ya yi sannan ya fice ya nufi É—akin Rakiya.

Da sallama ya shiga ɗakinta, ya hango ta zaune a kan tabarma ta sha kwaliyya sai ƙamshi take yi. Hannuwa ya buɗe mata, tana daga zaune ta ɗan tura baki gaba tana ɗauke kanta gefe. Ya lura neman kaɗan take yi 'yan kishin su motsa, don haka ya kama kunnuwansa da hannuwansa ya ce.
"Kaina bisa wuyana."

"Ka koma can na yafe kwanan."
Rakiya ta furta a shagwaɓe, waro ido waje ya yi cike da tsokana ya ce.
"Idan kika sallama ni ina zan saka kaina? Ki yi wa Allah ki taimaki marayan Allah."

Murmushi ta saki cikin zolaya ta ce, "Ai kana sani kake son yi wa marainiyar Allah riƙon sakainar kashi, kai da ga Inna nan a ina za ka kira kanka da maraya."
Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita, ya janyo ta jikinsa ya zuba mata ido cike da so ya ce.
"Wai yaushe kika iya surutu haka?"

Ta saka hannu ta riƙo fuskarsa kusa da tashi, har suna iya jin numfashin juna ta ce.
"Ranar da ka fara iya haÉ—a ido da ni."
Ta ƙarasa furucin tana kashe masa ido ɗaya, kamo ta zai yi ta miƙe da sauri tana dariya. Malam Hasan ya ce, "Yarinyar nan me kike nufi?"
Sai da ta ɗauko tire ɗin abincinsa sannan ta ce, "Ka fi kowa sani ai ƙolona."
Ita da shi gabaÉ—aya suka saka dariya, domin sun tuna lokacin da suka fara soyayya Malam Hasan yana matsayin Almajirin gidansu. Cikin farinciki suka ci abinci suna wasa da dariya, don a daren ranar sun faranta ran juna tamkar wasu sababbin amare.
Chapter 20 · 0% Book details